Yadda aikin titin jirgin kasa na Kano zuwa Kaduna ke tafiyar hawainiya

Ilahirin aikin a yanzu ya kai kimanin kashi 22.6 cikin 100.

Yadda aikin titin jirgin kasa na Kano zuwa Kaduna ke tafiyar hawainiya

Aikin titin jirgin kasa da ake gabatarwa daga Kano zuwa Kaduna da aka fara a karkashin gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na ci gaba da yin tafiyar hawainiya bayan da gwamnatin ta shude ta gaza kammala shi balle ta bude shi.

Wani bincike da Aminiya ta gabatar a cikin watannin nan, ya gano cewa sai an yi da gaske za a iya kamalla aikin nan da shekara daya mai zuwa.

A watan Yunin shekarar 2021 ne gwamnatin Buhari ta kaddamar da aikin amma ba a fara gudanar da shi ba sai a ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2022 da zimmar kammallawa a ranar 30 ga watan Yunin bana.

Kamfanin China Civil Engineering Construction Corporation Limited (CCECC) ne yake aikin titin jirgin mai nisan kilomita 200, inda aka ce in an kammala jirgin da za a kawo zai iya gudun kilomita 150 a cikin awa daya aikin da aka bayar da kwangilarsa a kan Dala biliyan 1.2.

Daya daga cikin manufofin aikin shi ne a fadada sufurin jiragen kasa tare da hade titin jirgin da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya zarce zuwa Kano domin kara inganta harkokin kasuwanci da saukaka safarar kayayyakin amfaninn gona da saukaka tafiye-tafiye ga jama’a musamman masu karamin karfi.

Titin ya tashi ne daga Unguwar Zawaciki a birnin Kano ya haura zuwa garin Kanwa a Karamar Hukumar Madobi da sauran kauyukan da ke kan hanyar Kano zuwa Kaduna ta Karamar Hukumar Ikara a Jihar Kaduna zuwa Makarfi inda kamfanin yake da babban yadinsa na ajiyar kayan aiki da ma’aikata.

Daga nan ne kuma aikin zai ci gaba zuwa garin Zariya ya zarce zuwa tashar jiragen kasa ta Rigasa a Kaduna.

Binciken Aminiya ya gano cewa da sauran rina a kaba kafin aikin titin jirgin kasan ya kammala domin akwai ayyuka da dama da har yanzu ba a fara su ba yayin da da yawa daga cikinsu aka kai wata gaba, al’amarin da ke nuna cewa za a dauki dogon lokaci kafin a kammala aikin.

Duk da kamfani daya ne yake aiwatar da aikin, an raba shi zuwa gida takwas, kamar yadda Aminiya ta gano.

Kashi biyar a bangaren Jihar Kano yayin da kashi uku suke bangaren Jihar Kaduna. Bangarori biyar da aka raba sun hada da Zawaciki inda nan ne mafara, sai Madobi, Kiru, Yako zuwa Makarfi.

Sauran yankuna ukun da suka rage, sun tashi ne daga Makarfi zuwa Rigasa wanda babu abin da aka yi a wannan bangare.

“Akalla za mu iya daukar wata biyar kafin mu gama gina wadannan magudanun ruwan da suke yankin Madobi kawai,” daya daga cikin ma’aikatan da ya nemi a sakaye sunansa ya shaida wa wakilinmu.

Yayin da wasu wuraren aka fara gina magudanun ruwan, da yawan wuraren ba a fara ba sai dai idan ba a duk hanyar za a gina magudanun ba.

Ma’aikata a yankin Kwanar Dangora har yanzu suna sharewa da gina tubalin da za a dora kwagirin layin dogon ne. Sai dai za a iya cewa aikin gina tubalin da za a gina layin dogon ya kai matakin kaso 90 cikin 100.

“Za mu iya daukar wata guda kafin mu kammala aikin wannan gadar,” wani injiniya a daya daga sassan aikin ya shaida wa Aminiya.

Sai dai a wata ziyara da wakilinmu ya sake kai wa wannan waje bayan wata daya, ci gaban aikin gadar bai wuce kaso 10 cikin 100 ba.

