Ya yi yunkurin rataye kansa don an hana shi shaye-shaye

Wani matashi mai kimanin shekara 25 mai suna Khalid Aliyu da ke kofar Nasarawa a birnin Kano ya yi yunkurin rataye kansa saboda mahaifiyarsa ta hana shi shan miyagun kwayoyi. Matashin wanda ya daura igiya a jikin fankar dakinsa daga bisani mutanen gidansu sun kai masa dauki, bayan da ’yan uwan matashin suka farga da […]

Ya yi yunkurin rataye kansa don an hana shi shaye-shaye
Ya yi yunkurin rataye kansa don an hana shi shaye-shaye

Wani matashi mai kimanin shekara 25 mai suna Khalid Aliyu da ke kofar Nasarawa a birnin Kano ya yi yunkurin rataye kansa saboda mahaifiyarsa ta hana shi shan miyagun kwayoyi. Matashin wanda ya daura igiya a jikin fankar dakinsa daga bisani mutanen gidansu sun kai masa dauki, bayan da ’yan uwan matashin suka farga da halin da yake ciki suka yi saurin sanar da mahaifiyarsu a karshe aka samu kwance igiyar da ya daura a wuyansa don rataye kansa. Mahaifiyarsa Malama Sa’adatu ta shaida wa Aminiya cewa “Allah ne Ya sa kwanansa na gaba, ’yan uwansa suka shiga dakin da yake suka ga halin da yake ciki har ya daura igiya a jikin fanka yana gab da sanya ta a wuyansa. Ganin haka suka yi ihu suka sanar da ni, na nemi taimakon jama’a aka zo aka kama shi.” Malama Sa’adatu ta kara da cewa: “Walalhi lamarin yaron nan ya ishe ni. A kullum sai ya tayar min da hankali sakamakon shaye-shayen miyagun kwayoyi da yake yi. Ina rokon gwamnati don Allah ta taimaka min ta kai shi makarantar horar da matasa ta garin kiru ko Allah Ya sa ya shiryu.” Sharu Atiku Sharifai, Shugaban kungiyar ’Yan sintiri ta Jihar Kano reshen Dala ya bayyana wa Aminiya cewa: “Bayan mun hana shi gudanar da abin da ya yi niyyar aikatawa sai muka dauke shi muka kai shi fadar Sarkin Kano. A nan ne Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi wa matashin nasiha game da lamuran rayuwa tare da bayar da umarnin a kai shi cibiyar gyaran halaye ta jihar.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi