Yadda aka gudanar da bikin Kabilar Duguza a Jos

Al’ummar kabilar Duguza daga kowane bangare na Najeriya, sun gudanar da babban taron tunawa da ranar kabilar a Jos babban birnin Jihar Filato. Da yake jawabi a wajen taron wani dan kabilar kuma dan Majalisar Dokoki ta Jihar Filato, mai wakiltar mazabar Pengana da ke Karamar Hukumar Bassa, Honorabul Ezekiel Bauda Afon ya ce a […]

Yadda aka gudanar da bikin Kabilar Duguza a Jos

Masu rawar gargajiya na ’yan qabilar Duguza a wajen taron

Al’ummar kabilar Duguza daga kowane bangare na Najeriya, sun gudanar da babban taron tunawa da ranar kabilar a Jos babban birnin Jihar Filato.

Da yake jawabi a wajen taron wani dan kabilar kuma dan Majalisar Dokoki ta Jihar Filato, mai wakiltar mazabar Pengana da ke Karamar Hukumar Bassa, Honorabul Ezekiel Bauda Afon ya ce a da mutane ba su san kabilar Duguza ba, amma yanzu sun kai wani mataki da aka san su a duniya.

Ya ce kabilar Duguzawa suna nan a ko’ina a kasar nan, don haka suna nan suna bincike domin gano duk inda suke a Najeriya. Mista Afon ya ce harshen Duguza yana da matukar muhimmanci, don haka ya yi kira ga kwamitin bunkasa harshen Duguza da aka kafa, ya yi kokari ya inganta aikinsa don ganin an bunkasa harshen.

Babban Bako Mai jawabi, Mista Najuba Ayuba ya yi kira ga iyayen kabilar su taimaka wa ’ya’yan kabilar ta hanyar daukarsu aiki a wurare daban-daban.

Ya yi kira ga al’ummar Jihar Filato da Najeriya su zauna lafiya, domin sai da zaman lafiya za a samu ci gaba. Daga nan ya roki  Allah Ya bai wa Najeriya shugabanni masu tausayi da za su kawo zaman lafiya da ci gaba a cikinta.

Aa jawabin, Sarkin Magama Gumau da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi, Malam Musa Sambo Duguza, ya bayyana cewa wannan babbar rana ce ga dukan ’ya’yan kabilar Duguza. Domin a duk shekara suna taruwa a irin wannan rana, don gudanar da irin wannan taro na  sada zumunci da tattauna abubuwan da za su kawo musu ci gaba. Ya yi kira ga dukan ’ya’yan kabilar su rumgumi neman iilmi da sana’o’i.

Tun farko a jawabin sabon Shugaban Kungiyar Kabilar Duguza ta Kasa, Barista Sale Magama ya yi ga kira ga al’ummar Duguzawa su ba su goyon baya da hadin kai, domin su kai ga nasara. Ya ce babban burinsu shi ne su hada kan al’ummar Duguzawa wuri guda domin su aiwatar da abubuwan da za su kawo wa kabilar ci gaba.

A karshe an rantsar da sababbin shugabannin kungiyar kabilar na kasa.

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta