Yadda aka gudanar da bikin tunawa da garin Shagamu
Mutanen garin shagamu sun yi bukukuwan tunawa da garin na Shagamu mai dadadden tarihi wanda yake a Jihar Ogun.Garin na daya daga cikin garuruwan Kurmi, wanda ke dauke da dinbin ’yan Arewa da suke zaune a yankin shekaru aru-aru kan sana’ ar goro, wacce ita ce ainihin dalilin tarewar ’yan Arewa a garin, baya ga […]
Mutanen garin shagamu sun yi bukukuwan tunawa da garin na Shagamu mai dadadden tarihi wanda yake a Jihar Ogun.
Garin na daya daga cikin garuruwan Kurmi, wanda ke dauke da dinbin ’yan Arewa da suke zaune a yankin shekaru aru-aru kan sana’ ar goro, wacce ita ce ainihin dalilin tarewar ’yan Arewa a garin, baya ga haka akwai dimbin Fulani makiyaya da sauran ’yan kasuwa.
Alhaji Ibrahim Shafi’i Walin Shagamu, wanda ya shaida wa Aminiya cewa a garin Shagamu aka haife shi shekaru 79 da suka wuce kafin daga bisani ya koma Legas bayan ya kammala karatu, inda ya kama aiki a shekarar 1959 ya kuma koma can da zama kuma duk sanda za a yi bikin tunawa da garin, yakan yi tattaki daga Legas domin ya halarci bikin. Ya kara da cewa manyan mutanen alfarma kan zo bikin daga Arewa, domin akwai lokacin da mai alfarma Sarkin Musulmi, marigayi Muhammadu Maciddo ya zo bikin.
Sarkin Hausawan Shagamu, Alhaji Mukhtari Abdullahi Maikano, ya shaida wa Aminiya cewa manufar bikin shi ne assasa hadin kan mutanen Shagamu kuma wannan shi ne karo na 31. Haka kuma duk ranar Asabar din karshen watan Oktoba ake gudanar da shi. Ya kuma shaida cewa Yarabawan yankin da ’yan Arewa ne suka shirya bukukuwan a karkashin jagorancin Oba Sonariwo Erinjugbo II, babban basaraken Lardin Yewa. A cewarsa, Sarkin Hausawan, babban abind a za ka yi wa Bayarabe da zai sa ya yi farin ciki kwarai, shi ne ka amsa gayyatarsa wanda hakan ne ya sanya al’ummar Arewa suka zo kwansu da kwarkwatarsu, domin su ba da tasu gudunmawar.
Shahararren dan kasuwar nan na Jihar Kano, A. A. Rano, Shi ne ya kaddamar da bikin da kudi, Naira miliyan biyar, ya shaida wa Aminiya cewa ya yi mamakin ganin yadda ’yan Arewa da Yarabawan yankin suka hada kansu. “Mun zo mun ga zahiri, mun ga hadin kan da ke garin Shagamu; sabanin labaran da muke ji a waje, ya kamata wuraren da suke rikice-rikicen addini da na kabilanci su dau misali a nan.” Inji shi.
Alhaji Ibrahim Yaro babban manajan kamfanin BUA ne ya wakilci shugaban kamfanin, Alhaji Abdussammad Isiyaka Rabi’u a wajan bikin ya kuma shaida wa Aminiya cewa masana’antunsu na ba da gudunmawa a ci gaban yankin da ma kasar baki daya; wajan samar wa matasa ayyukan yi, ya kuma ba da gudunmawar Naira miliyan biyu da rabi a bikin.