Yadda aka damfari masu neman gidan haya Naira miliyan 60 a Legas

Akalla mutum 70 ne suka fada a tarkon wasu ‘yan damfara masu nema wa mabukata gidan haya a Jihar Legas. Bayanai sun ‘yan damfarar sun cika bujensu da iska bayan tattara kudaden da suka karba a hannun jama’a kimanin naira miliyan 60. Mun lalata gonakin Tabar Wiwi 48 a Edo – NDLEA ‘Yan bindiga sun […]

Yadda aka damfari masu neman gidan haya Naira miliyan 60 a Legas

Akalla mutum 70 ne suka fada a tarkon wasu ‘yan damfara masu nema wa mabukata gidan haya a Jihar Legas.

Bayanai sun ‘yan damfarar sun cika bujensu da iska bayan tattara kudaden da suka karba a hannun jama’a kimanin naira miliyan 60.

Oluwasegun Adewara da wani mai suna Okeowo, sun karbi kudaden jama’a ne don kama musu daki a wani ginin bene mai hawa daya da ba a kammala gina shi ba a yankin Lawason a jihar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, sai da aka kai kowannensu daga cikin masu bukatar gidan wajen ginin suka gani da idanunsu kafin suka biya kudi.

An ce bayan da suka gama tattara kudin jama’a sarai, sai suka mika wa kowa risit masu dauke da kwanan wata mabambanta a matsayin ranar da kowannensu zai je ya karbi makulli ya soma amfani da dakinsa.

Daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa, Jacob Dunya ya ce, “…sama da mutum 120 ne suka biya kudin kama daki ga ‘yan damfarar a gidan da ke da sassa 14 kawai.

“Kudin da mutane suka biya ya kai kimanin naira miliyan 60, saboda wasunsu kudin shekara biyar suka biya kai tsaye.

“Ni kaina kudin shekara daya na biya, N600,000 ta cikin asusun banki na Oluwasegun Olanrewaju Adewara a ranar 26 ga Afriku, 26, 2022,” inji shi.

Bayanai daga yankin sun nuna cewa, wasu da abin ya rutsa da su sun sharbi kuka har da hawaye, wasunsu kuma lamarin ya kai su ga sumewa saboda takaicin asarar da suka tafka.

Kwamishinan Yada Labarai da Tsare-tsare na Jihar Legas, Gbenga Omotoso, ya ce laifi ne babba ka karbi kudin haya a hannun wani ba tare da mika masa wurin zaman ba kamar yadda yake kunshe cikin tsarin dokokin jihar.

Kwamishinan ya nuna kuskuren da jama’a kan yi wajen neman gidan haya, ta yadda ba sa zurfafa bincike kafin mika kudadensu ga wadanda suke neman muhalli a hannunsu.

Ya ce a halin da ake ciki, hukumarsu na ci gaba da farautar ire-iren wadannan batagarin, tare da cewa kawo yanzu sun samu nasarar kama wasunsu sun kuma kwatar wa jama’a da dama kudadensu.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara