Yadda aka gano kogwanni da ’yan kwaya ke sheke ayarsu a Kano
Hukumar NDLEA ta ce ta rushe mafakar dillalan kwayar wadanda suka mayar tamkar gida—da dakuna da tabarmi da kwanukan abinci, abun da ke nuni da cewar sun dade suna wannan aika-aika a wurin
An bankado wasu koguna da dillalan miyagun kwayoyi suka haka kuma suka mayar da su maboyarsu, inda a cikinsu suke hadahadar kayan maye iri-iri tare da holewa a Jihar Kano.
Hukumar Yaki da Miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta gano kogunan dillalan kwayar ne a yayin wani samame a unguwar Bulbula da ke yankin Rimin Kebe a karamar Hukumar Ungogo.
A yayin samamen, wadan Hukumar ta kira da ‘Operation Sharar Mafaka’, jami’an Hukumar NDLEA karkashin jagoracin kwamandansu, dahiru Yahya Lawal, sun tarwartsa kogunan da bta-garin suka mayar matattararsu ta sha da kuma hadahadar kwayoyi.
Aminiya ta gano cewa dillalai da masu shaye-shaye sun mayar da kogunan tamkar gidajensu. Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa bata-gari sun fi shekara 20 suna sheke ayarsu a yankin na Bulbula.
Hukumar NDLEA ta ce ta rushe mafakar dillalan kwayar wadanda suka mayar tamkar gida—da dakuna da tabarmi da kwanukan abinci, abun da ke nuni da cewar sun dade suna wannan aika-aika a wurin.

Duk da cewar lokacin da aka kai samamen yawanci diloli da masu shan kwayayoyin sun tsere, jami’an hukumar sun yi nasarar kwashe tulin da tabar wiwi da sauran miyagun kayan maye a sansanin, tare da kuma rushe kogon dutsen da ya zama maboyarsu.
NDLEA ta bayyana cewa ta kai farmakin ne bayan ta samu rahotannin sirri daga jama’a kan abin da ke faruwa a wurin.
Hukumar ta bakin kakakinta, Sadik Muhammad Maigatari, ta bayyana cewa tana shiri na sake rushe sauran koguna da mafakar dillalan kwaya a yankin, domin dakile fataucin miyagun kwayoyi da tabar wiwi a yankin Rimin Kebe da sauran sassan Jihar Kano.
“Za mu ci gaba da farautar wadannan bata-garin a duk inda suke. Wadanda suka shiga cikin wannan mummunar sana’ar su tuba su daina domin jami’anmu ba za su daina kai samame ba, har sai mun ga an daina cinikin miyagun kwayoyi a Jihar Kano.
“Shugaban Hukumar NDLEA na kasa, Janar Muhammad Buba Marwa ya ba mu umarnin cewar mu kakkabe dillalan kwaya a kowane lungu da sako na kasar nan,” in ji Maigatari.
Ya yi kira ga jama’a su kai rahoton maboyar dillalan kwaya ga Hukumar ba tare da bata lokacin ba, inda ya ce bayyana cewa samun bayanai daga jama’a shi ne kashin bayan yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Maigatari ya sha alwashin cewar NDLEA za ta ci gaba da kai samamen, duk inda mafakar dillalan kwaya take a jihar don ganin an kawo karshen matsalar sha da fataucin miyagun kwayoyi.

Sama da shekara 20 ana harkar miyagun kwayoyi a wurin
Masana sun ce sama da mutum miliyan daya ne ke ta’ammali da kwayayoyi a Jihar Kano inda kashi 16 zuwa 80 cikin 100 na adadin matasa ne.
Sun bayyana cewa ta’ammali da miyagun kwayoyi ke kara ingiza aikata laifi da tabarbarewar tarbiyya a tsakanin matasa daga kimanin shekaru 15 zuwa 50.
Sai dai kuma makonni biyu bayan farmakin da NDLEA ta kai yankin Rimin Kebe, mazauna yankin sun bayyana cewa har yanzu dillalan kwaya suna amfani da wurin kuma ya zama wajibi a dauki tsauraran matakai domin kawo karshen matsalar baki daya.
Ibrahim Aminu, wani mazaunin yankin Rimin Kebe, ya ce an dade ana dillacin kwaya a wurin kuma sakacin da aka yi ne ya sa wurin ya zama babbar mafakar dillalan kwaya da masu shaye-shaye.
“Sama da shekaru 20 ana harka kwaya a wurin. Gaskiyar magana an yi sakaci. Har yanzu bayan farmakin da NDLEA ta Kawo, masu sha da fataucin miyagun kwayoyi suna harkokinsu a wurin. Kai babu irin badalar da ba a yi a wurin da mata da matasa—sun mayar da tabar wiwi ba komai ba.
“Abinda muke fata shi ne jami’an tsaro su hada kai da dukkan masu ruwa da tsaki, a ci-gaba da kai samame a wurin, domin sama wa al’umma lafiya,” in ji Shi.
Ya ce saboda lalacewar tarbiyya a yankin, wasu magidanta sun tashi sun koma wasu unguwanni, ganin yadda cinikin kwaya ko tabar wiwi ya zama ruwan dare a yankin.
Shi ma wani mazaunin yankin, Abubakar Latu, ya ce harkan hadahadar tabar wiwi da kwaya sun ci gaba bayan harin na NDLEA, yana mai cewar dillalan kwaya ba za su daina ba muddin ba a kama su an yi musu tsattsauran hukuncin ba.
“Ko yanzu ka je wajen a Bulbula suna ci gaba da harkarsu. Harka ta riga ta zama wata annobar da tilas sai an hada da addu’a.
“Bulbulan unguwa ce a karkashin Rimin Kebe Amma kuma tana cikin karamar Hukumar Ungogo. Amma inda ake sayar da kayan maye ana kiran sa da risach (Research), akwai magudanar ruwa da ake ginawa saboda hanyar Bulbula-Gayawa-Ungogo. Abin takaici shi ne suna nan suna harkarsu kamar ba a kai musu farmakin kwanan nan ba,” in ji shi ba.
Ya ce akwai bukatar hadin gwiwa tsakanin kananan hukumomin Ungogo da Nassarawa wadanda suka yi iyaka a wajajen domin tunkarar matsalar.
Sai Dai Dagacin Zango, Alhaji Hamza Jibril, wanda yankin ke karkashin kulawarsa, da yake zantawa da wakilinmu ta wayar tarho, ya ce zai bincika ya ji abin da yake faruwa a wajen, bayan kai wa dillalan kwatar samamen NDLEA sannan daga baya zai tuntubi wakilinmu.

