Yadda aka kai harin bam a Jos
A ranar Lahadi da daddare wadansu mahara da ake zargin ’yan Boko Haram ne suka kai tagwayen hare-hare a shagon abinci na Shagalinku da ke Titin Bauchi Road da kuma Masallacin Juma’a na ’Yan Taya; masallacin da Shugaban kungiyar Izalatil Bid’a Wa’ikamatus Sunnah na kasa Sheikh Sani Yahaya Jingir yake gabatar da tafsiri. Daraktan Hukumar […]

A ranar Lahadi da daddare wadansu mahara da ake zargin ’yan Boko Haram ne suka kai tagwayen hare-hare a shagon abinci na Shagalinku da ke Titin Bauchi Road da kuma Masallacin Juma’a na ’Yan Taya; masallacin da Shugaban kungiyar Izalatil Bid’a Wa’ikamatus Sunnah na kasa Sheikh Sani Yahaya Jingir yake gabatar da tafsiri.
Daraktan Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA) mai kula da shiyyar Arewa ta Tsakiya Mohammed Abdulsalam, ya bayyana cewa mutane 44 ne suka mutu a wadannan hare-haren, inda 23 suka mutu a masallacin ’Yan Taya, 21 kuma suka mutu a shagon cin abincin, sannan aka kwantar da mutane 48 a Asibitin Maternity da na Plateau da kuma na Sunnah da sauransu, sai dai hukumar ta ce adadin wadanda suka mutu zai iya haura hakan.
Aminiya ta tattauna da wadanda tagwayen hare-haren suka rutsa da su, inda suka yi bayanin yadda suka tsira daga hare-haren.
Yadda aka kawo mana hari a wajen tafsiri – Sheikh Jingir
Bayan kai hare-haren na ranar Lahadin, a ranar Litinin Sheikh Sani Yahaya Jingir ya tattauna da wakilan Aminiya, inda ya yi bayani dalla-dalla kan yadda aka kawo harin da kuma yadda ya tsallake rijiya da baya. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Aminiya: Mene ne ya faru lokacin da aka kawo hari a masallacin ’Yan Taya lokacin da kake gabatar da tafsir a daren ranar Lahadin da ta gabata?
Sheikh Jingir: A gaskiya wannan al’amari na kawo harin ta’addanci da aka yi mana a masallacin ’Yan Taya da ke nan garin Jos, wato wajen da muke gabatar da tafsiri, ya zo ne daf da lokacin da za mu tashi daga wannan tafsiri. Sai muka ji wadansu mutane sun fito daga wadansu lunguna da suke kusa da wannan masallaci suna harbi da bindiga. Da mahalarta tafsiri suka ji harbe-harben bindigar, sai wadansu suka kwanta a kasa. Daga nan wani daga cikin masu harbe-harben nan ya zo har kusa da wajen da muke ajiye motocinmu, ya tada bam, ya tarwatsa kansa, ya bata motocin da suke wajen da jini da naman jikinsa. Bayan kura ta lafa sai muka kammala karatu muka yi addu’o’i, sannan muka tashi muka tafi gidajenmu.
Aminiya: Me za ka ce dangane da al’amarin yanzu?
Sheikh Jingir: A gaskiya mun gode Allah, domin idan mutum ya dubi yadda ake haduwa a wannan masallaci, zai san Allah Ya ba mu kariya a wannan hari da aka kawo mana. A nan ina son in yaba wa ’yan agajinmu da ’yan banga wadanda suke ba mu tsaro a wannan masallaci, kan irin kokarin da suka yi wajen kubutar da mutane da dama a wannan hari da aka kawo mana. Irin wannan harin ta’addanci ba shi ne na farko ba a Najeriya, hatta mu a nan wajen an sha kawo mana irin wadannan hare-hare wadanda muke ganin kamar na nuna jin haushin Musulunci da Musulmi ne da kuma kokarin ganin an jefa Najeriya a cikin masifa, musamman a yankin Arewa. Wadannan abubuwa da suke faruwa abin takaici ne. Amma ba za su taba karya mana gwiwa ba, da yardar Allah wa’azin da ba sa so a rika yadawa za mu ci gaba da yi.
Aminiya: Mutane nawa ne suka rasa ransu sakamakon hari da aka kawo muku wajen tafsiri?
