Yadda aka farfado da kungiyar Bunkasa Adabin Gargajiya ta Najeriya (NFS)

kungiyar nan da ta dade tana aiki wurjanjan wajen bukasa Adabain Gargajiya a Najeriya, wato ‘Nigerian Folklore Society (NFS)’ ta farfado, bayan da ta dauki tsawon lokaci ba a ji duriyarta ba.kungiyar ta farfado ne a sakamakon kafa wani kwamiti mai karfi, bisa shugabancin kwararren marubucin litattafan tatsuniyoyi, Dokta Bukar Usman; wanda ya dauki aniyar […]

Yadda aka farfado da kungiyar Bunkasa Adabin Gargajiya ta Najeriya (NFS)

kungiyar nan da ta dade tana aiki wurjanjan wajen bukasa Adabain Gargajiya a Najeriya, wato ‘Nigerian Folklore Society (NFS)’ ta farfado, bayan da ta dauki tsawon lokaci ba a ji duriyarta ba.
kungiyar ta farfado ne a sakamakon kafa wani kwamiti mai karfi, bisa shugabancin kwararren marubucin litattafan tatsuniyoyi, Dokta Bukar Usman; wanda ya dauki aniyar dawo da ayyukan kungiyar kamar yadda suke a shekarun baya.
A wata takarda, wacce ke dauke da sa hannun shugaban kwamitin farfado da kungiyar, shugaban ya ce ana gayyatar duk wani masani ko marubuci ko mai fasaha ko mai kishi da sha’awar Adabin Gargajiya, da ya shigo kungiyar ko kuma idan dama shi dan kungiyar ne a can baya; to ya zo ya sake jaddada rijistarsa.
“A madadin kwamitin farfado da kungiyar Bunkasa Adabin Gargajiya Ta Najeriya, ina farin cikin gayyatar daukacin al’umma da su shigo cikin wannan kungiya. Wadanda kuma suka kasance ’ya’yanta a can baya, to su zo su jaddada rijistarsu.” Inji Dokta Bukar Usman.
Ita dai kungiyar Bunkasa Adabin Gargajiya Ta Najeriya, an kafa ta ne a 1980, a yayin gudanar da taron kara wa juna sani ma taken: ‘Traditional Oral Poetry in Some Nigerian Communities, a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya a ranakun 16 zuwa 18 ga watan Janairu na shekarar. Kadan daga cikin ayyukanta sun hada da: Adanawa da bunkasa dukkan wasu kayayyaki ko aikin fasaha ko tatsuniyoyi da al’amara da sauran dukkan abin da ya shafi Adabin Gargajiya. kungiyar tana yin haka ne ta hanyar gudanar da bincike ko kuma daukar nauyin binciken da wallafa mujallu da kasidu da suka shafi Adabin Gargajiya, sannan kuma da gudanar da tarukan kara wa juna sani da nufin tattauna al’amuran da suka shafi adabin na gargajiya.
A can baya, kungiyar ta gudanar da tarukan bunkasa ilimi da musayar bayanai da suka shafi Adabin Gargajiya. Irin wadannan taruka sun hada da taron da kungiyar ta gudanar a Ibadan, a ranar 6 zuwa 9 ga watan Maris na shekarar 1989 mai taken: ‘Critical Currents and African Literature.’ Akwai kuma taron da kungiyar ta gudanar, mai taken:  ‘Issues in Northern Nigerian Literature’ ranar 11 zuwa 13 ga watan Satumba na shekarar 1989, a Jami’ar Bayero, Kano. Haka kuma an gudanar da wani taron a garin Kalaba, mai taken: “Nigeria Literature in Performance,’ a ranar 1 zwa 4 ga watan Nuwamba na shekarar 1989.
A yayin wadannan taruka, an tattauna al’amura masu dama da suka shafi Adabin Gargajiya, kamar kuma yadda aka kara wa juna ilimi ta wannan fuskar.
Tun daga lokacin da aka kafa kungiyar a 1980 ta fara gudanar da taronta shekara-shekara, inda taro na farko mai taken: ‘The Scope of Folklore Studies’ ya gudana a ranar 27 zuwa 30 ga watan Satumba na shekarar 1981. An gudanar da shi a Bagauda Lake Hotel, Kano. Sashen Al’adu na Gwamnatin Tarayya da kuma Hukumar Raya Al’adu ta Jihar Kano suka hada hannu suka dauki nauyin taron.
