Yadda aka kaddamar da saban Sarkin Hausawa da na Nufawa a Benin

A wannan makon ne majalisar sarakunan Hausawa ‘yan Arewa mazauna grin Benin na Jihar Edo ta gabatar da sunayan mutune biyu wadanda zasu gaji kujerar sarkin Hausawa da sarkin Nufawa mazauna grin. Shugaban majalisar Alhaji Hasan Adamu ya bayyana sanan Adamu Isha Adamu a mantsayin wanda ake sa ran ya gaji sarkin Hausawa da kuma […]

Yadda aka kaddamar da saban Sarkin Hausawa da na Nufawa a Benin
Yadda aka kaddamar da saban Sarkin Hausawa da na Nufawa a Benin

A wannan makon ne majalisar sarakunan Hausawa ‘yan Arewa mazauna grin Benin na Jihar Edo ta gabatar da sunayan mutune biyu wadanda zasu gaji kujerar sarkin Hausawa da sarkin Nufawa mazauna grin.
Shugaban majalisar Alhaji Hasan Adamu ya bayyana sanan Adamu Isha Adamu a mantsayin wanda ake sa ran ya gaji sarkin Hausawa da kuma Sani Idris Sani a matsayin sarkin Nufawa.
Shugaban majalisar ya ce sun mika sunayen mutum biyun ne a matsayin sarakunan gargajiya akarkashin majalisar Oba na Benin, saboda cancantar su.    
Kujerun biyu da aka kaddamar da sababbin shugabannin akwai ta marigayi sarkin Husawa Alhaji Isah Adamu wanda ya rasu a ranar asabar din sha biyar ga watan Agusta na wannan shekara inda aka zabi babban dansa Adamu Isah Adamu dan ya zama Sabon Sarkin Hausawan Benin. Sai kuma kujeran marigayi Sarkin Nufawa Alhaji Idiris Sani wanda ya mutu a ranar lahadi daya ga watan February na farkon wannan shekara inda aka bada sunan dansa Alhaji Sani Idiris Sani dan ya zama sabon sarkin Nufawan Benin.
Lokacin da ya ke gabatar da sunayen, shugaban majalisar Alhaji Hasan Adamu wanda kani ne ga marigayi sarkin Husawan Alhaji Isah Adamu
Alhaji Hasan Adamu ya ce “wadannan da muka ayyana sunansu domin sanin ce wa dukkanmu yan asalin yanki gudane inda muka fito don haka ina kira gareku da ku basu goyon baya da hadin kai tare da shawarwari na kwarai”.
Kuma Jim kadan bayan kaddamar da wadannan sababbin sarakunan Wakilin Aminiya ya samu zantawa da su daban-daban inda shi sabon Sarkin Hausawan Alhaji Adamu Isah Adamu ya ce “abin farin cikina shi ne ganin yadda muka fara samun hadin kai daga cikin gidanmu mu ‘yan uwa da kuma ainihin kanin Mahaiffinmu Shugaban majalisar Sarkin Hausawan Alhaji Hasan Adamu wanda shi ne kashin bayan tabbatar da ni amatsayin Sarkin Hausawa.
Shikuwa kuwa sabon sarkin Nufawan Alhaji Sani Idiris Sani cewa ya yi “lallai ina mai matukar farin ciki da godiya ga Allah da wannan zabena da aka yi amatsayin jagoran jama’a.”
Ya daya daga cikin aninda za su maida yankali akai a halin yanzu shi ne maganar tarbiya domin “rashin mayar da hankali akan neman ilimin addini da na zamani ya jefa matasa cikin wani hali na gurbacewar tarbiyya da suke shaye shaye da sace sace da sauransu, saboda haka wajibine ga iyaye da malamai da sarakuna su hada kai da hukumomi domin kawar da irin wannan mummunar dabi’ar ga yaranmu”.