Yadda aka gudanar da Bikin Nuna Fina-finan Indiya a Abuja

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka kammala Bikin Nuna Fina-finan Indiya a gidan sinimar Silberbird da ke garin Abuja.Wannan shi ne biki na farko da aka gudanar a Najeriya, inda makasudinsa shirya shi don murnar cika shekarar 100 da masana’antar fina-finan Indiya ta yi da kafuwa ne.Bikin wanda ya samu halartar dimbin masoyan […]

Yadda aka gudanar da Bikin Nuna Fina-finan Indiya a Abuja

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka kammala Bikin Nuna Fina-finan Indiya a gidan sinimar Silberbird da ke garin Abuja.
Wannan shi ne biki na farko da aka gudanar a Najeriya, inda makasudinsa shirya shi don murnar cika shekarar 100 da masana’antar fina-finan Indiya ta yi da kafuwa ne.
Bikin wanda ya samu halartar dimbin masoyan fina-finan Indiya da suka hada da ’yan Najeriya da kuma ‘yan kasar Indiya an gudanar da shi ne a ranar 31 ga watan Maris zuwa 6 ga watan Afrilu, 2014.
Wani abu da ya dada kayata bikin shi ne an nuna fina-finan ne kyauta.
An nuna fina-finai 12 a ranaku 6 da aka dauka ana gudanar da bikin, inda aka rika nuna fina-finai biyu kowace rana. Ana fara nuna fina-finan ne da misalin karfe shida na kowace rana.
A ranar 31 ga watan Maris, 2014 wato ranar da aka bude bikin ne aka nuna fim din ‘Gandhi’ da kuma ‘Lagaan’. A ranar 1 ga watan Afrilu aka nuna fim din ‘Chadke India’ da kuma ‘Stanley Ka Dabra’. A ranar 2 ga watan Afrilu an nuna fim din ‘Jodha Akbar’ da ‘Sholay’, inda 3 ga watan Afrilu kuma aka nuna ‘Debdas da kuma ‘Dhoom’, sannan a ranar 4 ga watan Afrilu aka nuna fim din ‘3 Idiots’ da ‘Ankhon Dekhi’. A ranar 5 ga watan Afrilu aka nuna ‘Pardes’ da kuma ‘Jordi Breakers’, inda a ranar karshe 6 ga watan Afrilu aka nuna fim din ‘Tare Zameen Par’ da kuma ‘Anjani Anjana’
Kamfanin takin zamani na Indorama da kamfanin Contec Global da Kamfanin Sadarwa na Airtel da Kamfanin mai na Seepco da asibitin Dr. Hassan’s Hospital & Diagnostic Centre da kuma Ofishin Jakandancin Indiya da ke Najeriya ne suka dauki nauyin shirya bikin.
A lokacin da Jakadan kasar Indiya a Najeriya Shri A. R. Ghanashyam yake jawabin bude taro a gaban matar shugaban kasa Dame Patience wadda ita ce babbar bakuwa ne ya ce cikin kasa da mako hudu suka shirya bikin, sun kuma yi hakan ne don kulla kawance tsakanin masana’antar fina-finan Najeriya da kuma Indiya.
Dame Patience ta yaba kokarin ofishin jakandancin Indiya a Najeriya bisa ga namijin kokarin da suka yi wajen shirya gagarumin bikin.
Sakatare na biyu a ofishin jakandancin Indiya da ke Najeriya N. Siban ya ce ya yi matukar farin ciki sakamakon shirya bikin nuna fina-finan Indiya a Najeriya karo na farko. Biki ne mai matukar tarihi, wanda aka shirya shi sakamakon bikin cikar shekara 100 da masana’antar fina-finan Indiya ta yi da kafuwa.
“Mun shirya bikin ne sakamakon shekara 100 da masana’antar fina-finan Indiya ta yi da kafuwa. Biki ne mai matukar tarihi. Lokacin da muka yanke shawarar shirya bikin mun yi tsammanin ba zai samu nasara ba, amma daga baya sakamakon kamfononin da muka tuntuba sai suka ba mu kwarin gwiwa, a gaskiya muna gode musu. Mun kuma gode wa gwamnatin tarayya sakamakon gudunmuwar da ta bayar.”
Da aka tambaye shi me ya sa ba su shirya bikin a Arewacin Najeriya kamar Kano ko Kaduna, inda a wadannan garuruwa ne aka fi kallon fina-finan Indiya, sai ya ce: “Mun yi tunanin hakan, amma sai kuma matsalar tsaro ta kawo tarnaki duk da cewa a wadannan garuruwa da ka ambata babu tashin hankali, amma sai ‘yan Indiya mazauna Najeriya musamman ma wadanda suke Kudanci da Abuja suka rika yin korafi a kan hakan. Hakan ya sanya muka ce bari mu yi a Abuja, sannan muka gayyaci jama’a. Duk da haka muna kokarin shirya gagarumin biki a daya daga cikin garuryuwan Arewa.”
Ya ce manyan jaruman fina-finan Indiya da suka hada da Shah Rukh Khan da Naseeruddin Shah da Anil Kapoor da Deepika Pandukone da Sonam da Dimple Kapadia da John Abraham da sauransu sun bayyana farin cikinsu da kuma addu’ar fatan alheri dangane da bikin.
Bukola Abdulgaffar da ta halarci bikin nuna fina-finan tare da ‘ya’yanta biyu ta ce ta samu gayyata ne daga wani likita BaIndiye da ke aiki a asibitin Dr. Hassan’s Hospital, sannan fina-finan kamarsu ‘3 Idiots’ da ‘Chadke India’ da kuma ‘Gandhi’ sun burge ta.
Kayode Hassan ya ce ya shigo yawo Silberbird ne sai ya ga ana bikin nuna fina-finan Indiya, kasancewarsa ma’abocin kallon fina-finan Indiya ne sai ya shiga. Daga nan ya rika zuwa har aka kammala bikin.  
Ministan harkokin kasashen waje Bashir dalhatu Wali ya rufe bikin, inda ya yi alkawarin yaukaka zumunci tsakanin Indiya da kuma Najeriya.