Ya zabi taba fiye da matarsa

Alkalin kotun shiyya na garin Ilori, hedkwatar Jihar Kwara, Mista Yusuf Abdulkareem, ya raba auren Uwargida Sherifat Azeez da mijinta Nurudeen saboda yawan zukar taba sigari da mijin yake yi a kowane lokaci, wanda matar ta ce har ya fi kaunar ya yi ma’amala da taba sigari fiye da ita kanta matarsa. A dalilin haka […]

Ya zabi taba fiye da matarsa
Ya zabi taba fiye da matarsa

Alkalin kotun shiyya na garin Ilori, hedkwatar Jihar Kwara, Mista Yusuf Abdulkareem, ya raba auren Uwargida Sherifat Azeez da mijinta Nurudeen saboda yawan zukar taba sigari da mijin yake yi a kowane lokaci, wanda matar ta ce har ya fi kaunar ya yi ma’amala da taba sigari fiye da ita kanta matarsa.
A dalilin haka ne Sherifat, mai shekaru 31 da haihuwa da ke zaune a gidan iyayenta a unguwar Maraba a garin Ilori, ta shigar da kara a wannan kotu tana neman a raba auren nasu, domin a cewarta ba za ta iya ci gaba da zaman aure da Nurudeen wanda ya mayar da cikin dakin kwanciyarsu da falon karbar baki wurin shan taba ba.
 Kafin Alkali Yusuf Abdulkareem, ya yanke hukumci sai da ya saurari bayanan miji da matar, inda matar ta yi bayani kamar haka, “mijina ya mayar da dakin kwanciyarmu da falon baki a matsayin wurin da yake zukar taba sigari da  hayakinta yake turnikewa a kowane lokaci ba tare da tunanin irin illar da yake haifarwa a gare mu ba. Hatta suturunmu ba su tsira daga warin hayakin tabar ba. Kuma haka al’amarin nasa yake idan ya shiga cikin abokansa. Saboda wannan mummunar dabi’a da yake aikatawa na tsawon shekaru uku da muke zaune tare kuma ya ki jin shawarar da nake ba shi, shi ne dalilin da nake rokon kotu ta yi wa Allah da Annabi ta raba wannan aure domin ni ba zan iya ci gaba da zama da wannan mutumi da ya fi sha’awar shan taba sigari fiye da ni kaina matarsa ba.” Inji Sherifat, wacce ta riga ta kaurace daga gidan mijin nata tun kafin a yanke wannan hukumci.
 Da yake kare kansa, Nurudeen, wanda bai musanta zargin da matarsa ta yi masa ba, sai dai ya shaida wa kotun cewa, akwai alamar wani abu da ta boye a cikinta amma ba maganar taba sigari ce dalilin rabuwar da take so ba, “domin tun kafin a daura mana aure a shekarar 2011, tana sane da irin zukar taba sigari da nake yi, wacce na saba da yin hakan kuma tana da wuyar bari. Na yi mamaki kwarai da ta kasa nuna korafinta na tsawon lokacin da muke zaune tare sai a yanzu. Saboda haka na amince da raba wannan aure da ta nemi a yi bayan ta butulce mini.”
 Bayan sauraron bayanan miji da matar ne Alkali Yusuf Abdulkareem, ya yanke hukumcin raba wannan  aure wanda ba a taba samun haihuwa a tsakani ba. Alkalin ya mika wa kowannensu takardar satifiket na shaidar raba auren.