‘Yadda aka gano ni bayan shekara 17 da sace ni’

Amina Idirisa an sace ta ne tun tana ’yar shekara biyar da haihuwa a garin Gombi da ke Jihar Adamawa, amma ba a tashi gano ta ba sai da ta kai shekara 22, wato bayan shekara 17 a wani kauye mai suna Maihula da ke Jihar Taraba. A yanzu dai Amina tana da ’ya’ya biyu […]

‘Yadda aka gano ni bayan shekara 17 da sace ni’

Amina IdirisaAmina Idirisa an sace ta ne tun tana ’yar shekara biyar da haihuwa a garin Gombi da ke Jihar Adamawa, amma ba a tashi gano ta ba sai da ta kai shekara 22, wato bayan shekara 17 a wani kauye mai suna Maihula da ke Jihar Taraba. A yanzu dai Amina tana da ’ya’ya biyu a aure biyu da ta yi. A zantawarta da Aminiya a Kaduna inda ta kai ziyara gidan kawunta ta ce matar da ta sace ta tuni ta rasu:

Aminiya: Me ya faru lokacin da kika bar gida shekaru masu yawa kina karama?
Abin da zan iya tunawa sace ni aka yi, a lokacin kuma da aka sace ni sai aka kai ni wurin wata mace inda na girma. Kuma ita ce take fada min cewa sato ni aka yi.
Aminiya: Tun kina ’yar shekara nawa aka sace ki?
Shekara biyar ko bakwai da haihuwa
Aminiya: Yanzu shekarunki nawa?
Shekaruna yanzu 22 da dauke ni shekara 17 ke nan yanzu.
Aminiya: Da aka dauke ki ina aka kai ki?
Can wani gari wai shi Maihula, kusa ne da Jalingo a Jihar Taraba wurin Bale. Kuma an sace ni ne a garin Gombi a Jihar Adamawa.
Aminiya: Ko za ki iya ba mu dan bayanin yadda aka yi aka sace ki?
Eh, ita matar ce ta ba ni labarin yadda aka yi, inda ta ce da ni a lokacin wai ina tallar mangoro ne sai ta turo wasu ’yan gidanta su kuma suka yi amfani da wanda ya san ni ya zo ya daukar min mangoro sai ni kuma wai ina bin sa a kan ya ba ni mangorona amma sai ya ki. Bayan mun shiga wani lungu sai mutanen nata suka dauke ni zuwa wurinta.
Aminiya: Aikin me kike yi mata da aka kai ki wurinta?
Ba na aikin komai. Ta ce da ni kawai ta sa an dauko ni ne domin in zauna da ita kawai a matsayin ’yarta ba wai don wani abu ba.
Aminiya:  Yaya sunan matar?
Ita ma sunanta Amina. Kuma sana’arta shi ne ba da magungunan gargajiya na bokanci.  Mutane layi suke yi mata suna karbar magani.
Aminiya: Yaya zamanku da ita a can garin?
Muna zaune ne kawai, inda take kulawa da ni. Ta dauke ni ’yarta ne kawai. Tana kuma yi min komai da nake so.
Aminiya: Ta sanya ki a makaranta?
Eh, ta sanya ni a makarantar boko amma na wata biyu kawai, bayan wata biyu sai ta ce ba zan sake zuwa ba. Haka ma makarantar Islamiyya shi ma na wata biyu na yi. Muna zaune ne kawai a wurinta, ba kuma abin da muke yi.
Aminiya: Ku nawa ne a wurinta?
Mu hudu ne a wurinta, kuma duk dauko mu aka yi. Amma a yanzu sauran yaran suna can garin.
Aminiya: Ta aurar da ke a can garin ne?  
Eh, na yi aure har sau biyu, na yi na farko na fito na sake wani aure. Ita ce ta aurar da ni. Auren farko ina da ’ya’ya biyu da mijina amma daya ta rasu. Sannan a aure na biyu ’ya mace na haifa.
Aminiya: Ina mijinki yake?
Yana Maihula, na baro shi can. Kuma ba na tsammanin zan sake komawa garin, tunda shi ma mun rabu da shi.
Aminiya: Ina ita matar da ta sa aka sato ki?
Ta rasu.  
Aminiya: Ita matar ba ta da ’yan uwa ne?
Tunda muke da ita a tsawon wadannan shekaru ban taba ganin ’yan uwanta ba, har ta rasu.
Aminiya: Bayan kin dawo gida ko kin samu mahaifanki?
Bayan na dawo gida ban samu mahaifiyata ba, domin ta rasu sai dai mahaifina na iske.
Aminiya: A lokacin da kike wurinta ko kin taba damunta cewa kina son zuwa gida?
A duk lokacin da na kawo mata wannan zance, sai ta dibo ruwa a kwarya, ta ce ga mamata nan idan ina son ganinta.
Aminiya: Kin taba leka kwaryar?
A’a, gaskiya ban taba lekawa ba, saboda ina tsoro.
Aminiya:  Me ke ba ki tsoro, kodai ba ki son ganin mahaifiyar taki ce?
A’a ina son ganinta, ni dai kawai tsoro nake ji, shi ya sa ba na iya leka kwaryar ruwan.
Aminiya: Sauran yaran da ke a gidan matar fa?
Akwai namiji da mata biyu, kuma babu mai kulawa da su. Domin shi namijin ma a yanzu ya lalace saboda shaye-shaye da sata da yake yi a yanzu. Yakan je ya sato abinci idan an kama shi sai a yi masa duka sannan idan aka tambaye shi dalilin yin satar sai ya ce shi yunwa yake ji shi ya sa yake sata.
Aminiya: Yaya aka yi ’yan uwanki suka gan ki har kika dawo gida bayan wannan yawan shekaru?
Na je bikin auren wata ’yar kishiyata ce a Jalingo, sai na yi wata kawa a garin wacce na kwashe wata uku a wurinta. Kafin wani mutum ya bukaci in zauna a gidansa a matsayin ubana tun da ba ni da inda za ni. Ina gidansa, sai yaransa suka rika damuna, daga nan sai na sake komawa Maihula, gidan surukata na zauna. Ita kuma kawar tawa wace na zauna a wurinta a Jalingo sai ta je Gombi gidan kawuna, da aka ba ta hotuna tana dubawa sai ta ga hoton yayata wacce muka yi kama da ita sosai. Sai ta fada musu cewa akwai wata kawarta da suka yi kama da wadda ke cikin hoon a can Maihula, wannan ya sa aka ci gaba da bincike sai suka tafi inda nake aka gano ni.
Aminiya: Yaya kika ji da kika dawo gida cikin ’yan uwanki?
Gaskiya na ji dadin dawowa gida domin na ga yayyena da kanena daya. Kafin a sace ni ina da yayye hudu, kuma da na dawo bayan wadannan shekaru sai na tarar da kane daya a bayana. Na gode wa Allah da Ya sa na dawo wurin ’yan uwana.