Zai yi wuya a gama nan da shekara daya

Yayin da yake tofa albarkacin bakinsa, wani jami’in tsaro da ke gadin ma’aikata ya bayyana cewa,  “Wannan aiki za a iya daukar shekara ba a gama ba, magana ta gaskiya ke nan.

“Su ma m’aikatan ba sa so a gama da wuri domin dan abin da suke samu zai tsaya. Akasarinsu kuma mutanen wadannan kauyukan ne,” in ji shi.

Wakilin Aminiya ya gano cewa da yawa daga wuraren da ake gudanar da aikin, ba a wuce kaso 40 zuwa 50 a ma’aunin kammalawa.

Hakazalika, daga cikin tashoshin da jirgin zai rika tsayawa don dauka da sauke fasinjoji da kayansu, babu ko daya da aka soma ginawa kawo yanzu.

A watan Afrilun shekarar 2023, Majalisar Dokoki ta Kasa ta sanar da sabon mai daukar nauyin ci gaba da aikin ta fuskar fitar da kudi, wato Bankin Ci-gaba na China (China Development Bank, CDB) wanda ya karbi ragamar aikin daga hannun wani Bankin Nedim Bank na China a karkashin wani tsarin ciwo bashi na shekarar 2016 zuwa 2018 na Gwamnatin Tarayya.

Majalisar ta ba da sahalewar a ciwo bashin Dala 22.8 a shekarar 2020 a karkashin matsakaicin tsarin ciwo bashi inda kamfanin da ke kwangilar da Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya za su fara aiki da sabon bankin a kan Dala miliyan 973.5.

A kwanan nan, an ga Sanata mai wakiltar Kogi a karkashin Jam’iyyar APC, Jibrin Isa yana sukar yadda aka samu tazarar tsakanin kudin da aka cire da farko, Dala biliyan 22.7 da wanda za a kashe yanzu Dala miliyan 973.5.

Aminiya ta lura mazauna yankunan da layin jirgi ya bi ta garuruwansa suke maraba da aikin domin a cewarsu, zai inganta rayuwarsu sosai tare da kawo musu ci gaba a harkokinsu na yau da kullum.

Haka suna da yakinin aikin zai kara dankon zumuci da alaka ta fuskoki daban-daban a tsakanin mazauna yankunan.

A cewar wasu daga cikinsu, baya ga bunkasa harkokin kasuwanci, hakan zai daga darajar garuruwansu musamman manoma wadanda suka yi imani idan layin dogon ya fara aiki, za su samu saukin safarar amfanin gona da sauran kayan ci gaba ta fuskar kasuwanci a tsakanin garuruwan yankin.

Baya ga tabbatar da ci gaba wajen samun saukin sufuri, layin dogon zai sama wa matasa da al’ummar yankunan da kuma baki ayyukan yi musamman manyan garuruwan da za a gina tashoshin da jirgin zai rika tsayawa.

Tsadar mai: Ma’aikata na cikin zullumi yayin da dan kwangila ya ajiye kayan aiki

Tashin gwauron zabo da man fetir ya yi a kwanakin da suka gabata inda ya ninka kudinsa kusan sau uku na matukar illa a kan aikin da ake gudanarwa, lamari da ya sa ma’aikatan da suke aikin a cikin zullumin da zai je ya dawo sakamakon ajiye wasu kayan aiki da aka yi.

A wata ziyara da wakilinmu ya sake kaiwa a babban ofishin dan kwangilar da ke Zawaciki, ya gano cewa an jibge wasu manyan motoci da ake amfani da su wajen jigilar daukar kasa, duwatsu da sauran kayan aiki.

Da suke magana a kan haka, wasu ma’aikata sun tabbatar wa Aminiya cewa tsadar man fetur ta sa an ajiye wasu daga cikin kayan aikin, al’amarin da ke nuna cewa da sauran rina a kaba.

“Ka ga yanzu an dawo da wasu motocin an ajiye saboda dole sai an sake zama an duba lamarin tsadar man nan. Shi wannan aiki, aiki ne da an tsara nawa za a kashe daga farkonsa har karshe, to ga shi kuma wani abu ya taso ba shiri,” in ji su.

