Yadda aka gudanar da bikin Ranar kabilar Amawa a Jingir

An gudanar da gagarumin bikin Ranar kabilar Amawa a garin Jingir da ke karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato a ranar Asabar da ta gabata. Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Filato kuma shugaban taron, Honarabul Titus Ayuba Alams, ya bayyana cewa babu shakka al’ummar kabilar Amawa mutane masu son […]

Yadda aka gudanar da bikin Ranar kabilar Amawa a Jingir
Yadda aka gudanar da bikin Ranar kabilar Amawa a Jingir

An gudanar da gagarumin bikin Ranar kabilar Amawa a garin Jingir da ke karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato a ranar Asabar da ta gabata.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Filato kuma shugaban taron, Honarabul Titus Ayuba Alams, ya bayyana cewa babu shakka al’ummar kabilar Amawa mutane masu son zaman lafiya.
Ya ce domin wannan kabila suna zaune lafiya tare da dukkan kabilun da suke zaune a wannan yanki shekara da shekaru. Har’ila yau ya ce wannan kabila sun ba da gudunmawa wajen ci gaban Jihar Filato da kasar nan ga baki daya. Don haka ya nuna matukar farin cikinsa da wannan biki da aka shirya.
Ya yi kira ga al’ummar na Amawa da sauran al’ummomin da ke yankin kan su gudanar da zabubbuka masu zuwa a cikin kwanciyar hankali. Kamar yadda ya ce: “Dukkanku ’yan uwan juna ne a wannan yanki, don haka ku cigaba da zaman lafiya a tsakaninku.”
Shi ma a nasa jawabin, Ogomo Pengana, Mista Isaac Bawa Sambo ya yi kira ga al’ummar kabilar Amawa kan a duba wasu al’adu a kasar Amawa, musamman wadanda suka shafi aure da rabon gado ga mata.
Ya ce ya kamata sarakunan gargajiya da masu ilmi da shugabannin addini na kabilar Amawa su zauna su dubi matsalar cewa, shin idan an tashi rabon gado, mata suna da kaso a gado a kabilar Amawa da kuma matsalar aure a kasar kabilar Amawa.
Ya ce: “Ya zama wajibi mu tashi mu yi gyara kan irin kudaden da ake kashewa idan an zo yin aure a kabilar Amawa. Domin sakamakon irin kudaden da ake kashewa wajen yin aure a kabilar Amawa, a halin yanzu akwai yara mata da dama da ba su sami yin aure ba. Don haka mu taru mu yi zama a kan wadannan matsaloli, domin mu warware su.” Inji shi.
Daga nan ya ba da tabbacin cewa kowa ya shirya a wannan yanki na Pengana kan za su gudanar da zabubbuka masu zuwa lafiya.
A nasa jawabin, babban bako mai jawabi kuma shugaban Kwalejin Ilmi ta garin Gindiri da ke Jihar Filato, Farfesa Shem Donn ya bayyana cewa babbar matsalar da ake fuskanta a kasar kabilar Amawa ita ce rashin tashi tsaye da matasan kabilar suke yi wajen kama sana’o’i.
“Muna fatar matasan kabilar Amawa za su canza wannan hali da suke da shi. Matasan Amawa, ku tashi ku kama sana’o’i, musamman sana’o’in hannu.” Inji shi.
Ya yi kira ga dukkan ’yan kabilar Amawa da suke rike da mukaman gwamnati da ’yan siyasa kan su yi kokari su rika samar wa da matasan kabilar ayyukan yi a wuraren da suke. Ya ce yin haka zai taimaka wa al’ummar kabilar Amawa.
Tun da farko a nasa jawabin, shugaban kungiyar ci gaban kabilar Amawa na kasa (AMONDA), Mista Simon B. Harry ya bayyana cewa sun shirya wannan taro ne domin su nuna wa duniya irin al’adun gargaji na kabilar Amawa tare da kaddamar da kalandarsu.
Ya ce: “A cikin watanni 11 da muka yi muna rike da shugabancin wannan kungiya ta ci gaban wannan kabila, mun samu nasarar hada kan wannan kabila tare da fara aikin gina wata cibiya ta koya wa matasan kabilar Amawa sana’o’i.”
Ya ce babu shakka idan suka kammala aikin gina wannan cibiya ta koyan sana’o’i, za a magance rashin aikin yi a dukkann kasar kabilar Amawa. Daga nan ya mika godiyarsu ga dubbin mutanen da suka halarci wannan
taro. Shi dai wannan taro ya samu halartar manyan ’yan siyasa da manyan ma’aikatan gwamnati tare da dubban al’ummar kabilar Amawa daga wurare daban-daban na fadin kasar nan. Kuma an gabatar da kade-kade da raye-raye da abincin al’ummar kabilar Amawa iri daban-daban a wajen wannan taro.

A-Kurkura: Guba ko Magani?

Tsohon Shugaban Jami’ar Ilori, Farfesa Ambali ya rasu

ICPC ta hana El-Rufai ganin likita —Hadiminsa

Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa