Yadda abinci mafi tsada a Ghana ya hallaka mutane

Hukumar Tantance Ingancin Abinci da Maguguna ta kasar Ghana, ta tabbatar wa kafar labarai ta BBC rasuwar al’ajabi da wadansu mutum biyar suka yi a wani kauyen Jihar bolta, bayan cin daya daga cikin abincin kasar mafiya shahara wato Banku da miyar kubewa. Hankulan mazauna kauyukan jihar sun yi matukar tashi, saboda rasuwar da wadansu […]

Yadda abinci mafi tsada a Ghana ya hallaka mutane

Hukumar Tantance Ingancin Abinci da Maguguna ta kasar Ghana, ta tabbatar wa kafar labarai ta BBC rasuwar al’ajabi da wadansu mutum biyar suka yi a wani kauyen Jihar bolta, bayan cin daya daga cikin abincin kasar mafiya shahara wato Banku da miyar kubewa.

Hankulan mazauna kauyukan jihar sun yi matukar tashi, saboda rasuwar da wadansu mazauna daya daga cikin kauyukan su biyar suka yi.

Hukumar Tantance Ingancin Abinci da Magungunan ta ce, tana zargin masarar da aka yi amfani da ita wajen tuka Bankun ce sanadiyyar mutuwar wadannan mutane bayan da suka ci Bankun.

Yanzu haka dai, hukumar ta ce ta fara binciken kwakwaf don gano musabbabin rasuwar mutanen, yayin da mazauna kauyen da kewaye suke fargabar yaduwar wannan matsala.

Hukumar ta ce za ta fara bincikenta ne ta hanyar gwajin samfurin abincin da mutanen suka ci domin ganin ingancinsa, sannan hukumomin tsaro da kuma shugabannin gundumar da lamarin ya faru ma suna da rawar da za su taka wajen gano abin da ya haddasa rasuwar mutanen da kuma tabbatar da cewa ba a sake samun irin wannan matsala ba.