Yadda abinci mai guba ya hallaka mata da ’ya’yanta 3
Wani abin alhini ya auku a garin Masaka da ke karamar Kukumar Karu a Jihar Nassarawa inda aka gano wata matar aure tare da ’ya’yanta 3 a mace a cikin dakinsu. An dai gano gawarwakin mamatan ne a ranar Talatar makon jiya bayan shafe wunin Litinin suna kulle a cikin dakinsu a gidan da iyalan […]

Wani abin alhini ya auku a garin Masaka da ke karamar Kukumar Karu a Jihar Nassarawa inda aka gano wata matar aure tare da ’ya’yanta 3 a mace a cikin dakinsu.
An dai gano gawarwakin mamatan ne a ranar Talatar makon jiya bayan shafe wunin Litinin suna kulle a cikin dakinsu a gidan da iyalan suke haya a Unguwar Eriya 1 a garin Masaka ba tare da sanin halin da suke ci ba.
A zantawarsa da Aminiya, mijin matar mai suna Mista Godwin Bello wanda ke aikin gadi a wani gida a Abuja, ya ce ya ziyarci iyalansa a ranar Lahadin makon jiya kamar yadda ya saba duk mako, sannan ya yi ban-kwana da su da misalin karfe 5 na maraicen ranar.
“Daga baya na kira matata ta waya da misalin karfe 7 na dare a ranar don sanar da ita na isa lafiya har take ba ni hakuri a kan rashin yin abinci kafin barowata gida. Na ce da ita ba matsala ai ba zan rasa abinci ba a gidan maigidana. Da gari ya waye na sake kiran wayarta domin gaisawa da iyalaina kamar yadda na saba yi duk safiya, amma har wayar ta katse ba a dauka ba. Da farko ban nuna damuwa sosai ba kasancewar a baya hakan ya taba faruwa da ya sa na bar wurin aiki na dawo, amma bayan isowata sai na samu ta bar wayar a daki sannan na gano ta a gidan wata kawarta da ta kai ’ya’yanmu su zauna ita kuma tana shirin shiga kasuwa,” inji shi.
Ya kara da cewa: “A lokacin ne ta ce da ni ba ta son zuwa kasuwa da wayarta, amma sai na nuna hakan bai dace ba. To da na buga wayarta ba ta dauka ba, da farko ban damu ba sosai kamar na wancan karo. Da maraice ta yi ne ba tare da nasarar yin waya da ita ba, sai na kira wani baffanta da ke kauyen Auta-Balaifi a kusa da garin don ya taimaka ya je ya duba su. Sai dai ya ce ana ruwan sama sosai a inda yake kuma ga shi dare ya yi, amma zai bari har sai da safe. Kuma ba ni da lambar wayar wani a gidan saboda bai wuce mako daya ba ke nan da muka kaura zuwa gidan bayan mun shafe kamar shekara 8 a wani gidan daban a garin inda muke zaune tun lokacin da na aure ta.”
“To da na ga gari ya fara wayewa ba tare da samunta a waya ba, sai na taso daga inda na ke aiki, na tafi gidan inda na isa da misalin karfe 5 na safe. Bayan isa ta sai na samu dan uwanta shi ma ya iso sai kuma wani dan uwana, suna tsaye a kofar dakin saboda yana rufe ta ciki. Nan na rasa abin da yake yi mini dadi kasancewar tun a lokacin hankalina ya tashi na san cewa ba lafiya, bayan na kula da takalmarta a wajen kofar dakin ga kuma dakin a rufe daga ciki,” inji shi.
Ya ce, “Daga nan sai na keta ragar da ke jikin barandar dakin sannan na balle kofar dakin, ina shiga sai ga matata da ’ya ‘yanmu 3 a kwance kowa da alamar kumfa tare a kasan bakinsa kuma ba sa numfashi. Na girgza matuka, bayan na dan samu kaina ne jama’a suka ba ni shawarar in je ofishin ’yan sanda don sanar da su abin da ya faru.”
Magidancin ya bayyana sunayen iyalan nasa da Gloria Godwin matarsa da suka shekara 8 da aure, sai dansu babba Jetro mai shekara 7 da ke aji 2 a makarantar firamare da Jewel mai shekara 5 da ke aji 2 a makarantar rainon yara, sai kuma Jenifer da ke neman shiga shekara ta 3. Ya ce matarsa da kanta ta sayawa ’ya’yansu 2 sababbin littattafan rubutu na makaranta da takalma daga kasuwancin sayar da dafaffiyar gyada da take kaiwa kasuwar garin. Ya ce ya samu ta kintsa littattafai da takalman yaran da niyyar kai su makaranta a ranar Litinin ta makon jiya da aka bude makarantu bayan dawowa daga hutu. “A zuwan baya-baya da na yi na wannan makon ta shaida min cewa ta samu aikin gida a cikin Abuja amma saboda ba za ta iya tsallake aikin gonar da take yi ba ta yanke shawarar za ta aike wata ’yar wanta da ta gama karamar sakandare ta fara aikin, idan ta gama aikin gonar sai ita ta karbi aikin,” inji shi.
“Ashe Allah Ya sa yarinyar ba za ta samu zuwa ba, da watakila da ita za a ci abincin da suka ci da muke kyautata zaton yana da guba ko an sa guba a cikin tukunyar da aka dafa shi wanda ya yi ajalinsu bayan sun ci,” inji shi.
Ya ce bayan isowar ’yan sanda gidan, sun dauki tukunyar girkin wadda ke da sauran abincin da mamatan suka ci wanda taliyar Indomi ce, sai kuma jakar leda 2 na taliyar da aka yi amfani da ita.
Ya ce ’yan sandan sun kai gawarwakin mamatan zuwa wani asibiti da ke garin Maraba inda aka gudanar da gwaji a kansu kafin daga bisani aka binne su da maraicen ranar a garin Masaka.
Mista Godwin ya ce duk da cewa akwai zargin guba aka zuba a abincin da iayalansa suka ci da dare, ya tabbatar da cewa bai san matarsa da wata matsala ta rashin jituwa da kowa ba, haka shi ma. Ya ce sun kuma rabu da kowa lafiya a gidan da suka zauna na tsawon shekara 8 gabanin dawowarsu zuwa wannan gida mako daya kafin aukuwar lamarin, sannan ya ce ba a bi su wani bashin kudin haya ba.
Da aka tuntubi, Babban Jami’in ’Yan sandan Masaka CSP Boniface M. ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ya mika rahotonsa ga hedkwatarrsu da ke Lafiya don ci gaba da bincike a kan lamarin.
Aminiya ta samu labarin cewa bayan aukuwar lamarin, wadansu matasa sun yi dafifi a gidan tare da bukatar sai a mika musu wata da ake zargi da hannu a lamarin ko su banka wa gidan wuta. Hakan ya biyo bayan kwalalar da wata mata ce ta yi a kasuwar garin inda ta ce tana da hannu a mutuwar mamatan, sai dai ba a tabbatar da ko matar tana da cikakken hankali ba.
Wanda aka yi wa rashin ya ce: “Na yi ta ba matsan hakuri tare da nuna musu cewa gidan na haya ne idan suka kona shi lallai za su sake jawo min karin wata fitinar, sai dai ba su dakatar da boren ba har sai da ’yan sanda masu yawa suka zo unguwar suka tarwatsa su.”