…..Mun yi murna da aka gano Amina – Kakarta

Hajiya Fatima ita ce kakar Amina da aka sace shekaru masu yawa. Ta tabbatar wa Aminiya cewa Amina ’yarsu ce da ta bace.

Daga Mohammad Yaba, Kaduna

Aminiya: Ko za ki waiwaya baya ki fada mana abin da ya faru da wannan jika taki Amina, shekaru 17 da suka wuce?
Ina gida nan ne abin ya faru, bayan kwanakin da Allah Ya dibar mata sai aka bugo mana waya aka ce an gano ta a Maihula can wajen Jalingo a Jihar Taraba. Muka tambayi yadda aka ce an gan ta. Sai aka fada min cewa wata kawarta ce ta je Gombi ta hadu da ’yar uwarta da ke aure a can sai ta ga kamanni sosai. Sai ta fada musu cewa ai kuwa akwai wata kawarta a Maihula wacce ta yi kama da ’yar uwar sosai.
Amma sai suka fada mata cewa su ba su da wata ’yar uwa a Maihula. Nan dai aka ci gaba da hira ba tare da sun mayar da hankali a kan zancen ba. Sai daga baya da maigidansu ya dawo sai suka fada masa zancen, shi kuma sai ya ce sun sani ko Amina ce da ta bace shekaru da yawa.  Daga nan sai aka shirya kan a samu wacce za ta je can domin ta je ta ganta. Ga shi kuma mahaifiyarsu ta rasu sai mahaifinsu ke da rai. Daga nan dangi kowa na cewa zai je garin sai dai aka shirya ita babbarsu ta dakin ta tafi garin da hoto a hannunta. Bayan ta isa gidan da aka ce ita Amina na aure sai mijinta ya hana a shigar masa gida.
Sai aka fada masa cewa wurin matarsa aka zo, amma sai ya ce shi dai ba zai yarda a shigar masa gida ba.
Daga nan sai ta ce a kai ta gidan mai unguwa. Bayan ta yi wa mai unguwa bayani sai ya aika a kirawo mijin. Da ya zo sai aka fada masa cewa ’yar uwar matarsa ce ja zo ganinta. Sai ya ce sai dai ya dauko matar zuwa gidan mai unguwa amma dai ba zai bari su shigar masa gida ba.
Da aka dauko ta sai suka dubi hotonta tana karama sai aka ce ai ita ce. Sai aka tambaye shi abin yi sai ya ce babu inda za ta je. Sai Amina ta ce masa dama sun rabu da shi amma saboda ba ta da gidan da za ta koma ne ya sa take zaune wurin mahaifiyarsa. Amma yanzu tunda ta ga ’yar uwarta za ta bi ta. Duk da haka sai ya ki. To, mu ma muna da ’yan uwa a can Taraba sai aka fada musu abin da ke faruwa daga nan sai suka ba da mota guda na ’yan sanda aka je garin suka karbo ta. ’Yan sandan sun fada masa cewa tunda babu aure a kanta, ba ta da amfanin zama da shi. Da dai suna da aure ne sai a sasanta ta ci gaba da zama. Daga nan sai aka saka su a mota zuwa can gida Gombi zuwa wurin mahaifinta da sauran ’yan uwa.
Aminiya: Ku kun gamsu cewa ita ce ’yarku Amina da ta bace?
Tabbas ita ce, da farko dai mun cire tsammanin ganinta. Mun tabbatar ita ce domin duk inda aka je da hotonta ake yawo lokacin da ta bace. Kuma ko da za a je can garin da hotonta aka je.
Aminiya: Ko a ina aka sace ta?
A can Gombi kusa da Yola a Jihar Adamawa ta yanzu aka sace ta. Suna tare da yarta ce sai aka dauke ta. Tun daga lokacin kuma ba a sake jin labarinta ba sai ’yan kwanakin nan da aka gano ta a Taraba. Har yanzu mahaifinta na can Gombi, kwanan nan ta dawo Kaduna.
Aminiya: Baba yanzu yaya kike ji a ranki?
Ina matukar farin ciki domin koda na je can garin na ga an dauko ta, mun yi murna sosai. Duk wanda ya je ya ganta in dai ya santa a lokacin tana karama, sai ya ce ita ce. Ko ma a hoton ma ita ce a ciki.