Taron kungiyar na biyu kuwa, mai taken: ‘Prose Narratibes in the Oral Traditions of Nigerian Communities,’ an gudanar da shi ne a ranakun 24 zuwa 27 ga watan Agusta na shekarar 1982, a Jami’ar Ilorin. Sashen Al’adu na Gwamnatin Tarayya da Hukumar Raya Al’adu ta Jihar Kwara suka dauki nauyin taron.
A karo na uku kuwa, kungiyar ta gudanar da taron nata na shekara-shekara a Jami’ar Sakkwato, a ranakun 6 zuwa 9 ga Disamba na shekarar 1983. Taken taron ya kasance: ‘Folklore and Ethical Orientation in Nigeria’ kuma Jami’ar ta Sakkwato ce tare da hadin gwiwar Sashen Al’adu na Gwamnatin Tarayya suka dauki nauyin gudanar da shi.
Taro na hudu ya gudana a 1984 a Jami’ar Ife da ke garin Ile-Ife, kamar kuma yadda na biyar ya gudana a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, a shekarar 1985. Taro na shida kuwa, an gudanar da shi ne a Kwalejin Ilimi ta Sakkwato, a shekarar 1987; a yayin da kuma taro na bakwai ya gudana a ranakun 5 zuwa 9 ga watan Disamba na shekarar 1988, a Jami’ar Legas. Taken taron shi ne: ‘Folklore, the Mass Media and Social Mobilisation in Nigeria’ kuma Sashin Al’adu na Gwamnatin Tarayya da Hukumar Raya Al’adu ta Jihar Legas ne suka dauki nauyin gudanar da shi.
kungiyar ta rika samun tallafi daga Ma’aikatar Fasaha da Al’adun Gargajiya ta Gwamnatin Tarayya. Haka kuma, an yi mata rijista da kungiyar Bunkasa Ilimi, Kimiyya da Al’adun Gargajiya Ta Majalisar dinkin Duniya (UNESCO) da ke da mazauni a birnin Paris na kasar Faransa. Haka kuma tana da kawaye da dama a kasashen duniya daban-daban.
kungiyar ta shiga cikin mawuyacin hali, a sakamakon mutuwar shugabanta, Dokta Shola Williams, a shekarar 1996. Ya amshi ragamar mulkin kungiyar ne daga tsohon shugabanta, Farfesa G. G. Darah.
A cikin watan Afrilu na bana ne Shugaban Jami’ar Bayero Kano, Farfesa Abubakar Rasheed ya shirya taron masana na duniya don bunkasa Adabin Gargajiya da nufin karrama Farfesa dandatti Abdulkadir, wanda kuma shi ma tsohon shugaban kungiyar ne. A yayin gudanar da taron ne, wanda ya samu halartar masana da dama, aka zartar da hukuncin sake farfado da kungiyar.
Nan take aka kafa kakkarfan kwamitin da zai yi aikin farfado da kungiyar, bisa shugabancin Dokta Bukar Usman. Sauran ’yan kwamitin sun hada da Farfesa dandatti Abdulkadir da Farfesa G.G. Darah da Farfesa Segun Adekoya da Farfesa Bade Ajuwon da Farfesa Abdu Yahaya Bichi da Farfesa Maikudi karaye da Farfesa Sani Abba Aliyu (Sakatare). Sauran sun hada da Farfesa (Uwargida) Asabe Kabir da kuma Dokta A.K. Babajo.
Ga mai bukatar shiga cikin kungiyar nan kuwa, shugaban kwamitin farfadowarta, Dokta Bukar Usman ya ce: “Ga duk mai bukatar shiga kungiyar Bunkasa Adabin Gargajiya Ta Najeriya (NFS) ko kuma yake son jaddada rijistarsa, sai ya aika da sakon bukatar hakan ta kiran waya ko kuma sakon tes ko na I-mel ta wadannan adiresoshin: Waya: 08034515110. I-Mel: [email protected]
“Kwamitin na zuba ido ga sababbin membobi, da fatan za su ci gaba da bibiyar ayyukan kungiyar har ma da amsa gayyatar zuwa tarukanta, musamman ma wanda za a gudanar a ranar 2 zuwa 4 ga Afrilu na 2014 da ikon Allah.” Inji Dokta Bukar Usman.