Yachilla Baba Jidda: Aure ya koya mini hakuri da juriya

Tarihin rayuwata Sunana Yachilla Baba Jidda, an haife a Jihar Barno ,kuma ni ‘yar kabilar Kanuri ce daga dangin marigayi Kaftin Babakura Kakaru.Na fara karatu a makarantar firamare mai suna Yarwa da ke Maiduguri,amma na gama a makarantar Yarwa babba.Na tafi makarantar sakandare ta ‘yan mata a Potiskum da ke Jihar Yobe a shekarar1967.Daga nan […]

Yachilla Baba Jidda: Aure ya koya mini hakuri da juriya
Yachilla Baba Jidda: Aure ya koya mini hakuri da juriya

Tarihin rayuwata

Sunana Yachilla Baba Jidda, an haife a Jihar Barno ,kuma ni ‘yar kabilar Kanuri ce daga dangin marigayi Kaftin Babakura Kakaru.
Na fara karatu a makarantar firamare mai suna Yarwa da ke Maiduguri,amma na gama a makarantar Yarwa babba.Na tafi makarantar sakandare ta ‘yan mata a Potiskum da ke Jihar Yobe a shekarar1967.Daga nan kuma sai na koma Maiduguri domin ci gaba da karatun gaba da sakandare ,daga nan kuma sai na tafi jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.Na karanci fanninTattalin arziki,kuma na yi bautar kasa a Jihar Legas.Na fara koyon aiki daga kasuwanci da muke yi na gida inda muke fita da shigo da ababen hawa daga baya kuma muka bude bangaren gyara mai suna” Cactus Nigeria Limited”.Sai a shekarar 1984 na dawo Maiduguri,na bude nawa harkokin kasuwanci na dinkin kayan kawata gida.Lokacin da aka yi wa maigidana canjin gurin aiki daga gwamnatin Jiha zuwa gwamnatin Tarayya sai na bude makarantar koyon dinki a Abuja kuma ana yin aiki mai kyau kasancewar ni ba bakuwa ba ce a sana’ar.
Na kasance mai gwagwarmaya a siyasa saboda ina so in taimaka a harkar gudanar da gwamnati a wannan kasa wata rana.Na fara a matsayin kansila a birnin Maiduguri,kuma na tsaya takarar zama memba ta gyaran tsarin mulki amma ban ci ba.Duk da haka ban daina siyasa ba,kasancewar mijina Jakada Baba Ahmed Jidda wanda shi ne Sakataren gwamnati a Jihar Barno,ya tsaya takarar gwamna a wannan Jiha.Haka nan lokacin da mijina yake Jakada a Burkina Faso,na sami kusanci da Buhari kasancewar yana halarta taron kasa da ake yi kuma mun kasance mu ne masu ba shi masauki,daga nan sai muka tsinci kanmu muna tattaunawa game da kasarmu, sai tsarinsa game da Najeriya a matsayinsa na Shugaban kasa ,ya burge ni.Kuma ya yi aikin Soja da marigayi Babana ba tare da ya sani ba ,kuma ya kasance shi ne Gwamnanmu a tsohuwar Jihar Borno.Saboda haka na zabi aiki da Buhari duk da cewa mijina dan PDP ne.A shekarar 2011,lokacin da aka sami jam’iyyar CPC sai na bai wa mijina hakuri na zama cikakkiyar ’yar jam’iyyar.Sai aka nada ni shugabar mata ta shiyyar Arewa maso Gabas.A yanzu ni ce jagorar yakin neman zaben dan takarar Shugabancin kasa a jam’iyyar APC Buhari.
Abubuwan da ba zan manta da su ba
Na yaba da hanyar da mahaifiyata ta taso da mu.Ta kasance mai zafi gurin tarbiyya kuma duk lokacin da muka dawo daga makaranta ba wanda zai tsaya yana shirme,za mu cire kayanmu ne kawai mu shiga aikace-aikacen gida kafin mu wanke kayan makantarmu mu yi shirin gobe.
Abin da na koya a gurin mahaifana
Ta koya min yadda zan zama matar gida ta gari da kuma yadda zan gudanar da rayuwar aure .Shi kuwa Babana ya kasance mai shiru-shiru ne kuma mai kulawa ne,amma ba ya son wargi.Ya yi matukar kokari wajen tabbatar da cewa ’ya’yansa sun sami ilimi.
Burina ina karama
A matsayina na yarinya,na so in zama malamar makaranta,saboda malaman ajinmu suna ba ni sha’awa a lokacin,kuma su kadai ne ma’aikatan da muke haduwa da su.Kuma lallai akwai uku daga cikinsu da nake so,kuma har yanzu nakan tuntubi daya daga cikinsu.Nakan yi tunanin kaina a matsayin daya daga cikin wadanan malamai, na yi gyaran gashi irin na Kanuri na tsaya a gaban aji ina koyarwa,amma wanan mafarkin ya wuce.
Yadda na hadu da mijina
Na hadu da shi ta hanyar abokansa lokacin ina makarantar gaba da sakandare,shi ya riga ya gama babbar makarantarsa yana jiran shiga Jami’a.A lokacin yana koyarwa na wucin gadi,mukan hadu yawanci a hanyata ta zuwa makaranta,daga nan muka fara.
jikokina,shi ya sa nake fatan Allah Ya kara min baiwa.

Abin da na koya a rayuwar aure
Aure ya koya mini hakuri,a rayuwar aure dole ka ga abu amma ka yi kamar ba ka gani ba,ka sa auduga ka toshe kunnuwanka daga zantukan mutane.kuma na lura idan kika sadaukar da kanki ga miji kuma kuka fahimci juna,aurenku zai dade.Kuma sai kin sadaukar da mafi yawan lokacinki da karfinki da abin da kike so domin a sami zaman lafiya.
Kasancewata Uwa
Zan ce abin sha’awa ne,lokacin da na sami dana na fari, na kusa gama Jami’a.Ko da yake haihuwar ta zo min ba zato,kawai na je awo sai likita ya ce ai haihuwa ta zo,daga ni sai mijina.Bayan na haihu na koma gida,sai na rikice saboda ban san yadda zan fara rainon ba.Amma bayan’yan’uwana sun zo daga Maiduguri sai na ji dadi.
Mutanen da suka fi burgeni
Akwai su da yawa,misali surukata wadda ta rasu kowa yana kiranta Mama amma sunanta Fatima.Ta kasance mai addini sosai da kulawa kuma malama ce.Na koyi abubuwa da dama daga gare ta,kuma al’umma sun yi rashinta matuka.Da a ce ta fito daga wuraren da mata suke zuwa makaranta da ta zama Farfesa.Haka nan mahaifiyata ma na koyi tarbiyya da aikin gida a wajenta,kasancewar kowa ya santa da iya girki a unguwarsu.Kuma na koyi hikimomi da dama daga wajenta.Akwai ’yar’uwata da ta mutu ita ma ina sonta,tana son tsafta kuma ta kasance mai kirki,sai dai na rasa su daya bayan daya.
Winnie Mandela tana daya daga matan da nake sha’awa kuma nake so,ita ce matar da nake so na yi koyi da ita yadda ta zauna da mijnta,ta sha wuya amma ba ta karaya ba. Tana tare da mijinta sama da shekara 30,kuma har yanzu ina sha’awarta.Ta bangaren maza kuwa akwai Babana da mijina da Janar Buhari,wani lokaci idan na duba yadda mijina yake da hakuri da juriya da yafiya, nakan roki Allah ya ba ni wannan baiwar.
Yadda nake kwalliya
Mutane sukan ce ina kwalliya,amma nasan ina so in yi shiga mai kyau matsakaiciya.Ina son yadi da kuma hada kaloli wajen kwalliya.
Yadda nake hutawa da iyalina
Mijina ya kasance mai aiki sosai amma idan ya dawo gida da yamma, mukan shakata da karanta jarida ko kallon talabijin tare.Mukan tattaka domin motsa jiki kuma nakan bi shi wajen wasan gof(golf).
Inda nafi so in je hutu
Wani guri ne a kasar Turkiyya,amma na gano wani guri a Masar kwanan nan inda nake so na rika zuwa.
Abubuwan da nake so a tuna ni da su
Idan zan sami dama in taimaka wajen ci gaban al’ummata ,ina so ya zama
daga abin da za a tunani da shi. Kuma ina fatan Allah Ya ba ni ikon riko da addini yadda zan rike mijina da ‘ya’yana da