Yadda aka gudanar da taron kungiyar matasan Fulani a Benin
A makon da ya gabata ne Shugabannin kungiyar Matasan Fulani Makiyaya ta kasa [AMFON], suka sake kira ga ‘ya’yan kungiyar, domin halartar wani zama na babban taro a garin Benin fadar mulkin Gwamnatin Jihar Edo, inda taron ya samu halartar manya-manyan shugabanni na Alumman fulani [Ardo-Ardo] na ko wani bangare cikin jihar da wajenta tare […]
A makon da ya gabata ne Shugabannin kungiyar Matasan Fulani Makiyaya ta kasa [AMFON], suka sake kira ga ‘ya’yan kungiyar, domin halartar wani zama na babban taro a garin Benin fadar mulkin Gwamnatin Jihar Edo, inda taron ya samu halartar manya-manyan shugabanni na Alumman fulani [Ardo-Ardo] na ko wani bangare cikin jihar da wajenta tare kuma da ainihin jagorori na babbar kasuwar Shanu Benin jIhar Edo.
A wajejn taron, shugabannin kungiyar matasan Fulanin da jagorori a babbar kasuwar shanu, sun tattauna a kan batutuwa da dama, wadanda suka hada har da batun barnace-barnace da masu gonaki ke korafi ana yi musu.
kungiyar ta nuna bacin ranta a kan yadda maganar barnar take ci gaba da karuwa a kowane lokaci. Saboda haka sai suka yi gargadi a kan abin da suka kira sakaci na wasu makiyayan masu dabbobi da suke bai wa ’ya’yansu kanana da ba su mallaki hankali ba shanu masu yawa, su tafi da sunan kiwo su je su tura su cikin gonakin mutane ba ruwansu kawai.
Saboda haka wannan tarun da wadannan shugabanni su ka yi da ‘ya’yan kungiyar, sun ce sun yi shi ne, a kan kyakkyawar manufa ta nema wa al’ummar Fulanin makiyayan ’yanci na samun zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsu da jama’a, kuma da ainihin manoma a jihar Edo da wajenta.
‘’Makasudin wannan taron da muka yi shi ne ganin yadda abubuwa daban-daban suke tasowa tsakanin manoma da makiyaya, wannan muke son mu hada kai, mu bi hanya wadda ta dace domin shawo kan matsalolin. Tabbatar da hadin kan Fulani makiyaya da samar musu hanyoyi na wanzar da zaman lafiya tsakaninsu da masu gonaki a wan nan jihar, inda ya kara da cewa saboda haka muke kira ga daukacin fulanin a kan su ci gaba da nuna halaye na kwarai ba irin wanda manoman suke siffantasu da su, ko suke zarginsu a kai ba,”inji shi.
Shugaban kungiyar matasan Fulanin Alhaji Shuaibu Haruna Sogiji ya shawarci Fulani makiyaya su hada kansu a kan abin da zai kawo musu ci gaba da zaman lafiya a kasar nan .
Ya ce ya zama wajibi ga duk wani Bafulatani makiyayi da zai shigo kurmi, musamman Jihar Edo to ya tabbatar ya tuntubi wakilan kwamiti da kungiyar ta ayyana su zama masu kula da sha’anin su, a wajen sasantawa tsakakanin manoma da su makiyaya a jihar, wadanda a ciki akwai shugaban kwamitin, Alhaji Musa Migiri sai Alhaji Golcho da Alhaji Sharif Ibrahim da Alhaji Idiris Danna da Alhaji Bello Sagera da Alhaji Mamman Sosal da Alhaji Abdalla Bilaki da kaftin Adamu sai kuma Alhaji Abdullahi Danna da Shuaibu da Malam Ibrahim mai katako da Audu jalingo da Alhaji Jingudo da Hasana Umar , sai Idis Adamu shauran su ne Alhaji Abbas Yusuf da Alhaji Tanle Obata da Alhaji Sani Mokawu yace shauran za su bayyana sunayensu nan ba da dadewa ba inji shi’’.