Yadda aka gudanar da Bikin Tunawa da Ranar 11 ga Satumba a Amurka
Amurkawa sun gudanar da bukukuwa da dama domin tunawa da ranar 11 ga Satumba, wato ranar da aka kai harin kunar bakin wake da ya yi sanadiyar kashe kusan mutum 3,000. A daidai lokacin da ake ci gaba da gabatar da bikin, har yanzu akwai mutum 5 da suke tsare suna jiran shari’a, kan zargin […]

Amurkawa sun gudanar da bukukuwa da dama domin tunawa da ranar 11 ga Satumba, wato ranar da aka kai harin kunar bakin wake da ya yi sanadiyar kashe kusan mutum 3,000.
A daidai lokacin da ake ci gaba da gabatar da bikin, har yanzu akwai mutum 5 da suke tsare suna jiran shari’a, kan zargin hannunsu a harin wanda yanzu ya kai shekara 17.
Shugaban Amurka, Donald Trump na cikin dubban Amurkawan da suka halarci taron tunawar da aka gudanar a Shanksbile, da ke cikin Jihar Pennylbania.
An gudanar da bikin ne daidai wurin da jirgi mai lamba 93 ya fadi bayan da fasinjojin cikin jirgin su 40 suka sake kwace jirgin daga hannu ’yan ta’addan kungiyar Alka’ida.
A jawabinsa, Shugaba Trump ya ce shaida wa wadanda suka rasa ’yan uwansu cewa wannan jimamin rashin ba su kadai ya shafa ba, domin abin ya shafi dukan Amurkawa ne.
Ya ci gaba da cewa “Muna cikin wannan bakin ciki tare da duk wani uba ko uwa ko kane ko wa na wadanda suka rasu a harin.”
Ya ce wannan waje da aka kai harin, ya zama cikin tahirin kasar wanda ba za a taba mantawa da shi ba a Amurka, “Wannan taro da muka saba yi shekara-shekara ya zama wani sako ga sauran kasashen duniya, kuma duniya ta sani har kwanan gobe Amurka ba za ta mika wuya ga ayyukan ’yan ta’adda ba,” inji shi.
A Fadar Gwamnatin Amurka kuma, Mataimakin Shugaban kasa, Mike Pence, tare da Sakataren Tsaron Amurka Jim Mattis sun yi taron ne a Ma’aikatar Tsaro da ke Pentagon tare da wadansu iyaye da ’yan uwan wadanda aka kashe a harin.
A can birnin New York kuwa, a dandalin da ake kira Zero, daruruwwan ’yan uwan wadanda suka rasa rayukansu ne suka halarci dandalin da nan ne tagwayen benayen nan biyu na Cibiyar Kasuwanci wadanda aka kai wa hari suke. A wannan wurin, an bayyana sunayen wadanda suka mutu a ranar ta 11 ga Satmba.
Shi dai wannan hari na ranar 11 ga Satumba, shi ne irinsa na biyu mafi muni da aka taba kaiwa a tarihin Amurka bayan na 1944.
Sai dai wannan hari ya sauya alkiblar Amurka a kan yaki da ta’adanci domin tun daga lokacin ne gwamnatin Shugaba Bush ta kaddamar da yaki da ’yan ta’adda da ta’addanci a duk fadin duniya.
Yanzu haka wadanda ake rike da su bisa zargin hannu a harin suna zama fursuna a sansanin sojan Amurka da ke Guantanamo a kasar Kyuba, bisa dalilan da ba wanda zai iya fayyacewa. Har yanzu Amurka ba ta bayyana rana ko lokacin da za a gudanar shari’ar mutanen ba. Wadansu dai suna hasashen sai a shekarar 2020 ko kuma bayan wannan lokaci za a yi shari’ar.
Da farko an fara yi wa mutanen shari’a a asirce a kasar Thailand daga nan aka koma Poland kafin daga baya a mayar da su Guantanamo.
daya daga cikin wadanda ake tuhuma da aikata wannan mummunan aiki mai suna Khalid Sheikh Mohammed dan kasar Pakistan wanda ke cikin sojan sa-kai ya nuna cewa ba shakka shi ne mutumin da ya kai harin na ranar 11 ga Satumban, 2011.
Sauran wadanda ake tsare da su a Guantanamo sun hada da Walid bin Attash, dan shekara 40 dan kasar Yemen, kuma shi ne jagoran sansanin kungiyar Alka’ida da ke Afghanistan.