Aiki zai ci gaba, amma ba za a gama da wuri ba — Masana

A tattaunawa da wani mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum musamman siyasa da kasuwanci, Dokta Kabiru Sufi ya ce akwai yiwuwar ci gaba da aikin amma ba a yanayin da aka dauko shi ba, domin kowace gwamnati tana da nata abubuwan da ta fi bai wa muhimmanci.

“Aikin zai iya tsayawa ya rika tafiyar hawainiya duba da yanayin kokarin da aka yi ta fuskar zuba kudi da sauransu daga gwamnatin da ta shude.

“Nawa aka bai wa dan kwangila da kuma tsare-tsare. Idan aka dubi wadannan abubuwa, to akwai yiwuwar a ci gaba da aikin amma ba a irin yanayin da aka faro shi ba.

“A kowace gwamnati da sha’anin mulki akwai ci gaba kuma irin wannan aiki, aiki ne da ko ma wace gwamnati ce ta zo ya kamata ta ci gaba da shi har a gama duk da cewa kowace tana da irin ayyukan da ta fi bai wa muhummanci. Amma dai, za a ci gaba,” in ji shi.

 

Da yake magana game da tasirin tsaro da kuma yanayin kasa, ya ce, “Dole idan aka dauko gabar aiki irin wannan a yi dubi ga wadannan sassa biyu ta fuskoki da dama domin tabbatar da an gama aikin yadda ya kamata.

“Idan aka samu matsala ko wani tsagaro, akan koma ne a yi gyara da tsare-tsare daidai da yanayin da aka tsinci kai a ciki, kuma na tabbata su yi hakan kuma suna da mafita a kan yadda za a shawo kan al’amarin.

“Idan muka yi maganar tsaro, dole an dauki matakai domin tabbatar da ba a samu matsala ba. Amma idan matsala ta zo, duk mai ruwa-da-tsaki a aikin har da ita kanta gwamnati, ana zama ne a duba tare a yi gyara domin tabbatar da cewa an gama aikin yadda ake da bukatarsa,” in ji shi.

A bangaren masanin tattalin arziki a Sashen Tsimi da Tanadi na Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Isiyaka Pedro cewa ya yi, “Babbar matsalar aikin na da nasaba da canjin gwamnati yayin da kammala aikin zai taimaka gaya wajen habakar tattalin arzikin kasa ta fuskar kasuwanci da ma’aikatu.”

Ya bukaci gwamnati ta yi kokarin shawo kan matsalar tsaro wacce ita ce babbar hanyar da ke kawo matsala ga sufuri mai inganci ga matafiya da ’yan kasuwa.

Dokta Shamsuddeen ya yi nuni da cewa tafiyar hawainiyar hanyar na kara wa aikin zama mai tsada lura ga canjin da ake samu a farashin Dala inda ya yi kira ga gwamnati ta yi kokarin tabbatar da kammala aikin a kan lokaci.

Duk yunkurin jin ta bakin masu ruwa-da-tsaki musamman Ma’aikatar Sufuri ta Kasa da Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya bai samu ba, bayan da suka ki cewa uffan lokacin da Aminiya ta tuntube su.

A wata ziyara da Ministan Sufuri, Sanata Sa’idu Ahmed Alkali ya kai inda ake aikin ya soki lamirin irin kayan da ake amfani da su wajen gudanar da aikin wadanda ya ce ba masu inganci ba ne.

Ministan ya bukaci ’yan kwangilar su yi duk mai yiwuwa wajen amfani da kayan aiki masu inganci domin kauce wa abin da ba a so ta fuskar tsaro da ingancin aiki.

Ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyara sansanin masu aikin da ke Makarfi a Jihar Kaduna.

Jagoran aikin kwangilar ya ce, ilahirin aikin a yanzu ya kai kimanin kashi 22.6 cikin 100 yayin da suka yi korafin matsalar tsaro na cikin dalilan da suke jawo tafiyar hawainiyar.