Yadda aka fidda jadawalin Gasar Zakarun Turai

RB Leipzing da ta kare a mataki na biyu a rukunin F za ta kara da Manchester City.

Yadda aka fidda jadawalin Gasar Zakarun Turai

Real Madrid, Zakarun Turai na 2021/2022.

A ranar Litinin ce dai aka hada yadda wasan zagaye na biyu na Gasar Zakarun Turai zai kasance, inda aka fidda jadawalin wasannin da za a fafata a zagayen kungiyoyi 16 na gasar.

A hadin da aka yi, kungiyoyin da suka buga wasan karshe a gasar a shekarar da ta gabata Real Madrid da Liverpool za su hadu a wasan zagaye na biyu a bana.

RB Leipzing da ta kare a mataki na biyu a rukunin F za ta kara da Manchester City da ta jagoranci rukunin G, Club Brugge zata kara ne da Benfica, AC Milan ta karbi bakuncin Tottenham.

Sauran wasannin sun hada da Eintracht Frankfurt ta hadu da Napoli, Borussia Dortmund da Chelsea, Inter da Porto, sai kuma wasa tsakanin PSG da Bayern Munich wanda ke cikin manyan wasannin da za’a buga a wannan zagayen.

A ranakun 14 da 15 da kuma 21 da 22 na watan Fabuwairun shekara mai zuwa ne za’a fara fafatawa a wasan farko na zagayen na biyu a gasar zakarun nahiyar Turai.

A bangaren gasar Europa kuwa, Barcelona da ta kare a mataki na uku a rukunin gasar Zakarun Turai, za ta kara ne da Manchester United, Juventus za ta kara da Nantes sai Sporting Lisbon da Midtjylland.

Sauran wasannin gasar ta Europa sun hada da Shakhtar Donetsk da Rennes, Ajax da Union Berlin, Bayer Leverkusen da Monaco, Sevilla da PSV Eindhoven sai FC Salzburg da Roma.

A ranar 16 ga watan Fabuwairu ne za’a buga wasan farko na gasar ta Europa, sai kuma wasa na biyu a ranar 23 na Fabarairu.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno