Yadda aka gudanar da bikin karrama ’yan fim a Abuja

A ranar Asabar da ta gabata dakin Taro na NAF da ke titin Ahmadu Bello Way da ke Abuja ya yi cikar farin dango da masu ruwa da tsaki a harkar fim, inda suka halarci bikin karrama ’yan fim karo na biyu da kamfanin sadarwa na MTN ya dauki nauyin shiryawa. A yayin da yake […]

Yadda aka gudanar da bikin karrama ’yan fim a Abuja
Yadda aka gudanar da bikin karrama ’yan fim a Abuja

A ranar Asabar da ta gabata dakin Taro na NAF da ke titin Ahmadu Bello Way da ke Abuja ya yi cikar farin dango da masu ruwa da tsaki a harkar fim, inda suka halarci bikin karrama ’yan fim karo na biyu da kamfanin sadarwa na MTN ya dauki nauyin shiryawa.

A yayin da yake jawabi Abdulkareem Muhammad wanda shi ne shugaban kwamatin da suka tantance fina-finan da aka shigar gasar da su ya ce, sun tantance fina-finan 77 a cikin kwana 14 ne.
“Mun tantance fina-finai 77 a cikin kwana hudu, hakan ba karamin aiki ba ne. A bana kyaututtukan sun kasu kashi biyu ne, akwai na wadanda aka aika sako (popular award) da kuma wadanda kwamitinmu ya tantance.”
Ya bayyana wadansu kura-kurai da suka dabaibaye fina-finan Hausa da suka hada da kura-kurai a bangare fassara daga Hausa zuwa Turanci, amma ya yi farin ciki sakamakon ci gaban da aka samu a masana’antar cikin kankanen lokaci.
Marigayin Rabilu Musa Ibro shi ne jarumin da ya samu kyauta biyu, Gwarzon Jarumin Barkwanci da kuma Jarumin Barkwanci mafi fice. Inda Ali Nuhu ya zama Gwarzon Jarumi mafi fice, Nafisa Abdullahi Gwarzuwar Jaruma mafi fice, Yaseen Auwal Gwarzon Darakta Mafi fice.
Kyautar alkalai (Jurist Award)
Sadik Sani Sadak shi ne Gwarzon Jarumi da fim din (dinyar Makaho), Hadiza Gabon Gwarzuwar Jaruma, Aminu Saira Gwarzon Darakta (Ashabul Khafi), Gwarzon fim: Ashabul Khafi, Gwarzuwar Tsara Labari, Rahma Abdulmajid (Su Ma Mata Ne), Gwarzon mai tallafa wa Jarumi, Mustapha Naburaska (Basaja), Gwarzuwar mai tallafa wa Jaruma, Fati Washa (’Ya Daga Allah), Gwarzon Mawaki T.K Ahmad (Saki Kowa).
An karrama Sarkin Gumel, Dokta Ahmad Muhammad Sani da Mataimakin Shugaban kasa, Namadi Sambo da Gwamnan Jihar Nasarawa Tanko Almakura.
Naziru Ahmad da Adam A. Zango da Nazifi Asnanic da Ali Jita sun nishadantar da taron.

A-Kurkura: Guba ko Magani?

Tsohon Shugaban Jami’ar Ilori, Farfesa Ambali ya rasu

ICPC ta hana El-Rufai ganin likita —Hadiminsa

Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa