Yadda ƙananan yara ke zaman kurkuku ba tare an da kai su kotu ba
Ayyuka sun yi wa kotunan yawa, don haka dole a riƙa samun irin wannan.

Rayuwar Nura Muhammad dan shekara 13 a duniya ta gamu da cikas bayan da ya tsere tsallake rijiya da baya a lokacin da gungun wasu ’yan ta’adda suka kai hari a kauyensu da ke Karamar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato, inda suka raba shi da iyaye kuma babu matsuguni.
Don haka ba shi da wani zabi, dole ya koma garin Sakkwato, domin fara sabuwar rayuwa.
Ko da aka tambaye shi inda iyayen nasa suka, sai ya kada baki ya ce, “Ban san inda iyayena suke ba,” ko sun rayu a lokacin da aka kai wa kauyen hari a farkon shekara ta 2023.
Kasancewar a baya Nura ya yi karatun Al-Kur’ani, sai ya sami saukin karbarsa a matsayin sabon dalibi a wata makarantar allo a garin Sakkwato.
Kafin ya tsere daga kauyen nasu ya yi karatun Al-kura’ani har zuwa Izu 6.
Yadda aka kama shi
Nura ya rasa ’yancinsa ne a watan Yulin shekara ta 2024 lokacin da aka kama shi tare da wasu abokansa su uku — Ahmad Abubakar da Ibrahim Shuaibu da Ibrahim Umar.
A cewar Nura, suna tsaka da barci ’yan sandan suka kai samame gidansu ne, suka kai su ofishin ’yan sanda na Kwani a Jihar Sakkwato.
Ya ce, “Da Keke NAPEN ’yan sandan suka zo, ba su fada mana komai ba kan dalilin kama mu, ko wanda ya kai musu rahoto, hasali ma tufafinmu da takalmanmu ma ba su bari mun sanya ba.”
Nura ya ce, daga baya ’yan sandan suka zargi Ahmad, daya daga cikin abokan nasa da satar gwangwanayen madara a wani shago a Tsohuwar Kasuwar Sakkwato, amma ba su bayyana wanda ya kai musu kara ba, kuma ba su bar yaran su yi bayanin bangarensu ba.
“Kai-tsaye suka kai mu kotu ba tare da tuntubar iyayenmu ko masu kula da mu ba. Daga nan aka tura mu gidan yarin Sakkwato a watan Yuli ba tare da an gurfanar da mu a gaban kotu ba,” in ji shi.
Ya ce kotun ta ce su dawo nan da makonni biyu, amma tuni suka shafe sama da wata guda ba tare da sanin yaushe nan gaba za a saurari shari’ar tasu ba ba. Gidan yarin yana karkashin kulawar Ma’aikatar Kula da Jin Dadin Jama’a da Jinkai ta Jihar Sakkwato.
Ziyarar da aka kai kurkukun a watan Satumbar 2024 ta nuna cewa Nura na daga cikin kananan yara 48 da ke tsare a wajen, kuma fiye da kashi 85 cikin 100 na yaran ba a gurfanar da su a kotu ba, ko kuma ba a same su da laifin da ake tuhumar su da aikatawa ba, amma aka kai su gidan gyaran halin.
“Yawancinsu suna jiran a gurfanar da su ne a gaban kotu. Wasunsu na bukatar su bayyana a kotu ne kawai don samun beli.
“Wasu kuma an riga an yanke musu hukuncin ko dai zaman gidan yari ko kuma biyan tara,” in ji Abubakar Ahmed, Jami’in Kula da Gidan Yarin.
Abubakar Ahmed ya dora laifin kan sakacin masu gabatar da kara da jami’an tsaro da ke kula da shari’ar kananan yaran.
“Abin damuwa ne sosai, domin ya kai ga sai mun kira masu alhakin kai su kotu. A wasu lokuta, ni ke kira in tunatar da masu gabatar da karar, su kai su kotu a kan lokacin da ya kamata.
“Wannan na daga cikin dalilan da suka sa har yanzu ba a gurfanar da wasu yaran nan ba,” in ji shi.
Aminiya ta lura cewa, ci gaba da tsare yaran ba tare da gurfanar da su a gaban kotu ba, ya saba Sashe na 166 na Dokar Kare Hakkin Yara ta Jihar Sakkwato ta Shekarar 2021, wadda ta takaita tsare yara gabanin shari’a, ga manyan laifuffuka da suka hada da tashin hankali ko yawan maimaita laifi, da sharadin idan yin hakan ne kadai zabin da ake da shi.
Tauye haƙƙin yara
Masana shari’a da masu fafutukar kare hakkin bil Adama sun yi tir da ci gaba da tsare yaran a gidan yarin Sakkwato.
Wani lauya mazaunin Sakkwato, Muhammad Isma’il ya bayyana hakan a matsayin abin saba wa Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya.
“Sashe na 35 na KundinTsarin Mulkin Nijeriya ya bai wa kowane dan Nijeriya ’yancin walwala.
“Ba za a tsare mutum sama da sa’o’i 24 ba, ba tare da an kai shi kotu an yi shari’a ba, sai dai idan babu kotu a tsakanin kilomita 40, idan aka kwatanta da sa’o’i 48,” in ji Lauya Muhammad Isma’il.
Ya ce a dokar Nijeriya tsarewar da ake yi a mutane kafin a yi shari’a ba ta da yawa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
“Sashin ya bai wa kowane dan Nijeriya ’yancin walwala, kuma babu wani mutum da za a hana shi irin wannan ’yancin.
“Wannan shi ne tanadi na farko da Gidan Yari na Sakkwato ke karyawa, na tsare yaran na tsawon watanni ba tare da samun wani hukunci ba, ba kuma tare da gurfanar da su gaban kotun da ta dace ba,”
Kamen masu zanga-zangar yunwa
Safiyanu Sani mai shekaru 14 yana daga cikin yaran da aka kama a lokacin zanga-zangar da aka gudanar a kwanaki 10 na farkon watan Agustan 2024, mai taken #EndBadGovernance, wadda aka yi a fadin Nijeriya domin nuna bacin rai bisa yadda kasar ke kara fadawa cikin matsanancin rayuwa.
Duk da cewa Safiyanu bai shiga zanga-zangar ba, amma ’yan sanda suka kama shi a yayin da yake kokarin neman man da zai yi amfani da shi a injin nikansa.
Saurayin ya ce, “Iyayena ba su san cewa a halin yanzu ina tsare a kurkuku ba, saboda ba a kai ni kotu ba. ’Yan sanda sun kawo mu nan kai-tsaye bayan kama mu. Sauran kuma manya ne kuma an kai mu gidan yari.”
A lokacin da tawagar ta ziyarci gidan yarin a watan Satumban 2024, Safiyanu ya ce daga cikin su yara hudu da akakama a lokacin zanga-zangar, an saki mutum daya.
Kamar yadda lamarin Safiyanu ta kasance, haka aka tsare wasu yara 28 a Babban Birnin Tarayya Abuja, saboda shiga zanga-zangar.
Sai dai ba kamar Safiyannu ba, an tuhume su ne da laifukan da suka shafi ta’addanci, inda Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare su.
Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Amnesty International ta bayyana cewa an kama wasu yara 12 tare da tsare su ba bisa ka’ida ba a Jihar Katsina yayin zanga-zangar.
Amnesty ta yi zargin cewa akwai yiwuwar jami’an tsaro sun kama wasu daga cikin yaran ne a kan tituna a lokacin zangazangar saboda abin da ta kira, “rashin adalci”.
“Yaran a yanzu suna cikin hadarin fuskantar barazanar tuhume-tuhumen karya,” in ji kungiyar.
Jinkirin yanke hukunci
Jamila, mai shekaru 16, ta shafe fiye da shekaru uku a tsare a gidan yari ba tare da an same ta da wani laifi ba.
Tun shekara ta 2021 aka kai ta gidan yarin matasa ne bisa zargin ta da kashe dan dan uwan tsohon mijinta.
Amma ta tabbatar da cewa, ba ta aikata laifin da ake zata ba. “Yaron ya mutu ne a dakina, amma ban san abin da ya faru ba, aka zarge ni da kashe shi, amma ba ni da laifi, wallahi, na rantse da Allah,” in ji Jamila, wadda ta bayyana cewa lamarin ne ya sa ta rabu da mijinta.
Ta bayyana takaici cewa gaskiyar abin da ya faru ba a bayyana yake ba, a yayin da kotu ke ci gaba da jinkirta shari’ar da take bata rayuwarta a gidan yarin.
Ta ci gaba da cewa, “kotu ta saurari karar, yanzu hukunci nake jira. Zuwanmu kotu na karshe shi ne a watan Afrilun shekara ta 2024, amma har ya zuwa watan Satumba na shekara ta 2024, ba mu ji komai ba. Ban san lokacin da zan bayyana a kotu ba nan gaba.”
Koma bayan ilimin yara
Ana kyautata zaton tsare yara a gidan yarin Sakkwato yana taimakawa sosai wajen matsalar rashin zuwa makarantarsu a jihar.
Rahoton Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), ya nuna wannan yana daga cikin dalilan da kusan kashi 53 cikin 100 na yaran jihar ba sa zuwa makaranta.
Rahoton ya ce, a shekarar 2023 sama da kashi 50 na yara da ba su wuce shekarun makarantar firamare ba, ba sa zuwa makaranta a wasu ihohi bakwai ciki har da Sakkwato.
Wato a cikin duk kananan yara biyu da suka isa shiga makarantar firamare a wadannan jihohi, daya ba ya zuwa makaranta kwata-kwata.
A ziyarar da aka kai gidan yarin a watan Satumban 2024, an gano cewa kashi 90 na tsararru 48 da ke gidan, ba su taba shiga aji ba.
Ragowar kuma sun bi sahun dubban yara marasa zuma makaratun boko a yankin Arewa maso Yamma.
Daya daga cikinsu, Aminu Hassan dan shekara 12, wanda aka kama jim kadan da kammala makarantar firamare, ya ce ana tuhumar sa ne da laifin taimaka wa barayi.
“Babur din makwabtanmu aka sace kuma aka zarge ni da taimaka msu. Zan so in bar nan, amma babu wanda zai zo ya karbi belina. Burina shi ne in fara sakandare tare da sauran sa’o’ina,” in ji shi.
Babu tanadin ba su ilimin boko — Gwamnatin Sakkwato
Da take mayar da martani, Gwamnatin Jihar Sakkwato ta amince da wannan matsala, inda ta bayyana rashin isassun kayan aiki a matsayin babban kalubale.
“Babu wani tanadi na ilimin yaran a gidan yari. Abin da ma’aikatar take yi kawai shi ne ta dauki wamo malamin Islamiyya da ke zuwa ya koyar da su ilimin addinin Islama,” in ji Daraktan Jin dadin Jama’a na Ma’aikatar Jin dadin Jama’a da Jin kai ta Jihar Sakkwato, Yusuf Sani.
Ya ce amma hakkin gwamnati ne ta tabbatar cewa kowane yaro a jihar ya sami damar samun ilimi a matakin farko.
Matsalar kasa
Tsare yaran ba bisa ka’ida ba a kurkuku da sauran cibiyoyin gyaran hali a Nijeriya ke yi bai tsaya a Jihar Sakkwato kadai ba.
Alkaluman da Hukumar Gyaran hali ta Nijeriya sun nuna a watan Oktoban 2024 mutum 84,337 ne ake tsare da su a gidajen yari a fadin Nijeriya, kuma mutum 56,973 daga cikinsu, har da kananan yara, suna zaman jiran shari’a ne.
Hakan na nufin a cikin kowadanne tsararru 10, mutum bakwai ba a gurfanar da su a gaban kotu ba. Mista Marbelous Monday, lauya ne mai aiki da Gidauniyar Citizens Gabel Foundation for Social Justice, ya bayyana tsare kananan yara a kasar nan a matsayin rashin mutunta tsarin mulki.
“Dalilan wadannan abubuwa su ne amfani da matsayi da yadda bai dace ba da saba wa doka da oda, da kuma karancin ayyukan sa ido,” in ji shi.
Ya ce ya kamata bangaren zartarwa su nisanci yin amfanida mulki, su mutunta doka, su kuma ba da damar shin shari’ar adalci kafin a daure yara.
A cewarsa, sau da yawa kotuna suna yin watsi da dokar shari’ar kananan yara. Dokar Kare Hakkin Yara ta Jihar Sakkwato ta 2021 da Dokar Kare Hakkin Yara ta 2003, na da nufin kiyaye rayuwar yara a jihar.
