Yadda aka gudanar da Sallar Idi a Oyo
Tun da sanyin safiyar ranar Talata ne al’ummar Musulmi maza da mata da kananan yara suka rika fitowa daga gidajensu zuwa filayen Sallar Idi a birnin Ibadan, a inda limaman mazhabobi daban-daban suka jagoranci yin Sallar Idi raka’a biyu cikin tsauraran matakan tsaro. Babban Limamin Ibadan Sheikh Abdulganiyu Abubakar Agbotomokekere shi ne ya jagoranci yin […]
Tun da sanyin safiyar ranar Talata ne al’ummar Musulmi maza da mata da kananan yara suka rika fitowa daga gidajensu zuwa filayen Sallar Idi a birnin Ibadan, a inda limaman mazhabobi daban-daban suka jagoranci yin Sallar Idi raka’a biyu cikin tsauraran matakan tsaro.
Babban Limamin Ibadan Sheikh Abdulganiyu Abubakar Agbotomokekere shi ne ya jagoranci yin Sallar a babban filin Idi na Agodi da ke Ibadan a inda Mai martaba Olubadan na Ibadan Oba Saliu Adetunji da Sarkin Musulmin Yarbawa Alhaji Dawud Akinola Makanjuola da mataimakin Gwamnan Jihar Oyo Alhaji Rauf Olaniyan da Sanata Teslim Folarin suka kasance cikin manyan mutanen da aka gudanar da Sallar ta bana a tare da su. A bana al’ummar musulmi a Ibadan sun yi Sallah ne a rana daya wato Talata bayan sanarwar ganin jaririn watan Shawwal da mai Alfarma Sarkin Musulmi Sultan na Sakkwato Alhaji Sa’adu Abubakar ya bayar a daren ranar Litinin ba kamar bara da aka kulle kofofin shiga filin Idi na Agodi ba a dalilin sabanin ganin watan da aka samu a tsakanin al’ummar musulmi wanda ya haifar da yin Sallar da babban Limamin ya Jagoranci wasu musulmi ’yan kalilan da suka fara yin Sallar a ranar Alhamis a maimakon Juma’a a daidai irin wannan lokaci ba. Cikin sakonsa, sabon Gwamnan Jihar Oyo Injiniya Seyi Makinde ya yi kiran ne ga al’ummar musulmi musamman masu hannu da shuni su yi amfani da dukiyarsu wajen taimakawa ‘yan uwansu gajiyayyu domin tsamar da su daga kuncin rayuwar fatara da talauci. Gwamnan ya fadi hakan ne cikin takardar sanarwa da Shugaban Ma’aikatan gwamnati Cif Bisi Ilaka ya sanya wa hannu cewa, idan attajirai suka yi amfani da dukiyarsu wajen tallafawa talakawa to kuwa za a samu ragowar talauci a Najeriya.
Shi kuwa tsohon Gwamnan Jihar Oyo Sanata Rasheed Ladoja cikin sakonsa ga musulmi ya fara taya su murnar zagayowar wannan rana ta Eidil Fitri ne. Sai dai ya yi amfani da wannan dama wajen yin kira da kakkausan harshe ga Gwamnonin Jihohi 6 na Kudu maso Yammacin kasa da su jingine siyasa waje daya su hada kai domin samo mafita a kan matsalar tsaro da ya ce, wannan ne muhimmin abun da al’umma suke bukata. Su ma al’ummar musulmi ‘yan Arewacin kasar da ke zaune a birnin Ibadan sun gudanar da karamar Sallar ta bana ne a filayen Sallar Idi na harabar gidan gwamnati a inda Sheikh Rufa’i Hussaini ya jagoranci masu mazhabar Dariku da filin wasannin na Adamasingba da Sheikh Sani Haruna ya jagoranci mabiya Izalatul Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah. Haka kuma akwai Filayen Sallar idi masu yawa a cikin birnin Ibadan a inda wasu musulmi mabiya mazhabobi daban daban suka yi sallarsu a bana. An gudanar da bukukuwan Sallar bana ne cikin tsauraran matakan tsaro da aka girke ’Yan sanda dauke da bindigogi a sassa daban daban na birnin Ibadan.
Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton babu wani labari da ya shafi tashin hankali a wani sashe na Ibadan. Aminiya ta samu rahoton cewa, al’ummar musulmi a manyan garuruwan Jihar Oyo da sauran jihohin Kudu maso Yamma duk sun gudanar da sallar bana lafiya.