Yadda aka gudanar da taron Majalisar Sarakunan Hausawa
Sarakunan Hausawa da manyan masu rike da sarautu na Jihar Legas sun yi wani taro a fadar Shugaban majalisar sarakunan Hausawa na Jihohi 17 a Kudancin kasa Sardaunan Yamma, Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin da ke Ibadan. Taron ya mayar da hankali ne a kan batun nada fitaccen dan kasuwa mai hada-hadar canjin kudade a […]
Sarakunan Hausawa da manyan masu rike da sarautu na Jihar Legas sun yi wani taro a fadar Shugaban majalisar sarakunan Hausawa na Jihohi 17 a Kudancin kasa Sardaunan Yamma, Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin da ke Ibadan. Taron ya mayar da hankali ne a kan batun nada fitaccen dan kasuwa mai hada-hadar canjin kudade a Legas Alhaji Isma’ila Salihu Maikakan a matsayin Sarkin Yakin Jihohin Yamma, wanda masarautar Agege ta ki amincewa da nadin saboda wasu dalilai.
Majalisar masarautar Hausawan Agege ta shigar da kara kotu na neman a dakatar da nada Alhaji Isma’ila Salihu Maikankan a matsayin Sarkin Yakin Yamma.
Mako daya da wucewa kafin a yi taron na ranar Asabar da ta wuce sai da wannan dan kasuwa Alhaji Isma’ila Salihu Maikankan ya jagoranci dimbin jama’arsa na ciki da wajen Najeriya da suka rufa masa baya zuwa fadar Sarkin Sasa a Ibadan da nufin nada shi a kan mukamin Sarkin Yakin Jihohin Yamma. Sai dai a matsayinsa na Uba, Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin bai tabbatar da nada shi a kan wannan sarauta ba, a maimakon haka ya mika masa rawani da hula da alkyabba da takkardar shaida (certificate) ne, inda ya umarce shi ya koma ya nemi gafarar majalisar masarautar Hausawan Agege da za ta tabbatar masa da wannan sarauta idan ta yafe masa.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya cewa dan kasuwa Isma’ila Maikankan ya bi umarnin Sarkin Sasa, inda ya jagoranci jama’arsa zuwa fadar Sarkin Hausawan Agege a inda ya shafe kusan awa daya a durkushe yana neman gafarar Sarki da ‘yan majalisarsa.” Majiyar ta ce, majalisar Sarkin Agege ba ta yafe masa ba a maimakon haka ne Sarkin Hausawan Agege Alhaji Musa Muhammed Dogon Kadai ya jagoranci manyan Sarakuna da masu rike da sarautu na Legas zuwa fadar Sarkin Sasa, inda suka nemi a warware nadin da aka yi wa Alhaji Isma’ila Maikankan a matsayin Sarkin Yakin Yamma. Sai dai Sarkin na Sasa bai amince da yin haka ba a maimakon haka ma ya nuna amincewa da wannan nadi ne, kuma ya yi karin girma ga Sarakunan Hausawa guda 3 na Jihar Legas da suka halarci taron na ranar Asabar.
Da yake tabbatar da batun karin girma da aka yi wa sarakunan, Sarkin Sasa ya yi wa dimbin mahalarta taron bayani kamar haka:, “A matsayina na Shugaban Majalisar Sarakunan Hausawa a Jihohi 17 na Kudancin kasa daga yau na tabbatar da nada Sarkin Hausawan Agege Alhaji Musa Muhammed Dogon Kadai a matsayin mataimakin Sardaunan Yamma. Daga yau ya zama mataimakina, kuma na tabbatar da nada Sarkin Hausawan Ikotu a Legas Alhaji Nuhu Alhassan a matsayin Sarkin Bai na Jihohin Yamma. Shi kuwa Sarkin Hausawan Idi-Araba Alhaji Hassan Auyo na nada shi ne a matsayin Garkuwan Yamma”.
Duka wadanda suka yi jawabai a gaban jama’a sun nuna matukar farin ciki ne da matakin warware wannan matsala da Sarkin Sasa ya dauka. Sun karanto Ayoyin Alkur’ani da Hadisan Annabi Muhammad (SAW) da suka yi nuni da irin shugabancin jama’a da Sarkin Sasa yake yi wajen yin adalci da koyi da Annabi Muhammadu (SAW), kamar yadda Addinin Musulunci ya shimfida wajen kawo karshen wannan matsala da taki ci taki cinyewa.
Da yake yi wa Aminiya karin haske Sarkin Sasa cewa ya yi: “Mun kawo karshen wannan matsala bayan dukkan masu jayayya sun amince da irin hukumcin da muka zartar. Nan ba da dadewa ba za mu tabbatar da nadin Alhaji Isma’ila Maikankan a matsayin Sarkin Yakin Yamma. Na umarce shi a matsayinsa na Bahaushe da ke zaune a garin Agege ya rinka girmama masarautar ta Agege. Kuma ya ci gaba da yin amfani da dukiyarsa wajen taimaka wa masarautar da sauran jama’a.”
Da yake tofa albarkacin bakinsa Sarkin Hausawan Idi-Araba Alhaji Hassan Auyo ya jinjina wa Sarkin Sasa ne a game da karin girma da ya yi wa Sarakuna uku ‘wanda ba mu za ci haka ba, domin abin da ya kawo mu nan Ibadan daban. Ina rokon Allah (SWT) ya yi mana jagoranci wajen sauke nauyin da ke wuyanmu wajen tallafa wa mutanenmu da ke zaune a wannan sashe domin samo hanyar fita daga kuncin rayuwa. Ina yin kira ga jama’armu su taimaka wajen bayar da hadin kansu gare mu (shugabanni), ta yadda za mu ci gaba da ayyukan kare ‘yancin mutane kamar yadda muka saba.”
Galadiman Yamma Alhaji Umar Adamu da Magajin Garin Agege Alhaji Ali Abubakar Zango suna daga cikin manyan masu rike da sarautu a Jihar Legas da suka halarci taron na Sasa.