Yadda aka gudanar da bikin raya al’adun kabilar Duguza a Magama Gumau
An gudanar da ranar raya al’adun kabilar Duguza a garin Magama Gumau da ke karamar hukumar Toro a Jihar Bauchi, a karshen makon da ya gabata. Da yake jawabi a wajen taron shugaban karamar Hukumar Toro Alhaji Yakubu Bala dansidi ya bayyana matukar farin cikinsa ga al’ummar kabilar Duguzawa kan yadda suka shirya wannan taro […]
An gudanar da ranar raya al’adun kabilar Duguza a garin Magama Gumau da ke karamar hukumar Toro a Jihar Bauchi, a karshen makon da ya gabata.
Da yake jawabi a wajen taron shugaban karamar Hukumar Toro Alhaji Yakubu Bala dansidi ya bayyana matukar farin cikinsa ga al’ummar kabilar Duguzawa kan yadda suka shirya wannan taro na raya al’adunsu.
Ya yi kira ga al’ummar kabilar na Duguza su ci gaba da zaman lafiya da sauran al’ummar da suke wannan yanki, kamar yadda suka saba.
Shugaban wanda daraktan sashin ilmi da walwala na karamar Hukumar Ibrahim Yaro Gumau ya wakilta, ya yi kira ga al’ummar Duguzawa da sauran al’ummar karamar Hukuma Toro su sanya ’ya’yansu a makaranta tare da daukar nauyinsu, har ya zuwa manyan makarantu jami’o’i. Domin a cewarsa yin haka zai dada kawo cigaba a yankin.
Daga nan ya yi kira ga matasan yankin su kama sana’o’i, su guji shaye shayen miyagun kwayoyi da shiga kungiyoyin sara suka. Kuma su guji yarda miyagun ‘yan siyasa suna amfani da su wajen tayar dafitina.
Shi ma a nasa jawabin, mai girma Sarkin Magama Gumau Alhaji Musa Sambo Duguza ya bayyana cewa sun shirya wannan taro ne domin su raya al’adunsu na gargajiya na kabilar Duguzawa, saboda yaransu masu tasowa su san al’adun nasu.
Ya ce a duk shekara suke gudanar da irin wannan taro kuma suna gudanar da wannan taro ne a duk inda kabilar Duguzawa suke zaune a Najeriya.
Ya ce don haka sun gudanar da irin wannan taro a garin Dass dake jihar Bauchi da garuruwan Mista Ali da Saya da Jingir dake karamar hukumar Bassa da karamar hukumar Jos ta gabas a jihar Filato. A yayinda a bana kuma suka shirya wannan taro a garin Magama dake karamar hukumar Toro a Jihar Bauchi.
Ya yi kira ga gwamnati da masu hanu da shuni su tallafawa matasan su koyi sana’o’i domin su sami abin dogaro da kansu.
Ya mika godiyarsa ga gwamnatin Jihar Bauchi da jami’an tsaro da dukan wadanda suka halarci wajen wannan taro kan goyan baya da hadin kan da suka basu wajen gudanar da taron.
Shi dai wannan taro wanda aka gabatar da jawabai da yin kade-kade da raye-raye da wasanni na kabilar Duguzawa. Ya sami halartar Yariman Toro Alhaji Sani Ahmed Toro da dan majalisar dokokin Jihar Filato mai wakiltar mazabar Pengana kuma sakataren kungiyar kabilar Duguzawa ta kasa Honarabul Ezikeal Afon Bauda da shugaban karamar Damban Alhaji Bello Magama da Hakimin kasar Toro, Katukan Bauchi da sauran manyan sarakunan gargajiya da suka fito daga wurare daban daban na Najeriya.