Sheikh Jingir: To, a bangarenmu kwamitin da muka nada don tantance mutanen da suka rasa rayukansu a wannan hari ya kawo mana rahoton cewa mun rasa mutane guda 27. Kuma tuni mun yi jana’izarsu a makabartar da ke garin Naraguta.
Aminiya: Ko akwai wadanda kake zargi da kawo harin?
Sheikh Jingir: A makonni biyu da suka gabata na yi wa’azi a kan wadansu da ake gani a kan babura, inda suka rufe ko’ina a jikinsu, sai idanunsu kawai ake gani, wadannan mutane ba su san ko’ina ba, idan ka hau babur dinsu ka ce su kai ka wani wuri ba su sani ba, to na yi wa’azi a kan su, na nemi a yi bincike a kansu.
Aminiya: To, wane kira kake da shi zuwa ga malaman da suke gudanar da tafsiri cikin wannan wata?
Sheikh Jingir: Ina kira ga dukkan masu gabatar tafsiri su ci gaba da tafsirin da suke gudanarwa a cikin wannan wata. Kuma su ci gaba da wayar da kan jama’a kan muhimmancin zaman lafiya da tafiya cikin natsuwa.
Aminiya: To, a karshe wanne kira ne kake da shi zuwa ga gwamnati da sauran al’ummar kasar nan, dangane hare-haren ta’addancin da ake kaiwa a garuruwa?
Sheikh Jingir: Ina kira ga mahukunta da sauran masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro su kara himma wajen kawo karshen ayyukan tarzoma a kasar nan. Kuma ina kira ga al’ummar kasar nan cewa kada mu yi tsammanin an samu canjin gwamnati, mu koma gefe mu zauna. Ya kamata mu fito mu tallafa wa gwamnati domin ganin an yaki wadannan ‘yan ta’adda.
Mu yi hattara domin mun yarda Allah Ya taimake mu mun samu canjin gwamnati. Bayan da muka yi ta addu’o’i kuma muka tsaya aka yi aiki, aka yi zabe wanda Ya ba mu nasara. Don haka kira na shi ne a sake mayar da hankali kan tsaro ta hanyar lura. Da an ga wani abu mai alamar canji, kada a yi shiru a fito a fadakar da gwamnati da jama’a. Domin wadannan mutane ba su da kyakkyawar manufa. Don haka bai kamata mu shantake mu ce ai maganar ta wuce ba. Lallai mu rage barci; mu rage tafiya babu lura. Mu rika kai rahoton dukkan abin da ba mu gane ba. Kuma mu kyautata halayenmu; mu ci gaba da addu’o’in da muke yi.
Yadda na tsira daga harin – Umar Malwa
Umar Idris Malwa da ke zaune a Tudun Fera a Titin Bauchi Road ya ce kwanciyar da ya yi a kasa lokacin da ake ta harbe-harbe saboda fadakar da su da shugaban rundunar ’yan sandan sashin Nasarawa na cewa, idan ana harbe-harbe kada mutum ya mike ne ya taimaka masa ya tsira daga harin, inda bayan ya shiga masallaci ne ya ga Sheikh Jingir zaune a kan kujera yana addu’o’i. “Jiya (Lahadi) na samu zuwa wurin tafsir a Masallacin ’Yan taya, muna zaune ni da wadansu ’yan unguwarmu uku, amma a yanzu da nake asibiti na ga gawar daya daga cikinsu. Muna zaune a bayan motar Sheikh Sani Yahaya Jingir, sai muka fara jin harbe-harbe, a lokacin sai wani abu ya fado mini, kasancewar ina cikin wata hukumar samar da tsaro da ake kira Neighborhood, DPO na Nasarawa ya taba kiranmu wani taro, a nan suka fadakar da mu idan irin haka ta faru to kada mu rika tashi a tsaye, mu rika mirginawa a kwance.”
Ya ce yana cikin mirginawa ke nan, a kusa da shi akwai wani sanye da jar riga a gefen hagu, don har sun gaisa ma, sai ya ga ya mike, “to harbin da aka yi sai ya same shi, sai ya fadi, sai na ci gaba da mirginawa, sai ya zama mutane da dama sun mike suna gudu, inda suka rika taka ni, zan iya cewa mutane fiye da 50 sun taka ni, inda wani ya taka kaina da bayana da kuma hannuna.
