Yadda aka ceto kananan yara 72 a Taraba

Mary Yakubu ‘yar shekara 40 ne da ‘yan sanda suka tsare bisa zargin sace yara kanana 72. An kama ta da yara 23 a karon farko kafin a sake gano sauran yaran a wurinta. Wakilin Aminiya ya gano cewa an kama Mary Yakubu ne a tashar mota sa’ilin da take kokarin tafiya da yaran wani […]

Yadda aka ceto kananan yara 72 a Taraba

Mary Yakubu ‘yar shekara 40 ne da ‘yan sanda suka tsare bisa zargin sace yara kanana 72. An kama ta da yara 23 a karon farko kafin a sake gano sauran yaran a wurinta.

Wakilin Aminiya ya gano cewa an kama Mary Yakubu ne a tashar mota sa’ilin da take kokarin tafiya da yaran wani garin daga Bali a Jihar Taraba.

Asirin Mary waddda malamar makarantar firamare ce a garin ya tonu ne bayan wasu da suka san cewa ba ita ce mahaifiyar yaran ba, sun tsaigunta wa ‘yan sandan da suka cafke ta.

Yayin gabatar da ita ga manema labarai a Hedkwatar Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Taraba, Mary ta yi ikirarin cewa iyayen yaran ne suka ba ta su ta nemi wanda zai iya rike yaran ta ba shi su.

Amma ‘yan sanda sun ce matar ta kwashi yaran ne da nufin kai su wani wuri da a sani ba. Ta kuma yaudari iyayen yaran ne ce wa zata sa su a makaranta.

Kakakin rundunar DSP David Misal ya ce bayan an gano yaran, an sake gano karin wasu yara 49 da ta dauka daga kauyuka daban-daban a kananan hukumomin Bali da Gassol.

DSP David Misal ya bayyana cewa an ceto yaran a garin Maraban Baissa na Karamar Hukumar Donga inda ta boye su da nufin kai su wurare daban-dabn a sassan kasar nan.

Yadda take samun yaran

Mary Yakubu kan shiga kauyuka tana yaudarar iyaye su ba ta ‘ya’yansu ta sa a su a makarantar Boko, a cewar Kakakin Rundunar. Kasancewar babu makarantun boko a kauyukan ya sa iyayen yara yarda su ba ta ‘ya’yansu.

Sai dai ‘yan sanda sun gano cewa matar tana ba da yaran ne ga mutane a matsayin masu yi musu ayyuka a gidajensu, ba tare da sanin iyayensu ba.

Bincike don ceto yara

Kama matar ya sa Gwamnatin Jihar ta ba da umurnin fadada bincike domin a gano gaskiyar yadda ita Mary Yakubu take yi da yaran.

Ana kuma zargin zargin akwai sauran yaran da ta dauka da ba ta riga ta fadi inda ta kaisu ba.

Gwamna Darius Ishaku ya kafa wani kwamiti na musamman a karkashin jagorancin mataimakinsa Alhaji Haruna Manu.

Kula da yaran da aka ceto

Ma’aikatar Mata da Jin Dadin Yara Kanana a Jihar ta karbi yaran su 72 inda ake lura da su a Jalingo kafin a tantance iyayensu da kuma kauyukan da suka fito.

Wata majiya a ma’aikatar ta ce yanzu haka an gano kauyukan da Mary ta dauko yaran sai dai ba su da hanyoyin mota ba makarantun Boko ba asibiti.

Hakan ta ce gwamnan jihar ya bayar da umurnin a samar da hanyar mota da makarantun firamare da asibiti a kauyukan, kafin hannanta yaran ga iyayensu.

Makomar Mary

Yanzu Mary Yakubu na can tsare a gidan yarin Jalingo har sai an kammala bincike a gurfanar da ita a kotu.

Tarihin matsalar a Taraba

An fara samun matsalar nan a jihar Taraba ne a shekarar 2015 sadda aka kama wani Fasto dan asalin Jihar Filato da yara 17 da ya dauko daga wani kauye a Karamar Hukumar Bali cewa zai kai su Jihar Filato ya sa su a makarantar boko.

Faston ya shiga hannu ne sadda yake kokarin ketarewa da yaran kogin Ibbi zuwa Jihar Filato.

Sai dai babu wata shaida da ta nuna ko an hukunta domin har zuwa ba a sanar da matakin da hukuma ta dauka a kansa ba.

Kama barauniyar kananan yara

Bayan nan, sijoji sun kama wata mata mai suna Ruth Okorokwo ‘yar asalin Jihar Imo dauke da yara uku da ta sato daga garin Numan da ke Jihar Adamawa da garin Jayda Iware na Jihar Taraba.

Dubun matar ya cika ne a ranar 13 ga watan Agustan 2019 a wurin da sojoji ke bincken ababen hawa a garin Sabon Gida da ke kan hanyar Jalingo zuwa Wukari.

Ruth Okoronkwo ta shaida wa ‘yan sanda cewa Allah ne ya kama ta domin ta dade tana satar kananan yara daga Arewacin kasar nan tana sayar da suu a kan Naira 200,000 ko fiye agarin Anaca da wasu sassan yankin Kudu masu Arewa.

A yanzu haka an gurfanar da wannan mata a gaban wani kotu a garin Jalingo don yin mata shari’a.