Mai Unguwar Rimin Kebe, Malam Iliyasu Adamu, ya ce yankin da abin ke faruwa ba ya karkashin jagoracinsa. Ya ci gaba da cewa, Mai Unguwar Bulbula ke da hakki da wurin, amma Suna da labarin farmakin da NDLEA ta Kai yankin domin dakile fataucin miyagun kwayoyi.
kokarin wakilinmu na jin ta bakin Mai Unguwar Bulbula ko wakilinsa bai yi nasara ba.
Illar shaye-shaye
Wani matashi mai rajin yaki da shan kwaya da dangoginsu a tsakanin matasa kuma Shugaban kungiyar Wayar da Kai ta (KASYADAREC) Usman Musa danmari, ya ce sakacin al’ummar yankin ya taimaka wurin habakar matsalar, inda ya bukaci su ci gaba da kai rahoton maboyar dillalan kwaya ga Hukumar ta NDLEA domin daukar matakan da suka dace.
“Gaskiya akwai sakacin al’ummar da suke zaune a yankin. Ya dace kodayaushe su sanar da Hukumar kafin abin ya kai ga haka. Ya kuma dace su dauki mataki sosai a yankin domin tallafa wa hukomomi. To Amma Alhamdulillahi dai, tunda an fara kai sumame a wajen, watakila za a samu sauki man gaba,” a cewa danmari.
Ya Kara da cewa matsalar yawan fadace-fadacen daba da jagaliyar siyasa a tsakanin matasa Yana da alaka da yawan fataucin miyagun kwayoyi da tabar wiwi a Kano Inda yai nuni da cewa dalilin haka ne ma gwamnati ta mayar da Kasuwar magani zuwa Dan Gwauro.
Me ke sa ’yan mata shaye-shaye?
Mataimakiyar Kwamanda Mai Kula da Sashe na Musamman na Drug Demand Reduction (DDRU) na NDLEA, Maimuna Garba Muhammad, ta ce sun lura cewar abun da ke sa mata shiga shaye-shaye shi ne rashin kula da tarbiyya tun daga gida da talauci da matsalolin aure da tasirin kawaye da abokai da kuma son rayuwar nishadi da holewa.
Ta ce abin da suke yi a wannan bangaren mata shi ne, shiryar da matasa musamman mata da kokarin dawo da su kan turba.
“Mun sha kama yara mata kananan ’yan shekaru 17, 18, 19, 20 zuwa 25 a otel-otel suna harkarsu ta sha kayan maye. Idan muka tambaye su me ya sa suke shan kayan maye, sai su ce mutuwar aure ko damuwa ko rashi abin da za su rike kansu da sauransu ko Kuma suna ganin wasu suna watayawa da rayuwarsu.
“A takaice da ba karamar illa kayan maye ke yi wa jama’a ba. Sobada haka dole sai mun tashi tsaye mun yaki harkar,” a cewarta.
Jihar Kano ce ta biyu wajen masu ta’ammali da kayan maye bayan Jihar Legas, wadda take kan gaba kamar yadda NDLEA ta tabbatar.
Ita ma Rundunar ’Yan Sanda a wani rahotonta, ta ce kayan maye irin su hodar Iblis da kwayar taramadol da tabar wiwi su Ke kara taimaka wa tsageru da ’yan jagaliyar siyasa da sauran masu aikata laifi, inda ta ce akwai alaka tsakanin aikata laifi da kuma shan kwaya ko kayan maye.