Ya za a raba Najeriya?

Abu ne mai sauki mutum ya bude baki ya ce a raba Najeriya,to amma a aikata ba karamin aiki ba ne.Kusan abu ne wanda bai yiwuwa a raba bahaguwar kasa kamar Najeriya.Tarihin A Raba,ya samo asali tun lokacin turawan mulkin mallaka,bayan an jefi shugabannin Arewa a Legas, saboda sun ki goyon bayan kudirin da Cif […]

Ya za a raba Najeriya?
Ya za a raba Najeriya?

Abu ne mai sauki mutum ya bude baki ya ce a raba Najeriya,to amma a aikata ba karamin aiki ba ne.Kusan abu ne wanda bai yiwuwa a raba bahaguwar kasa kamar Najeriya.
Tarihin A Raba,ya samo asali tun lokacin turawan mulkin mallaka,bayan an jefi shugabannin Arewa a Legas, saboda sun ki goyon bayan kudirin da Cif Anthony Enahoro na Najeriya ta zama kasa mai ‘yanci a shekarar 1956. An yi wannan a shekarar 1953, abin da ya biyo baya , shi ne, tarzoma a Kano tsakanin ‘yan Arewa da ’yan Kudu.
Daga nan sai Ojuku ya yi yunkurin raba kasar abin da ya haifar da yakin basasa na tsawon shekaru uku, amma dai ba a yi nasarar raba kasar ba,sai ma zubda jinin bayin Allah ciki har da na mata da yara kanana, wadanda yunwa ta kashe.Yunkurin sake Raba kasar ya sake kunno kai lokacin da Manjo Orka ya yi yunkurin yanke wasu jihohin Arewacin Najeriya daga Najeriya, ciki har da Katsina da Kano,shi ma wannan yunkuri bai samu nasara ba.
Dawowarmu mulkin farar hula, an samu kafuwar kungiyoyin tsageru kamar kungiyar Yarabawa ta O.P.C., kungiyar Inyamurai ta MASSOB da kungiyar BAKASSI BOYS, duk wadannan sun yi yunkurin raba kasar nan,  amma har yau hakarsu bat a cimma ruwa ba.
Hujjar da masu da’awar ganin rushewar tarayyar Najeriya kodayaushe suke bayarwa ita ce wai kabilun Najeriya sun yi yawa,wai bambance-bambancen da ke tsakaninmu sun yi yawa saboda haka,ba za mu iya zama a matsayin kasa daya al’umma daya ba.
Kazalika,wasu na da tunanin cewa idan an raba kasar, shi ke nan za mu yi bankwana da matsalar cin hanci da talauci da koma baya.To sai dai fitattun masana Tarihi irin su marigayi Farfesa Kenneth Onwuka Dike sun yi rubuce-rubuce, inda suka kalubalanci irin wannan tunani na ‘yan Nazi.Raba Najeriya bisa kabila abu ne da ke da hadari matuka, saboda auratayya tsakanin kabilun Najeriya da ta auku sakamaon Hijira da kasuwanci da cudanya ta dimbin shekaru wadda ta fara tun kafin zamanin mulkin turawa,yau a Funtuwa akwai Yarabawan da ba su iya Yarbanci ba, kazalika a wasu sassa na Kudu kamar Ikko akwai Hausawan da tuni sun rikide sun koma Yarbawa,wasu tun kakakkaninsu na farko,to idan ka ce za ka raba kasar,su wadannan bayin Allah da suka maida Jos da Legas da Kano a matsayin mahaifarsu,yaya za ka yi da su? Za ka kore su, su koma garuruwansu na da? Yaya za ka shata iyakokokin kasar? Misali tunda bisa kabilanci za a yi rabon, yaya za ka tantance tsakanin Idoma da Tib a Benue,ko Hausa da Bare-bari a wasu Jihohin Arewa maso Gabas,ko rigingimun da ke Faruwa a Kudanci tsakanin Itsekiri da Ijaw da sauransu.
Masu ganin za a yi la’akari da Addini,to yaya za ka dakile batun rikicin Izala da Shi’a? ko ya za ka yi da dimbin musulman da ke Kudu maso Yamma ko Kiristocin Yankin Tsakiya (Middle Belt)? Koko in an raba, za a danne su a hana su sakat?
Za a raba kasar shiyya-shiyya ne koko jiha jiha koko kananan hukumomi? ya za ka dakile  bangaranci,misali Karaduwa da Katsina a Jihar Katsina koIbira da Igala a Kogi da sauransu.
Matsalar Najeriya ba ta Addini ba ce, ko ta kabila illa dai matsala ce wadda wasu azzalumai ke amfani da addini ko kabila suna samun abin duniya. Dubi yadda Malaman addini ke hawan motoci masu tsada,wasu ma har jiragen sama suke saye.Lallai ba za su so a samu fahimtar juna ba,domin da an samu to su .’ kashinsu ya bushel ’yan siyasa masu cin zabe da addini, ana yi musu yakin neman zabe a kaikaice a Masallatu da Jami’u suma nasu ya kare.
Raba Najeriya ba zai warware matsalolin mutane ba, akwai miyagu a kowane yanki na Najeriya, bata lokaci ne kawai,idan za mu fada wa kanmu gaskiya, to mu aikata abubuwan da suka dace,mu daina fakewa da bambance bambancen jinsi ko kabila.
Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina, Sakataren kungiyar Muryar Talakawa 08165270879

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno