Yadda aka gudanar da gasar Karatun Alkur’ani da Baibul

Cibiyar Horar da Matasa da suka tsinci kansu cikin harkar shaye-shayen miyagun kwayoyi ta Malam Niga da ke a Rigasa, Kaduna ta shirya gasar Karatun Alkur’ani da Baibul domin murnar zagayowar Makon Tunawa da Addinai ta Duniya.Shugaban cibiyar Malam Lawal Maduru da ake kira da Malam Niga ne ya jagoranci gasar bangaren Musulunci da aka […]

Yadda aka gudanar da gasar Karatun Alkur’ani da Baibul
Yadda aka gudanar da gasar Karatun Alkur’ani da Baibul

Cibiyar Horar da Matasa da suka tsinci kansu cikin harkar shaye-shayen miyagun kwayoyi ta Malam Niga da ke a Rigasa, Kaduna ta shirya gasar Karatun Alkur’ani da Baibul domin murnar zagayowar Makon Tunawa da Addinai ta Duniya.
Shugaban cibiyar Malam Lawal Maduru da ake kira da Malam Niga ne ya jagoranci gasar bangaren Musulunci da aka gudanar karo na farko a cibiyar da ke Rigasa, Kaduna.
A jawabinsa Malam Lawal Maduru ya ce sun assasa wannan gasa ce ta karatun addinin a cibiyar tasu domin nuna wa duniya cewa akwai addini a cibiyar wanda ya shafi Musulunci da Kiristanci, kuma gasar ta zo daidai da makon Tunawa da Addinai ta Duniya.
Da yake jawabi, Malam Lawal Maduru ya bayyana farin cikinsa kan wannan gasa inda ya ce akwai akalla Kiristoci 40 a cibiyar kuma suna gudanar da addininsu yadda ya kamata ba tare da tsamgwama ba. Ya ce akalla matasa 1,650 cibiyar ta horar a cikin shekara 10 da kafa ta.
Ya ce karon farko ke nan da cibiyar ta shirya gasa irin wannan kuma daga cikin littattafin addinin da aka raba wa matasan a karshen gasar sun hada da Hadisai da Fikhu da Sira da Bagadadi; su kuma Kiristoci an raba musu littattafan addu’o’i na kullum da Baibul da kuma sauransu.
 “Saboda addinin Musulunci da Kiristanci su suka fi karfi a kasar na ya sa muka fara gasar a kansu inda muka karantar da su wasu darussa na addinan biyu. Shi Fasto Buru ya jagoranci bangaren Kiristoci ni kuma na jagoranci na Musulmi.  Mun yi haka ne domin duniya ta san cewa ba karamin aiki muke yi ba.
Malam Maduru ya kara da cewa, “Za mu ci gaba da shirya irin wannan gasa domin dama tun farko muna karantar da yaran karatu ta gefe guda ne, amma tunda yanzu duniya ta fito da wannan rana ta tunawa da addinai mu ma za mu ci gaba da shirya irin wannan gasa ga dukkan addinan biyu a cibiyar nan tamu.
Wanda suka yi nasara an raba musu littafan da za su kara musu hazaka a fannin sanin addininsu. Misali littafin Ahalari da aka bai wa wadanda suka yi fice a gasar, littafi ne mai kyau wanda idan har suka mayar da hankali wajen karatunsa sosai mutum na iya zama har waliyi.”
Ya ce “Akalla dalibai shida ne suka fafata a gasar; uku Musulmi, uku Kirista. Maza da mata haka kuma muna saran nan gaba za mu kara yawan wadanda za su shiga gasar,” inji shi.
Fasto Yohanna Buru daya daga cikin malaman addinin Kirista da ya jagoranci wadansu fastoci zuwa cibiyar , ya ce an shirya wannan gasa ce ga matasa Kiristoci da kuma Musulmi da suka tsinci kansu cikin shaye-shaye.
Ya ce wannan gasa za ta taimaka wa matasan su tuna da Allah a yayin da ake ci gaba da kulawa da su a wannan cibiya inda ake kuma koyar da su sana’o’i daban-daban.
Fasto Buru ya ce gasar za ta taimaka wajen nuna wa matasan muhinmancin ci gaba da zamantakewa cikin lumana a tsakanin Musulmi da Kiristocin da ke cibiyar domin su kara fahimtar junansu.
“Mun yi amfani da wannan rana ko mako na addinai da Majalisar dinkin Duniya ta sanya domin kara fahimta a tsakin addinan duniya baki daya wajen shirya wa matasanmu Musulmi da Kiristoci da ke a wannan cibiyar gasa a kan littattafanmu biyu wato Alkur’ani da Baibul. Muna ganin wannan zai taimaka wajen tunatar da matasanmu, musamman wadanda ke cibiyar fahimtar zama da juna lafiya sannan kuma gasar za ta taimaka wajen kusantar da su ga mahaliccinsu. Koyar da su karatun addini za ta taimaka matuka wajen kawar musu da miyagun halaye na shaye-shayen kwayoyi da suka tsinci kansu a ciki. Baya ga wannan ziyara da muka kawo wannan cibiya kuma za mu ziyarci sauran malaman addinai da ke jihar nan domin kara fahimtar juna a tsakaninmu,” inji shi.
daya daga cikin dalibai Kirista da ya yi fice a gasar mai suna Celestine Biniyat ya bayyana farin cikinsa na zama na farko a gasar karatun Baibul.
“Gaskiya nasarar da na samu ta kara min karfin gwiwar ci gaba da neman ilimin addininmu. Duk da cewa dama ina da ilimin Baibul amma ban yi nisa ba sosai, sai da na zo nan cibiyar. Muna amfani da littattafan da aka ba mu safe da yamma domin kara ilimi,” inji shi.
Aminu Sheikh Hanaga ne ya zo na daya a bangaren gasar karatun Alkura’ni da aka shirya a cibiyar.
Ya shaida wa Aminiya cewa “Ina gode wa Allah da Ya ba ni nasara sannan ina gode wa Malam Lawan Maduru a bisa irin tarbiyyar da yake ba mu, domin ganin mun samu rayuwa ingantacciya da kuma ilimi na addini domin inganta rayuwarmu. Wannan gasa da aka shirya mana ta kara min kuzari na in ci gaba da neman ilimin adddinn Musulunci. Dama tun ina gida na sauke Alkur’ani amma sai da na zo cibiyar nan ne na samu hadda, kodayake ban gama haddace Alkur’anin duka ba. Amma dai na san a hankali zan haddace shi, tunda muna karatun sau uku a rana har da asubahi.”
Solomon Yusuf, Kirista ne kuma yana daya daga cikin malaman Kiristoci da suka karantar da daliban ilimin Bibul a cibiyar ,ya ce, “Ni ne nake karantar da su wasu ayoyi da surori daga Littafin Maganar Allah.”