Yadda ado yake kara wa mace daraja

A al’adance da kuma  Musulunce kwalliya abu ne mai muhimmanci musamman ga ’ya mace, domin kwalliya da adon da ya dace ga mace yana kara mata kima da daraja a idon alumma. Musulunci rayayyen abu me da ya dace da kowane irin zamani, kuma ba shi da sandararren tunani, ya yarda mace ta yi ado, […]

Yadda ado yake kara wa mace daraja
Yadda ado yake kara wa mace daraja

A al’adance da kuma  Musulunce kwalliya abu ne mai muhimmanci musamman ga ’ya mace, domin kwalliya da adon da ya dace ga mace yana kara mata kima da daraja a idon alumma. Musulunci rayayyen abu me da ya dace da kowane irin zamani, kuma ba shi da sandararren tunani, ya yarda mace ta yi ado, ta sanya kaya masu kyau, kuma za ta iya yin jagoranci a wasu abubuwan da suka dace da ita a rayuwar dan adam, kuma ta ci ta sha duk abinda take so kamar yadda namiji yake yi.
Don haka halas ne ga mace Budurwa ko bazawara, ta shafa turare ta sanya zobe da sarka da Awarwaro, ko ta rina gashi da yin lalle da shafa Janbaki, da Janfarce da sauransu.  Amma fa irin yadda addinin Islama ya tanadar.   Haka nan mace za ta iya yin zane a fuska wanda zai kara mata kyau, duka wadannan halas ne ga budurwa, amma da sharadin ba ta yi haka ne don ta  yaudari namijin da yake son ya aureta ba.  Don kada ya dauka nata ne na asali, don haka wajibi ta sanar da shi ta yi haka ne don yin ado.
Ita kuwa Matar Aure tana da damar yi wa mijinta kwalliya da dukkanin kayan Ado da suka hada da: Rina gashi ko sanya Janfarce ko karin gashi da yin zane a fuska da yake kara kyau.  Haka kuma sanya sarka da zobe da awarwaro da lalle, dukkaninsu halas ne macen Aure ta yi wa mijinta ado da su matukar ba ta bayyanasu ga wasu mazajen ba, mijinta da muharramanta ne kadai ke da ikon gani. Hakazalika matar aure tana iya fesa turare idan za ta fita unguwa amma ya kasance ba mai kanshin da zai iya daukar hankalin mutane ba, musamman maza.
Babu shakka musulunci da al’ada sun bai wa mace damar yin kwalliya da ado, matukar kwalliyar ba za ta bude hanyar yin fasadi ba, amma kwaskwarima da maida tsohuwa yarinya ta hanyar kwalliya ga mace abu ne me kyau da ya kan kara mata kima da martaba a idon mazaje, kai har ma da kawaye.
Ibrahim Hamisu ya rubuto ne daga Kano, kuma za a iya samunsa a 08060651676.