Yadda aikin ci gaban shiri yake wajen daukar fim – Bashir Datti
Bashir na daya daga cikin mutanen bayan fage a masana’antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood). A hirarsa da Aminiya ya bayyana yadda aikin bangaren ci gaban shiri yake yayin daukar fim, matsalolin da ya fuskanta da kuma burinsa a masana’antar. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Ko za mu fara da takaitaccen tarihinka? Da farko dai sunana […]
Bashir na daya daga cikin mutanen bayan fage a masana’antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood). A hirarsa da Aminiya ya bayyana yadda aikin bangaren ci gaban shiri yake yayin daukar fim, matsalolin da ya fuskanta da kuma burinsa a masana’antar. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Ko za mu fara da takaitaccen tarihinka?
Da farko dai sunana Bashir Lawandi Datti. An haife ni a Jos da ke Jihar Filato, na yi karatun boko a garin Jos.
Tun yaushe ka fara harkar fim, sannan me ya ja hankalinka ka shiga harkar?
Na fara harkar fim tun a shekarar 2001, na fara fitowa a yaro ne. Na fara da fim din Magaji Mijinyawa mai suna Kallon Gajimare, daga nan na fito a fim din Gori, wanda Ali Nuhu ya ba da umarni. Mun fito a matsayin ’ya’yan jaruma Saima Muhammad. Ka san Kannywood za ka shiga da niyyar yin wani abu, a karshe sai ka ga ba shi ka yi ba, sai ka ga ka fi kwarewa a kan wani abu. Na ci gaba da bin Ali Nuhu zuwa wuraren aikin daukar fim, inda shi ne ya nuna mini aikin ci gaban shiri.
Bayan nan na hadu da wani darakta a Jos mai suna Salisu Mu’azu, sai ya kara zaunar da ni ya koya mini aikin ci gaban shiri. Hakan ya sa na rike wannan bangare a matsayin sana’a a Kannywood.
Abin da ya ja hankalina na shiga harkar fim kuwa zan iya cewa sha’awa ce ta sa hakan. Idan ban manta ba, ko lokacin da mahaifinmu ya bar Maiduguri ya dawo Jos ba na kallon fina-finan Hausa, na fi kallon fina-finan Turanci. Sai na je Kano wurin kanwar mahaifinmu, na zauna a wurinta kusan wata biyu, a lokacin ta fara sanya mani ra’ayin fim din Hausa. Idan ina gida sai ta sa fim din Hausa, babu inda zan je dole in tsaya in kalla. Tun daga lokacin sha’awar ta fara shiga raina. Bayan na dawo Jos ma sai na ci gaba da kallo. Wata rana jarumi Tijjani Faraga ya zo gidanmu, a lokacin yana neman yayata mai suna Iyami, ni kuma na dawo daga buga kwallo sai ya ji ina wakar fim din Mujadala. Sai ya ce mata ai wannan yaron zai yi kyau da fim, daga nan ya shigo da ni harkar fim.
Akwai bangarori da dama a masana’antar fim, kama daga fitowa a fim, ba da umarni, shiryawa da sauransu, me ya sa ka zabi bangaren ci gaban shiri?
Ina da burin zama darakta, to hanya mafi sauki da mutum zai zama darakta ita ce ta samun kwarewa a bangaren ci gaban shiri, domin duk fitowa bayan fitowa za ka sani. Ta yi kyau ko ba ta yi ba, dole ka karanta yadda aka tsara labari, sannan za ka rika lura da yadda kowane darakta yake aikinsa. Daga nan za ka rika koyo, sannan bangaren ci gaban shiri yana son natsuwa. Idan fim ya yi kyau to ka tabbata bangaren ci gaban shiri ya taka babbar rawa a fim.
Wadanne matsaloli ka fuskanta a harkar fim?
