Yadda aka gano gidan da ake boye yaran da aka sace a Gwagwalada

Sakamakon kama wadansu mutum biyu da ’yan sintiri da ake kira Bijilanti suka yi suka mika ga ’yan sanda a garin Kafanchan bisa zarginsu da kama kananan yara suna sayarwa, ’yan sanda sun yi nasarar gano wani gida da ake tara kananan yara bayan an sato su daga wurare daban-daban a garin Gwagwalada da ke […]

Yadda aka gano gidan da ake boye yaran da aka sace a Gwagwalada

Sakamakon kama wadansu mutum biyu da ’yan sintiri da ake kira Bijilanti suka yi suka mika ga ’yan sanda a garin Kafanchan bisa zarginsu da kama kananan yara suna sayarwa, ’yan sanda sun yi nasarar gano wani gida da ake tara kananan yara bayan an sato su daga wurare daban-daban a garin Gwagwalada da ke yankin Birnin Tarayya, Abuja.

Asirin wadanda ake zargin ya tonu ne bayan sace wadansu yara biyu da ake zargin sun yi a garin Kafanchan a karshen watan jiya da kuma farkon wannan wata. Ana zarginsu ne da sace wani yaro mai suna Goodluck, mai kimanin shekara 6 a bayan Loko da kuma Sebastine Dabid mai kimanin shekara uku da watanni a Unguwar Musa duk da ke garin Kafanchan.

Yayin da yake bayyana wa Aminiya yadda aka yi, wani jami’in tsaro da ya bukaci a sakaye sunansa saboda ba ya da iznin yin magana da ’yan jarida, kuma ’yan sanda sun hana ’yan jarida daukar hoto ko bayar da wani karin bayani zuwa lokacin hada wannan rahoto, ya ce gano gidan da ake tara kananan yaran da aka sace a Abuja, ya biyo bayan kama daya daga cikin masu satar yaran ne suna kai wa dillaliyarsu wacce ke zaune a garin Gwagwalada.

Bayan samun cikakken bayanin inda suke kai yaran da suka sacen, wadanda ake zargi da satar yaran, wato Amos Williams da Caleb, sun ce wata mata ta sayi yaran biyu da suka sace a kan Naira dubu 250.

Daga nan ne DPO din ’yan sanda na Kafanchan Baba Ali ya tura jami’ansa tare da daya daga cikin kamammun inda bayan zuwa gidan suka tarar da wadansu kananan yara da aka raba su da iyayensu kimanin 26 da ma’aikatan gidan da suka hada da maigadi da masu dafa abinci da masu lura da yaran da aka sato inda aka taso keyarsu gaba daya zuwa Kafanchan.

Kafin isowarsu, Hedkwatar ’Yan sandan Shiyya ta Kafanchan ta cika makil da mutane kowa na dubawa ko zai ga wani nasa ko wanda ya sani, sai dai yara biyu ne kawai ’yan garin Kafanchan a cikin yaran da aka zo da su, inda da damansu ba su san garuruwan da suka fito ba.

“Mun yi nasarar kama daya daga cikin wadanda ake zargin ne mai suna Amos Williams amma yayin da abokin ta’asarsa mai suna Caleb ya samu labarin kama shi, sai ya yi maza ya sanar da shugabar tasu da ke Gwagwalada a Abuja, inda ta sulale ta gudu, shi kuma daga baya aka kama shi yana kokarin guduwa,” inji majiyar.

Dabid Simon, shi ne mahaifin Sebastine da aka sace, ya bayyana wa Aminiya cewa wanda ya sace masa dansa a gidansu ma yake zaune kuma ya saba wasa da yaron har yaron na kiransa Baffa. “A ranar da zai sace shi ya fito sun yi wasa da shi, amma zuwa can sai ba mu ga yaro ba, ashe ya dauke shi ya tafi da shi. Washegari sai ga shi ya dawo alhali babu wanda ya san ya yi tafiya ma. Yana ji muna cigiya har muna ce masa ka ga abokin wasanka, har yanzu ba mu gan shi ba, ashe har ya je ya sayar da shi kan Naira dubu 50, kamar yadda ya fada mana,” inji mahaifin yaron.

Wannan lamari ya zamo bako anu a Kudancin Jihar Kaduna inda aka nemi jama’a su rika kiyayewa tare da lura da ’ya’yansu da kuma wadanda suke hulda da su.