Amma abin takaici, kotuna da ke da alhakin tabbatar da wadannan dokokin, sun yi watsi da wasu tanade-tanaden, musamman a shari’ar da ake yi wa yara, duk da tanadin Sashe na 213 na Dokar Kare Hakkin Yara ta Nijeriya da Sashe na 160 na Dokar Kare Hakkin Yara ta Jihar Sakkwato.
Doka ta haramta kotuna amfani da kalmar ‘mai laifi’ ko ‘wanda aka yanke wa hukunci’ a yayin da ake magana kan yara da aka gurfanar a kotu.
Sai dai bincikenmu ya gano cewa kotuna kamar Babbar Kotun Shari’a ta Musulunci da kuma Babbar Kotun Majistare da ke Sakkwato, suna amfani da wadannan kalmomi ba bisa ka’ida ba, a duk lokacin da suka yi zama a matsayi na musamman a kan shari’ar yara.
“An yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara daya ko biyan tarar Naira 30,000,” kamar yadda yake a rubuce a takardar da wani alkalin Kotun Shari’ar Musulunci ya bayar a kan daya daga cikin yaran a watan Yulin da ya gabata.
Haka lamarin yake a Babban Kotun Majistare ta Sakkwato inda alkali ya rubuta hukuncin nasa a wata shari’a tsakanin daya daga cikin yaran mai suna Suleiman Usman da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta Nijeriya a watan Mayu.
Takardar umarnin shigar da yaron gidan yari ta kunshi ‘kalmomi’ da aka haramta amfani da su a shari’ar kananan yara a jihar.
Wani mai fafutukar kare hakkin yara, Usman Ismail, ya ce rashin bin dokokin kare yara da kotu ke yi, koma-baya ne ga tsarin shari’ar Nijeriya.
Ya kuma dora laifin a kan rashin kafa kotu ta musamman domin sauraron shai’ar yara.
Ya ce, “Tsarin shari’ar kananan yara a Nijeriya na bukatar kotuna na musamman, kamar yadda muke da su kan harkokin zabe.
”Al’adar kyale kotunan yau da kullum su saurari shari’o’in kananan yara a wasu lokuta, shi ne dalilin tsawaita shari’ar, wanda ba dole ne ba.
“Dalili shi ne saboda ayyuka sun yi wa kotunan yawa, don haka dole a riƙa samun irin wannan. Dole a samu tagaro.
“Bayan kafa dokoki, ya kamata gwamnatin Nijeriya a dukkan matakai su nuna da gaske suke yi, wajen kare walwalar yara da hakkokinsu saboda su ne masu gina kasar nan nan gaba,” in ji Usman.
Za mu bincika — Gwamnati
Ma’aikatar Jin dadin Jama’a da Jin kai ta Jihar Sakkwato ta musanta cewa wasu daga cikin yaran da ake tsare da su a gidan yari na Sakkwato sun shafe watanni ko shekara ba a gurfanar da su a kotu ba, ko kuma yanke musu hukunci.
“Ba ni da masaniya game da shari’ar fursunonin, don haka ban san abin da bincikenku ya gano ba ba,” in ji kakakin Ma’aikatar, Ummu Abubakar, yayin da take sada wakilin Aminiya da Daraktan Jin dadin Jama’a na Ma’aikatar, Yusuf Sani.
Daraktan ya ce, a iya saninsa, an tsare wasu daga cikinsu a gidan yarin ne na wani dan lokaci, amma bai san cewa wasunsu sun shafe shekara guda ba tare da yanke musu hukunci kan laifukan da ake zargin su da aikatawa ba.
“Yanzu mu ke jin cewa akwai yara a da aka tsare tsawon shekaru ba tare da an yanke musu hukunci ba. Za mu bincika,” kamar yadda Yusuf Sani ya yi alkawari.
Ya kara da cewa, domin inganta jin dadin fursunonin, ofishinsa na gab da samun amincewar Gwamnan Jihar Sakkwato Aliyu Ahmad domin sake gyara Gidan Gyaran Hali na jihar.
An gudanar da wannan binciken ne, tare da tallafi daga Gidauniyar Tiger Eye da ke kasar Ghana da Gidauniyar MacArthur, da ke kasar Amurka.