Yadda aka hana matasa ɗibar fetur bayan faɗuwar tankar mai a Taraba
Ɗaruruwan matasa ne suka yi tururuwa suna yunƙurin ɗibar fetur bayan faɗuwar tankar a kusa da Shatatetalen Mil 6 da ke Jihar Taraba, amma jami’an tsaro suka hana su
Jami’an tsaro sun daƙile yunƙurin matasa na ɗibar man fetur da ke tsiyaya daga wata tankar mai da ta yi hatsari a Jihar Taraba.
Ɗaruruwan matasa ne suka yi tururuwa suna yunƙurin ɗibar fetur bayan faɗuwar tankar a kusa da Shatatetalen Mil 6 da ke Jihar Taraba, amma jami’an tsaro na Sibil Difens (NSCDC) suka hana su.
Faɗuwar tankar ke da wuya a ranar Laraba masu shaguna a wurin suka rufe suna tserewa saboda tsoron tashin wuta, amma matasan suka nemi zuwa su ɗebi man cikinta.
Kakakin Hukumar NSCDC na Jihar Taraba, Iliya Samuel, ya bayyana cewa zuwa jami’an hukumar a kan lokaci wurin ya taimaka wajen kawar da barazanar tashin wuta.
- ’Yan bindiga na tserewa zuwa cikin al’umma a Sakkwato —Gwamnati
- Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji
Iliya wanda ya ce an garzaya da direban motar da ya samu rauni a hatsarin zuwa asibiti inda aka duba lafiyarsa.
Kakakin rundunar ’yan sand a a jihar ya ce an ɗauki matakan da suka kamata a wurin da tamkar ta yi hatsari, domin daƙile duk wata barazana.
Wannan na zuwa ne kwana uku bayan mutuwar sama sa mutanen 100 a yayin da suke kwasar fetur daga wata tanka da ta faɗi a Mahaɗar Dikko da ke Ƙaramar Hukumar Gurara ta Jihar Neja a kan Babbar Hanyar Abuja zuwa Kaduna.
A ranar Litinin wata mai ɗauke da mai ta fadi a jihar, inda mutane suka yi rububin zuwa ɗibar man da ta ɗauko.
Shaidu sun ce mutanen sun yi zaton man fetur ne, amma sai suka ga ashe man girki motar ta ɗauko.