Ya zama kurman karya don kin sauraran matarsa na shekara 62

Wani magidanci mai suna Barry Dawson mai shekara 84 da ke zaune a birnin Waterbury a jihar Connecticut kasar Amurka, na fuskantar barazanar tilasta masa sakin matarsa, bayan da matar ta kai kararsa akan cewa, yana yi mata karyar cewa shi kurma ne har na tsawon shekaru 62 suna zaman aure a matsayin kurman karya, […]

Ya zama kurman karya don kin sauraran matarsa na shekara 62

Wani magidanci mai suna Barry Dawson mai shekara 84 da ke zaune a birnin Waterbury a jihar Connecticut kasar Amurka, na fuskantar barazanar tilasta masa sakin matarsa, bayan da matar ta kai kararsa akan cewa, yana yi mata karyar cewa shi kurma ne har na tsawon shekaru 62 suna zaman aure a matsayin kurman karya, a cewar Barry ya yi hakan ne don kaucewa sauraran kalaman matsar shi.

A rahoton da aka gabatar a takardar da take dauke da tilastawa Barry sakin matarsa, kasancewar bai taba furtawa matarsa kalma daya ba tun aurensu, matar shi mai suna Dorothy da ke da shekara 80.

Misis Dorothy, ta koyi alamomin kalmomi da zata iya magana da mijinta, kasancewar iya saninta mijin nata kurma ne bai iya magana da ita.

A cewar Misis Dorothy, “Na dauki shekara biyu ina koyon yadda zan yi magana da hannuwa, har na kai matsayin kwarewa da magana da hannu, daga baya yazo ya samu matsalar idanu wanda a yanzu na tabbatar matsalar idanun itama karya ce”.

Ma`auratan sun samu `ya`ya shida tare da jikoki 30, yayin da duk iyalan sun tabbatar da Mista Barry kurma ne.

A cewar Misis Dorothy, idan mijinta yana gida sai ya kasance kamar kurma. Amma wata rana ina kallon bidiyon Youtube sai  ga shi yana waka  da daddare a wata mashaya, a maimakon ya kasance wajen bada tallafi, yanzu na fahimci kome game da mijina.

Lauyan Mista Barry, Robert Sanchez ya kare wanda yake wakilta akan cewa, akwai yiwuwar mijin yana yi wa matarsa kamannin kurma ne don kaucewa wasu kalaman da zasu bashi kunya.

Lauya Robert Sanchez, ya bayyana cewa mutumin da ake kwatantawa matarsa shi kurma ne, ba yana nufin yi hakan bane don cutar da iyalin shi, da ace yana cutar da ita ne ta ya ya aurensu zai kai tsawon shekara 62 suna tare.

Lauya Robert, ya ce “Mista Barry ya kasance ba mai yawan magana ba ne, idan har da ace shi kurman gaske ne da yanzu sun rabu da matarsa shekaru 60 da suka wuce, kuma yana yi wa iyalansa ne kawai ba wani ba”.

Duk da haka dai Misis Dorothy ta ce zasu hadu da Lauyan da ke kare mijinta a kotu kuma tana bukatar a biya ta kudi don sakamata da irin wahalar zaman auren da ta yi da mijinta.

 

 

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana

An rantsar da Shugaban Mozambique Daniel Chapo

China za ta sayar wa Elon Musk TikTok saboda rashin tabbas