Yadda aka kai wa mahaifin Kwankwaso hari

A ranar Talatar da ta gabata ce wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, suka kai hari cikin masallacin kofar gidan Majidadin Kano, Hakimin Madobi kuma mahaifin Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso wato Alhaji Musa Saleh.daya daga cikin wadanda abin ya rutsa da su, wani tsohon soja mai […]

Yadda aka kai wa mahaifin Kwankwaso hari

A ranar Talatar da ta gabata ce wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, suka kai hari cikin masallacin kofar gidan Majidadin Kano, Hakimin Madobi kuma mahaifin Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso wato Alhaji Musa Saleh.
daya daga cikin wadanda abin ya rutsa da su, wani tsohon soja mai suna Usman Nadada, da cikin masu kare lafiyar hakimin, ya ce “Da misalin karfe takwas na dare muna cikin masallaci bayan an sallama Sallar Isha, sai mutanen suka bude mana wuta daga bangaren Yamma maso Kudu kuma ina jin harbin kamar mutum uku ne zuwa hudu suke yinsa.”
Nadada ya ce harbin da Saje Shu’aibu ya yi daga cikin masallacin da kuma daya daga jami’an SSS da na dan sandan da ke waje mai suna Christopher ne suka hana mutanen zuwa cikin masallacin.
Ya ce bayan sun yi harbi na misalin minti 20 zuwa sama da suka ji an yi shiru sai suka juya suka nufi yamma, ta inda suka fito suka yi tafiyarsu.
Nadada ya ce duk da cewa yana tare da bindigarsa, amma kasancewar suna cikin masallaci abin ya rutsa da su babu yadda za su yi su fito su fuskanci mtanen da harbi, ya ce wani yaro mai suna Sani dahiru da ya fito da nufin zai gudu sun harbe shi ya rasu a nan take.
Ya ce mutum uku ne maharan suka kashe da suka hada da wani tsohon soja mai suna Muhammad da Saje Christopher da ya mayar da harbi ga mutanen suka biyo har bayan bishiyar da ya buya, suka harbe shi.
Daga cikin wadanda suka samu raunuka da Aminiya ta zanta da su sun hada da jami’an tsaro na SSS, mai suna Umar wanda ke jinya a Asibitin Malam Aminu Kano, kuma ya ce ba su ankara ba, bayan idar da Sallar Isha suna tare da hakimi sai suka ji harbi, bayan sun mike tsaye da harbin ya ci gaba sai suka kwanta a kasa. Ya ce kafin ya kwanta ne harsashi ya same shi a hannu, sannan kuma da ya yi kokarin hana wani yaro kuka, nan ma wani harsashin ya same shi a kafa.
Shi kuma Ibrahim Tanko wanda ake yi wa lakabi da Gago, ya ce shi soja ne a bataliya ta 3 da ke Barikin Bukabu kuma abin ya rutsa da shi ne kasancewar ya je ganin gida Kwankwaso. Ya ce “Bayan an idar da Sallah kawai sai muka ji harbi, ni harsashin farko ne ma ya same ni a kafadata ya huda ya fita.”
Wadanda aka raunata har da autan su Gwamna Kwankwaso, wato Suleiman Musa Saleh da gilashin tagar masallacin ya yi wa rauni, sai wani yaro dan kanen Gwamna Kwankwaso wato Baba Kwankwaso mai suna Yusuf Saleh da aka harba a hannu.
Wani da ya ganewa idonsa, Musa dahiru ya ce mutanen sun je garin ne a cikin Jeep da Golf da babura biyar kirar Boder, tun misalin karfe shida na yamma suka yi sansani a makarantar Firamare ta Galadimawa. Ya ce tun kafin su kai harin wasu suka ga suna raba bindigogi, inda har wani Adamu ya je ya fada wa Saje Christopher abin da ke faruwa. Ya ce bai sani ba ko marigayi Christopher ya sanar da sauran jami’an ko manyansa kafin harin ya faru.
A yayin da Gwamna Kwankwaso ya kai ziyarar ga wadanda suka yi rauni, ya ce an sallami mutum bakwai daga cikin 13 da aka raunata, inda ya tabbatar da kashe mutum 3.
 Ya nanata niyyar gwamnati na ci gaba da tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ASP Magaji Musa Majiya, ya tabbatar da rasuwar mutum 3 da raunata 12, kuma ya ce har zuwa lokacin ba su gano su wane ne suka kai harin ba, sai dai suna ci gaba da bincike.