Ya yi yunkurin shiga Saudiyya da kwalaben giya cikin aljihu

Jami’an Hukumar Kwastam ta kasa Saudiyya sun dakile yunkurin wani mutum na shiga kasar da kwalaben giya 12 a wasu aljifan sirri da ya yi a wandonsa. Jaridar Gulf News da ake bugawa a Saudiyya ta ruwaito shugaban Kwastam na hanyar kan iyaka ta Sarki Fahad da ta hade Saudiyya da Baharain Fahad Al Otaibi […]

Ya yi yunkurin shiga Saudiyya da kwalaben giya cikin aljihu
Ya yi yunkurin shiga Saudiyya da kwalaben giya cikin aljihu

Jami’an Hukumar Kwastam ta kasa Saudiyya sun dakile yunkurin wani mutum na shiga kasar da kwalaben giya 12 a wasu aljifan sirri da ya yi a wandonsa.
Jaridar Gulf News da ake bugawa a Saudiyya ta ruwaito shugaban Kwastam na hanyar kan iyaka ta Sarki Fahad da ta hade Saudiyya da Baharain Fahad Al Otaibi yana cewa, wani jami’i ne ya sha jinin jikinsa kan matafiyin inda ya yi masa binciken kwakwaf. Ya ce yana caje shi sai ya iske shi da kwalaben giya 12 a aljifansa da aka kara wa wandonsa, shida ta gaba shida ta baya.
dan fasakwaurin ya sanya doguwar riga a kan wandon don boye kwalaben giyar kamar yadda wata kafar labarai ta Saudiyya mai suna Sabk ta ruwaito.
Motocin da suke fitowa daga Bahrain zuwa Saudiyya suna haduwa da Kwastam ne kawai a bangaren Saudiyya, sai kuma idan motoci za su shiga Bahrain a bincike su a kan iyakar kasar Bahrain.
Hanyar iyaka ta Sarki Fahad mai tsawon kilomita 25 an bude ta ne a Nuwamban 1986, kuma fiye da mutum dubu 30 ne ke amfani da ita a kowace rana don kai da kawo a tsakanin Bahrain da Saudiyya, lamarin da ya mayar da ita mafi hada-hada da jama’a a tsakanin kasashen Larabawa.
Mutane sukan yi yunkurin fasakwaurin bama-bamai da makamai da kwayoyi da dabbobin daji da tsuntsaye da galibi akan boye su a cikin akwatunan katako ta wannan hanya.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50