Yadda aka hana kida a biki a Nijar
Masarautar Abzin da ke Jihar Agadez a Jamhuriyar Nijar ta hana wasu dabi’u da suka hada da anko da hana kade-kade yayin bukukuwan aure ko suna. Kuma mazauna Agadez sun yi maraba tare da sam barka da wannan mataki. Matakin da Mai martaba Sarkin Abzin ya dauka yana ci gaba da samun tsokaci daga mazauna […]

Masarautar Abzin da ke Jihar Agadez a Jamhuriyar Nijar ta hana wasu dabi’u da suka hada da anko da hana kade-kade yayin bukukuwan aure ko suna.
Kuma mazauna Agadez sun yi maraba tare da sam barka da wannan mataki.
Matakin da Mai martaba Sarkin Abzin ya dauka yana ci gaba da samun tsokaci daga mazauna garin Agadez da suka ce sun dade suna jiran irin wannan mataki.
Mata da su ne dokar hana anko ta shafa sun ce za mu ce ta tarar da mu je mu, sun kuma koka game da da ayarin da ake yi yayin kai amarya a lokutan bikin.
Wata mata Malama Gaisha ta shaida wa BBC cewa, dama iyaye mata ne suke shan wahalar sayen anko a lokutan biki.
“Muna neman abin da za mu kai bakin salati amma sai batun anko ya daga mana hankali don yara suna sa mu a gaba sai mun saya musu.”
Shi ma Malam Mohamed wani mahaifi a garin Agadez, ya jinjina wa Mai martaba Sarkin Abzin kan wannan doka ta hana anko da ayarin motocin kai amarya da kide-kide ranar aure ko suna da dai sauransu.