Na fuskanci matsaloli masu yawa. Matsala ta farko ita ce, a zahirin gaskiya a Jos na fara aikin ci gaban shiri, ana yin aikinsa a cikin takarda. Bayan na koma Kano da aiki kuma su mutanen can wadansu ba su san amfanin takardar ci gaban shiri ba, da ka suke aikinsu. Matsalar ita ce, sun ga kamar na zo musu da sabon abu ko kuma ina nuna musu ba su san aiki ba, domin duk lokacin da za a dauki wata fitowa ina bayan mai kyamara, sannan ina ta rubutawa, ina kuma tambayar wannan mai kyau ne ko marar kyau. Na sha wahala kafin na fahimtar da mutane amfanin aikin ci gaban shiri. Sannan na zauna da masu tace hotuna, da yawansu idan an kammala daukar fim an ba su takardar aikin ci gaban shiri, sai su ajiye a gida, ba za su yi aiki da shi ba. Amma bayan na zauna da su sai na fahimtar da su amfanin wannan takarda, a nan suka fahimci lallai aiki da wannan takardar zai saukaka musu aikinsu.
A bangaren nasarori fa?
Na samu nasarori a harkar fim, saboda na fara harkar tun ba ni da komai. A cikin harkar na tara abin da na shirya fim kuma na koyi abubuwa da yawa, domin tun ina aikin ci gaban shiri har na zama mataimakin darakta. A dalilin fim na sayi mota kum nake biyan kudin karatun da nake yi.
Wadanne fina-finai ne ka yi aiki a matsayin jami’in ci gaban shiri?
Fina-finan suna da yawa, duk fina-finan kamfanin FKD Production na Ali Nuhu, tun daga kan Sai Wata Rana har zuwa yanzu ni nake masa aikin ci gaban shiri. Sannan fina-finan kamfanin Saira, tun daga kan kona Gari har yanzu ni nake masa aiki.
A bara kun shirya fim mai suna Gidan Aure, fim din ya fita kasuwa, me za ka ce a kan fim din?
An samu nasara sosai, domin a cikin nasarar ma har na sayi mota, sannan ma’aurata da yawa sun ilimantu da amfanin tattauna matsalaloli tsakaninsu.
Me kake hango wa Kannywood a nan gaba?
Ina hango mata ci gaba, saboda kamar ni ka ga na koma karatu sosai, sannan akwai ire-irena da yawa da suka koma karatu, irinsu Nazir danhajiya da Yunusa Mu’azu. Ka ga gaba harkar za ta dawo sai da mai ilimi, ka ga duk abin da aka ce yana tare da masu ilimi kai ma ka san zai bunkasa. Don haka a gaba idan ba ka da ilimin harkar ba za ka iya ba. Ina ba duk wanda yake harkar fim shawarar ya koma karatu.
Wane buri kake da shi a harkar fim?
Burina masana’antar fim ta bunkasa ta kai matsayin da idan an yi fim sai duniya ta sani. A wuce kasuwancin kasuwar kofar Wambai.
Wadanne matsaloli ne suke ci wa Kannywood tuwo a kwarya, sannan wadanne hanyoyi za a bi wajen magance su?
Matsalolin sun hada da rashin karatu daga bangaren masu yin sana’ar, akwai mutanenmu da suke yin harkar da ka, don haka ina so su je su karo ilimi a kan harkar fim, ba wai na ce musu jahilai ba. Matsala ta biyu ita ce bangaren zabar ’yan wasa. Wani lokaci idan za a zabi ’yan wasa ba a duba cancanta, mukan duba wane ne yake kusa da ni, sai in sa shi, amma idan za ka dauko mutumin da ya dace ko da ba ku shiri, za a ga fim din ya fi kyau. Sai matsalar satar fasaha, mutum zai kashe kudinsa amma daga ya sake fim sai ya ga na masu satar fasaha jingim. Don haka ina rokon hukumar kare hakki mallaka ta tashi tsaye wajen gudanar da aikinta. Wani lokacin masu kallo su ke ba da babbar gudunmuwar da ake yin fim marasa kyau, za su ce idan aka yi fim har ba jarumi wane, to ba za su kalla ba. Shi kuma mai fim zai ce kudi ya fito nema, don haka bari ya yi ta sa musu wanen da suke son ganin, koda kuwa bai cancanta ba. Ina so ’yan kallo su rika bin ma’anar labari, kada su ce sai wane da wane a cikin fim kafin su kalli fim din.
Tun bayan da na shirya fim din Gidan Aure, sai na dan daga kafa, sannan na sake komawa karatu, amma nan gaba zan zo musu da fim mai kayatarwa da ilimantarwa da kuma fadakarwa. Za su ga canji.