Yadda aka gudanar da bikin Sallah a Masarautar Fika a Yobe
Sarkin ya buƙaci al’umma da su yi wa jihar sa ma Najeriya addu’ar samun zaman lafiya.
Kamar kowane lokaci, a bana ma an gudanar da bukukuwan Sallah a Marasarautar Fika da ke Jihar Yobe cikin yanayin walwala da farin ciki.
A jawabinsa na barka da sallah ga al’ummar masarautar, Mai martaba Sarkin Fika, kuma shugaban majalisar Sarakunan Yobe, Muhammad ibn Muhammad Abali Idris, ya yi kira ga al’ummar masarautar da su zauna da junansu lafiya.
- Yadda Kwankwaso ya yi bikin sallah a Kano
- Sojoji sun ƙwato mata da yara 34 daga hannun Boko Haram a Borno
Yara da ’yan mata ne suka gudanar da bukukuwansu na Sallah ta hanyar raye-raye da kaɗe-kaɗe a harabar fadar, cikin kwanciyar hankali da farin ciki.
Kazalika, a fadar Mai Martaba Sarkin Pataskum, Alhaji Umar ibn Wurya Bauya, an gudanar da bukukuwan sallah cikin farin ciki.
Sarkin, ya yi kira ga al’ummar masarautar da su zauna lafiya da juna tare da yi wa jihar da Najeriya addu’ar samun zaman lafiya.