Yadda aiki tukuru ya samar mana da lambar yabo ta duniya – Kwanturola Bashar

Hukumar Kwastam ta Duniya (WCO) ta girmama Rundunar Kwastam ta Tinkan mai kula da gabar tekun Legas a Najeriya. An girmama rundunar ne saboda irin hobbasan da ta yi a cikin shekara biyu, musamman ma kamen manyan makamai da miyagun kwayoyi da ake yin fasa kwaurin shigowa da su cikin kasa. Aminiya ta samu zantawa […]

Yadda aiki tukuru ya samar mana da lambar yabo ta duniya – Kwanturola Bashar

Hukumar Kwastam ta Duniya (WCO) ta girmama Rundunar Kwastam ta Tinkan mai kula da gabar tekun Legas a Najeriya. An girmama rundunar ne saboda irin hobbasan da ta yi a cikin shekara biyu, musamman ma kamen manyan makamai da miyagun kwayoyi da ake yin fasa kwaurin shigowa da su cikin kasa. Aminiya ta samu zantawa da Kwamandan Rundunar mai barin gado, Kwanturola Bashar Yusuf, wanda ya yi karin haske a kan dalilin samun wannan lambar yabo:

 

Ko za ka yi mana karin haske game da wannan lambar yabo da rundunarku ta samu daga Hukumar Kwastam ta Duniya (WCO)?

Da farko ina godiya ga Allah (swt) da Ya sa Najeriya ta samu irin wannan lambar yabo da girma daga Hukumar Kwastam ta Duniya, wadda t ba Rundunar Kwastam ta Tinkan. Bayanin da Babban Sakataren hukumar ta WCO, Kunio Mikuriya ya yi cikin satifiket din da ya sanya wa hannu, ya nuna cewa an girmama mu ne saboda irin rawar da rundunarmu ta Tinkan ta taka a cikin shekara biyu, wajen dakile miyagun ayyukan fasa kwauri da ceto al’ummar Najeriya daga fadawa cikin kuncin rayuwa. Muna jinjina wa duka jami’an Kwastam da ke aiki a gabar tekun Tinkan da ’yan kasuwa da sauran jama’a da muke hulda da su; wadanda suka taimaka wajen ba mu hadin kai da ya kai ga nasarar tara kudaden harajin fito fiye da Naira miliyan dubu 300 da muka samu a bara 2017. Ka ga ke nan Rundunar Kwastam ta Tinkan ta samar da kashi daya bisa uku na jimlar kudi Naira tiriliyon 1.7 da Rundunar Kwastam ta tara a kasa baki daya.

Wadanne irin ayyukan fasa kwauri kuka dakile da ya kai ga samun wannan lambar yabo?

Kadan daga ciki sun hada da kamen da muka yi na hodar ibilis mai darajar kudi fiye da Naira miliyan dubu biyu da kamen miyagun kwayoyi na Tramadol masu yawan gaske da matasa suke sha ba tare da kula da illarsu ga rayuwarsu ba da kamen manyan bindigogi (pump action). Irin wadannan bindigogi sun fi AK 47 illa da tayar da hankali

saboda za a iya kashe mutane 40 gaba baya a lokaci daya da harbin irin wannan bindiga guda daya. Ba kamar AK 47 da ake harbin mutum daya tak da ita ba. A lokaci daya muka kama wadannan bindigogi guda 2010. A baya ma mun sha kama kasa da haka da dubunan harsasai. Ba a taba yin irin wannan kame a Najeriya ba sai a wannan lokaci da muka jajirce da yin aikin sadaukar da kai domin kare mutuncin kasarmu Najeriya. Wannan manyan kame ne ya sa hukumar WCO da hadin gwiwar Rundunar Kwastam ta Najeriya suka ga cewa mun cancanci a karrama mu da lambar yabo, wacce ba a taba samun irinta a tarihin kafuwar rundunar kwastam ta Tinkan ba.

Wane sako za ka aika wa ’yan kasuwa?

Sakona ga ’yan kasuwa shi ne, lambar girma da muka samu tana nuna mana cewa jan aiki ya same mu fiye da wanda muka yi a baya da za mu tashi tsaye wajen lalubo hanyoyin kare mutuncin kasa da bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Ta bangaren Kwanturola-Janar, Kanar Hameed Ali (mai ritaya) fa, wacce gudunmowa ya ba ku da kuka kai ga wannan nasara?

Babbar gudunmawa da kowane shugaba zai bayar ita ce ya ba ka damar yin aiki daidai da yadda doka ta ce a yi. Shekara 2 da ya turo ni nan Tinkan, Wallahi bai taba kirana ya ce in yi kaza in bar kaza ba. Ya mutunta ni, ya bar ni na yi aikin kare mutuncin kasata tsakani da Allah kuma na ji dadin haka. Ina rokon Allah Ya saka masa da alheri, ya sa mu rika samun shugabanni irinsa, amin.