Yadda abinci ya kashe ‘yan gida daya a Zamfara

Lamarin ya gigita mai gidan wanda da kyar aka samo shi a kidime cikin daji

Yadda abinci ya kashe ‘yan gida daya a Zamfara

Mutum bakwai ‘yan gida daya sun mutu bayan sun sha wani fate-fate a kauyen Augi da ke Karamar Hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara.

Wani dan uwan mamatan ya shaida wa Aminiya cewa abun ya faru ne bayan ‘yan gidan sun ci abincin da wata ‘yar uwarsu mai shekara 12 ta girka.

“Ta kawo tsakin masara ta ce wa mahaifiyata za ta yi fate-fate ita muka ta ba ta izinin yin girkin.

“Ta bukaci mahaifiyar ta ba ta sinadarin dandano na ‘Ajino-Motto’ amma uwar ba ta ba ta bayar ba, watakila saboda aikin da take yi ya dauke mata hankali.

“Daga nan sai yarinyar ta shiga dakin uwar domin ta dauko da kanta; amma aka yi rashin sa’a ta dauki gishirin lalle a matsayin sinadarin dandanon, ka san suna kaman da juna sosai.

“To da gishirin lallen ta yi girkin a matsayin sinadarin dandanon”, inji Yahaya.

Ya kara da cewa,”Da ta gama sai ta zuba nata ta kuma sa wa kaninta da kannenta mata uku da mahaifiyar da kuma kishiyar mahaifiyar.

“Bayan kamar awa daya da cin abincin sai suka fara ciwo suna karkarwa kumfa na fita daga bakinsu.

“Ba a dade da haka ba sai yarinyar da kannenta hudu suka mutu.

“Wadanda suka rasun su ne Maryam, Rabi, Fatima da Muhammad da kuma ita Maimuna.

“Mahaifiyar da kishiyar kuma sun rasu ne bayan an kwantar da su a wani asibiti a Bungudu.

“Yayarta da ta ziyarci gidan a ranar ita ma ta ci abincin amma tana samun sauki a asibitin”, inji shi.

Wakilinmu ya ce abun da ya faru a cikin iyalan ya dimauta mai gidan har ya shiga jeji, daga baya aka tura mutane suka nemo shi, inda suka same shi a gigice.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja