Yadda aka gano gidan hada magungunan jabu a Legas
Rundunar ’yan sanda a karkashin kwamitinta na musanmman da ke bin diddigin miyagun laifuffuka ta hanyar amfani da hanyoyin kimiyyar sadarwar zamani (IRT) a karkashin jagorancin Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda, Abba Kyari ta bankado wani gida da ake buga jabun magunguna a Jihar Legas. Rundunar ta kuma kama mutum hudu da ake zargi sun kware […]
Rundunar ’yan sanda a karkashin kwamitinta na musanmman da ke bin diddigin miyagun laifuffuka ta hanyar amfani da hanyoyin kimiyyar sadarwar zamani (IRT) a karkashin jagorancin Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda, Abba Kyari ta bankado wani gida da ake buga jabun magunguna a Jihar Legas. Rundunar ta kuma kama mutum hudu da ake zargi sun kware wajen hada jabun magungunan tare da tarin na’urori da injuna da suke aiki da su.
Wata sanarwa da Kakakin Rundunar ’Yan sandan Najeriya, Mataimakin Kwamsihinan ’Yan sanda Jimoh Mashood ya fitar ta ce rundunar ta bankado gidan hada jabun magungunan ne a gida Mai lamba 2 da ke Unguwar Okunnenye a yankin Ikotun Egbe a Legas. Ya ce an kama wadanda ake zargi da hada jabun magungunan da suka hada da Emeka Madu mai shekara 47 wanda ya mallaki gidan, sai Eze Young mai shekara 26 da Chijoke Umunna mai shekara 19 sai Kingsley Obilo mai shekara 22.
Ya ce rundunar ta kama wadanda ake zargi da tarin jabun magunguna da suke hadawa tare da kayayyakin hada magungunan wadanda suka hada da garin alabo da sinadarin sauya launi da manyan injinan hada magunguna da motar da suke amfani da ita wajen rarraba magungunan zuwa sassa daban-daban. “Allah kadai Ya san adaddin mutanen da suka nakasa ko suka rasa rayukansu sakamakon wannan ta’asa, ana kuma ci gaba da zurfafa bincike kan lamarin kafin daga bisani a gabatar da su a kotu domin su fuskanci shari’a,” inji shi.
A Jihar Legas dai ana samun wuraren da ake hada-hadar jabun magungunan ba bisa ka’ida ba, wuraren da suka hada da kasuwani da cikin unguwanin da jama’a ke zaune.