Ya zargi ma’aikaciyar banki da laifin handame masa kudi
Wani dan kasuwa da ke sana’a a kasuwar tumatur da ke Deide Abuja, mai suna Lawal Abubakar, ya zargi wata ma’aikaciyar banki da ke amsar kudi a bankin Diamond na kasuwar sayar da kayan gini na Abuja da ke Deidei, mai suna Maria Baiyar, da yunkurin cinye kudi Naira dubu dari biyu da uku da […]
Wani dan kasuwa da ke sana’a a kasuwar tumatur da ke Deide Abuja, mai suna Lawal Abubakar, ya zargi wata ma’aikaciyar banki da ke amsar kudi a bankin Diamond na kasuwar sayar da kayan gini na Abuja da ke Deidei, mai suna Maria Baiyar, da yunkurin cinye kudi Naira dubu dari biyu da uku da ya kai bankin, inda ya danka mata ta hanun wani da ya jagorance shi zuwa wajenta, sannan ya ba ta takardar bayanin cika kudin (teller) da hannunsa.
A lokacin da ya ke bayani a Kotun majistiri ta Abuja da ke garin Jiwa a ranar Talatar da ta gabata, Lawal Abubakar ya bayyana wa kotun cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a 17 ga watan Janairu ta wannan shekarar, bayan mai gidansa wani mai suna Abubakar Usman ya aike shi da kudin don sawa a wani asusun ajiya da ya cika bayan ya shiga bankin, sai dai ya ce a daidai lokacin da layi ya zo kansa, sai wani jami’in banki ya umarce shi da ya hau kan bene hawa na farko, kasancewar ba a amsar kudi da ya dara naira dubu 100 a kasa.
“bayan na hau hawa na farko na bi wani layi a wajen, sai dai ana cikin haka ne kuma sai wani da ke zaune a kan kujera ya tunkaro ni ya ce yana gabana a layin. Bayan mun fara jayayya ne wani mutum da na tsammanin ma’aikaci ne a wajen ya sa baki, sannan ya bukace ni da na je bangaren kasa, na shaida masa cewa daga wajen nake amma aka umarce ni da na zo hawa na farko. a nan ne ya jagorance ni zuwa wajen wannar jami’ar banki, inda ya mika mata kudin da na kawo bayan ya karba daga wajena, sannan ni da kaina na mika mata takardar da na cike na bayanin kudin (teller,) sannan na gaya mata cewa zan wuce sallar juma’a, kasancewar na makara, amma zan dawo na karbi takardar bayan takammala shigar da kudin.’’
Ya ciga da cewa, “sai dai bayan na dawo daga sallar, da na tambaye ta takardar, sai ta ce da ni ai wanda ya jagorance ni zuwa wajenta ya dawo ya karbi kudin bayan ya sanar da ita cewa ya sauya ra’ayi a game da shigar da kudin, inda kuma ta ba shi.’’
Maria Baiyar wanda tun farko mai Shari’a Josephine Obano ta bada belinta a yayin zama na farko da ya gabaci na ranar Talatar, ranar da dan sanda mai shigar da kara Noah Moses na ofishin ’yansanda na garin Gwagwa ya gurfanar da ita kotun bayan shigar da karar ta ofishinsu, ba ta ce komai ba a yayin zaman in banda shiga cikin sundukin kara bayan an kira karar.
Da Kotu ta nemi jin ta bakin lauyanta mai suna Anietie Udoh, ko yana da tambaya ga mai kara? lauyan ya roki kotun da ta ba shi lokaci don shirya tambayoyinsa. Daga nan ne kuma kotun ta dage shari’ar har zuwa ranar 12 ga watan Maris don cigaba da sauraron karar.