Yadda aka dakile zanga-zangar juyin juya-hali

A makon jiya ne tsohon dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore ya sanar shirinsa na jagorantar zanga-zangar juyin juya-hali a Najeriya mai taken ‘#RebolutionNow,’ inda kuma Hukamar Tsaron Kasa (DSS) ta yi caraf ta cafke shi a ranar Lahadi kuma take ci gaba da rike shi bayan kotu ta ba ta damar ta […]

Yadda aka dakile zanga-zangar juyin juya-hali

A makon jiya ne tsohon dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore ya sanar shirinsa na jagorantar zanga-zangar juyin juya-hali a Najeriya mai taken ‘#RebolutionNow,’ inda kuma Hukamar Tsaron Kasa (DSS) ta yi caraf ta cafke shi a ranar Lahadi kuma take ci gaba da rike shi bayan kotu ta ba ta damar ta ci gaba da rike shi na kwana 45 maimakon kwana 90 da ta nema.  Sowore ya yi kira ga ’yan Najeriya su ci gaba da zanga-zangar duk da kama shi aka yi.

A safiyar Litinin ce masu zanga-zangar ta #RebolutionNow suka fara zanga-zangar a wasu jihohi, sai dai abin bai yi wani tasiri ba.

Mai magana da yawun Hukumar DSS ya bayyana cewa su ke da alhakin kama shi kuma dalilinsu na yin haka shi ne zarginsa da ake yi na yunkurin hambarar da gwamnati mai ci.

Zanga-zangar ba ta yi tasiri ba a Arewa

Zanga-zangar ta gudana a wasu sassan Kudu duk da cewa ba wani tasiri ta yi ba, amma Arewa wasu ma ba su san ana yi ba.

A jihohin Arewa irin su Kaduna da Babban Birnin Tarayya Abuja da Kano da Katsina abin bai yi tasiri ba, domin ba kowa ne ma ya san labarin ba, sai dai wadansu da suke amfani da kafofin sada zumunta.

A ranar Litinin da aka yi tunanin tashi da zanga-zangar, mutanen Kaduna su kuma sun tashi ne da batun shari’ar Shugaban Kungiyar IMN ta ’yan Shi’a mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Neman sauyi ba ta’addanci ba ne – Kungiyar HRW

Da take bayanin game da kama Sowore, Kungiyar Human Rights Watch, ta yi Allah-wadai da kama jagorar zanga-zangar ta #RebolutionNow.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce “Idan har an tsare Omoyele Sowore ne da manufar taka wa zanga-zangar da ya shirya birki, hakan na nuna irin rashin hakurin gwamnati ga masu suka, a fili.”

Ta kara da cewa “Yin amfani da kalmar sauyi ta ‘rebolution’ a matsayin wani take ba zai sa gwamnati ta bayyana haka a matsayin ta’addanci ba sannan bai kamata a kalle shi a matsayin laifi ba,” kamar yadda BBC ya ruwaito.