“Amma haka na rika mirginawa har na je asalin kofar da malam yake wucewa, sai na ga wani yaro dan agaji dan shekara 5, yana tsaye yana kuka, sai na kwantar da shi, muka ci gaba da mirginawa, bayan an daina harbe-harben ne sai na bar yaron, sannan na ci gaba da rarrafe har na koma gefe na kwanta, daga nan na shiga masallaci, jama’a saboda abin da ya faru duk sun mike.” Inji shi.
Ya ce daga nan ya ji ana fadin, Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un, “ni ma sai na karbi wannan kalma, ’yan agaji suka rika fiffitowa, duk da na ji wannan ciwon amma na ji wani karfi a jikina. Mahaifina shi ne sakataren gudanarwa na kasa, sai na fara nemansa, saboda ni nake rike masa Al’kur’aninsa, in shiga har inda Sheikh Sani ke gabatar da Tafsir, kujerar mahaifina tana daga gefe, a nan zan ajiye masa Al’kur’aninsa, sai in koma waje in zauna, to hankalina ya tashi da ban gan shi ba, a nan na tambaye wani dan agaji, mai suna Shafi’u Yakub wurin da mahaifinmu yake, sai ya ce mini yana nan, na rika zaga cikin masallacin ban gan shi, daga nan na rika tattara Al’kur’anai, wadansu duk jini ya bata su, wadansu kuma sun yi kaca-kaca, hankalina bai kwanta ba, sai na zo wurin motarmu, to a nan na gan shi, inda na ce masa mu tafi gida.” Inji shi.
Da aka tambaye shi ko a lokacin da ya shiga cikin masallacin ya ga Sheikh Sani sai ya ce: “A lokacin da na shiga na gan shi zaune a wurin da ya saba zama yana gabatar da Tafsiri, haka shi ma mai ja masa baki Malam Aminu Yusuf yana zaune a kujerarsa, inda dan agaji Shafi’u Yakub na ga ya kare malam, shi kuma Malam na ga yana addu’o’i.”
Ya ce daga baya ’yan agaji suka bukaci a ragu a cikin masallacin, daga nan aka kunna lasifika, Malam Aminu Yusuf ya yi addu’a aka watse.
‘Mace mai karamin siket ce ta kawo harin bam wurin cin abinci’
Juliet Peter daya daga cikin masu aiki a sahgon cin abincin na Shagalinku ce wadda ta samu mummunan raunika a lokacin da bam din ya tashi a wurin sayar da abincinsu, ta bayyana cewa wata budurwa ce mai sanye da karamin bakin siket da kuma riga ruwan hoda ce ta tayar da bam din.
Ta ce tana cikin dakin da ake sayar da abinci sai uwargijiyarsu Hajiya Rakiya ta ce ta dafa mata maganin Hausa na ciwo siga a wajen da murhunsu yake, “dama kowace rana ni nake dafa mata, a lokacin ta ce in duba kan kujerarta domin ta kulla maganin ta ajiye, ita kuma sai ta dauki buta don ta zaga, na dauki ledar sai ban ga maganin ba, sai na rufe, sai na fito, to a nan na ga wata yarinya da jaka, sai muka hada ido da ita daga nan na kawar da kaina, kafin ka ce me sai na ga haske ya mamaye ko’ina, sai na ji na fadi, bayan na fadi sai na ce Allah Ka cece ni, sai wutar shagon ta dauke, ni dai ban san da yaya na kai can saman kwalta ba, kusa da shagon Hajiya Sa’a.”
Ta ce daga nan wadansu bayin Allah suka dauke ta a Keke-Napep, su ma ba su fi minti biyar da barin shagonsu ba, wadannan mutane ne suka kawo ta asibiti.
Da aka tambaye ta labarin da ake yada wa na cewa ko mota kirar 406 ne maharan suka zo da ita, sai ta ce, “A gaskiya ba zan iya tabbatar da hakan ba, domin a cikin shago, bayan na fito ne na ga shigowarta daga kofa ta uku, da jakarta a rataye, ta sanya riga mai ruwan hoda da kuma dan karamin bakin siket, a nan ta tsaya, daga nan bam ya tashi.”
Ta ce ma’aikatan da suke aiki a shagon sun fi goma, amma a yanzu ba za ta iya tantance wadanda suka mutu a cikinsu ba, saboda yanayin halin da ta samu kanta a ciki, sannan ba za ta iya cewa ko wadda ta kawo harin ma ta mutu ko tana da rai ba.
A karshe ta gode wa Allah da ya tseratar da ita, sannan ta bukaci hukuma ta matsa kaimi don dakile hare-haren kunar bakin wake.