Yadda aka bai wa hammata iska a majalisar Turkiyya
Daga gidan yari, Atalay ya tsaya takarar kujerar majalisar dokokin lardin Hatay.
Faɗan ba-zata da ya kai ga zubar da jini ya barke a Majalisar Dokokin Turkiyya a yayin wata zazzafar muhawara a ranar Juma’a.
Rikicin ya ɓarke ne a lokacin da ’yan majalisar ke muhawara kan matsayin wani jigon ’yan hamayya, Can Atalay, da aka yi wa hukuncin dauri.
- Abba ya naɗa Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida
- An saki ɗaya daga cikin jiragen Gwamnatin Nijeriya da aka riƙe a Faransa
An soma muhawar ce bayan da kotun tsarin mulkin kasar a farkon wannan watan ta yi fatali da matakin da majalisar dokokin ta dauka na korar Can Atalay daga kujerarsa ta majalisar.
Sai dai a ranar Juma’a, wani jigo a majalisar, Ahmet Sik ya kare Atalay daga sukar da ’yan majalisar daga bangaren jam’iyya mai mulki suke yi masa.
“Ba abin mamaki ba ne kiran Atalay a matsayin dan ta’adda,” in ji shi.
“Sai dai ina so duk ’yan kasa su sani cewa manyan ‘yan ta’addan kasar nan su ne wadanda ke zaune a kan wadannan kujerun,” in ji shi, yana nuna bangaren da mafi rinjayen ’yan jam’iyyar masu mulki ke zaune.
Wannan furuci dai shi ne silar tayar da jijiyoyin wuya daga ‘yan majalisar dokokin jam’iyya mai mulki.
Ana tsakar ne haka ne aka fara fadan bayan da Alpay Ozalan, wani dan majalisa na jam’iyyar da ke mulki a kasar ta Turkiyya ya je har kujerarsa ya tunkude Ahmet Sik har kasa.
Wani hoton bidiyo da aka wallafa daga baya, ya nuna jami’ai na goge jini daga wajen da shugaban majalisar ke zama.
Jagoran babbar jam’iyyar hamayya, CHP, Ozgur Ozel, ya yi Allah-wadarai da tashin hankalin, yana mai cewa ya ji kunyar kasancewarsa a wajen.
Wane ne Can Atalay da aka yi rigima a kansa?
Can Atalay yana daya daga cikin mutum bakwai wadanda aka tuhuma a shekarar 2022 kuma aka yankewa hukuncin daurin shekaru 18 a gidan yari biyo bayan wata shari’a mai cike da rudani.
A shari’ar ce kuma aka yanke wa mutumin da ya samu lambar ta bayar da agaji, Osman Kavala hukuncin daurin rai da rai.
Daga gidan yari, Atalay mai shekaru 48 ya tsaya takarar kujerar majalisar dokokin lardin Hatay da girgizar kasa ta yi barna a babban zaben watan Mayun da ya gabata.
An zabe shi a matsayin mamba na jam’iyyar Ma’aikata ta Turkiyya, wadda ke da kujeru uku a majalisar dokokin kasar.
Sai dai wannan nasarar da aka samu a zaben ya haifar da takaddama tsakanin magoya bayan Shugaba Recep Tayyip Erdogan da shugabannin ’yan adawa wanda ya kai Turkiyya ga fuskantar rikicin tsarin mulki a bara.
Matakin da majalisar ta yanke a watan Janairu kan Atalay ya biyo bayan hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke wanda ya tabbatar da hukuncin da aka yanke masa, lamarin da ya tube masa rigar kariya.
Sai dai a ranar 1 ga watan Agusta, Kotun Tsarin Mulkin Kasar, wata hukumar da ke da alhakin yin nazari kan ko hukuncin da alkalan suka yanke ya bi ka’ida ta Turkiyya, ta yi watsi da hukuncin da Kotun Daukaka karar ta yanke.