Yadda aka kama Bafaranshe zai yi wa matar direbansa fyade

Wata matar aure da ke yi wa bature dan kasar Faransa aiki a gidansa ta koka cewa ya yi yunkurin yi mata fyade. Maryam Ukpoji da ke aikatau a gidan Bafaranshen ta shaida wa Aminiya cewa ta shekara shida tana aiki a gidansa a Jihar Legas kuma babban jami’i ne a wani kamfanin man fetur. […]

Yadda aka kama Bafaranshe zai yi wa matar direbansa fyade

Maryam Ukpoji, ‘yar aiki mai zargin Bafaranshe da neman yi mata fyade

Wata matar aure da ke yi wa bature dan kasar Faransa aiki a gidansa ta koka cewa ya yi yunkurin yi mata fyade.

Maryam Ukpoji da ke aikatau a gidan Bafaranshen ta shaida wa Aminiya cewa ta shekara shida tana aiki a gidansa a Jihar Legas kuma babban jami’i ne a wani kamfanin man fetur.

Ta ce mijinta ya fara aiki da wanda take zargin ne a matsayin direbansa a shekarar da ta gabata ta 2019.

Maryam ta ce an fara takun saka tsakanin mijinta da mai gidansu bayan mijin nata ya nemi izinin tafiya coci a ranar Lahadin farko bayan Gwamnatin Jihar Legas ta bude wuraren ibada.

“Bayan Baturen ya dauki mijina aikin direba a shekarar da ta gabata sai ya nemi mu koma gidansa mu zauna tare da shi, inda ya ba mu daki guda da ke kuryar gidan.

“Da farko mijina ya ki yarda, domin ba ya so ya saki gidan da muke a unguwar Yanoworo, domin gudun saki na dafe, amma baturen ya ce dole direbansa ya kasance tare da shi a kowane lokaci.

– Ya fake da guzuma domin ya aikata masha’a

“Bayan an bude wuraren ibada a Legas ne sai mijina ya tambaye shi izini ya bashi dama ya tafi coci, sai ya fusata yana ta yi masa fada, ya ce shi babu ruwansa da addini, ya ce baya bukatar aikin mijin nawa inda ya bukaci ya je ya kirani.

“Da misalin karfe 10 na dare suka dawo gidan tare da mijina, sai ya zo ya ce mai gidanmu ya ce yana son gani na, ya fada min yadda suka yi, bayan ya nemi ya ba shi izinin zuwa coci; sai muka tafi bangaren mai gidan namu tare da mijina.

“Ko da muka isa sai ya bude kofa na shiga. Mijina ya yunkuro zai shigo sai ya rufe kofar da karfi, ya ce da ni yake son magana ba da mijina ba. Da ya ga haka sai ya koma gefe ya tsaya.

“Muna shiga rumfar gidan sai ya tube rigar da ke jikinsa ya shiga dakin girki ya zuba shayi a kofi ya koma ya same ni ina tsaye.

“Sai ya ce na matso kusa da shi na zauna sai na ki. Na dauka zai kawo min karar mijina ne, amma sai na ga yana ta yi min maganganun banza, abin da a baya ba ya yi min.

“Ya tambaye ni ko mijina na waje? Ko da na je na duba sai na ce masa eh, yana jikin mota.

“Sai ya ce na je na ce masa ya tafi, da naje na fada wa mijin nawa umarnin mai gidanmu sai ya tafi.

– Yadda ya yi kokarin yi min fyade

“Ko da na dawo sai ya fara cewa na rabu da mijina mutumin banza ne, baya kula da ni; Shi zai kori mijina amma ni ba zai kore ni ba, zai ba ni kulawa da ‘ya’yana.

“Sai ya je ya kawo min kayayyakin sha masu sanya maye na ki karba, na ce masa ba na shan abu mai sa maye.

“Ina kokarin ficewa, na ce masa mai gida don Allah kar fa ka ji haushi na don na fice. Ban raina maka ba, amma ka yi hakuri. Kafin na farga ya je ya tsare hanyar da zan bi na fita.

“Ban yi aune ba sai na ga ya cire gajeren wandonsa, ya fito da mazakutarsa wai na tsotsa.

“Nan da nan hawaye ya cika fuskata. ya ce dole sai na tsosi mazakutar, wai dole na yi masa abin da yake so, domin ni baiwarsa ce, mijina ma haka; in ban biya masa bukatarsa ba zai sa a kore mu daga gidan cikin kasa da awa guda domin kudi yake biya, Naira miliyan 12 a shekara.

“Ban yi aune ba sai ya cakumo ni, ya kama ni da kokawa daga nan, gajeren wandan ya sabule daga jikinsa, ya sa kafa ya cire shi baki daya.

“Ya riko rigata ta gaba ya yage ta, nan na yi ta kururuwa har Allah Ya sa wani mai gadi ya jiyo ya bude kofar.

– An kama shi ya yi zindir

“Da mai gadin ya shigo sai ya haska shi da fitila ya ce Benoit Gueho, kai ne haka?

“Ya yi wuf zai dau kayansa ya saka, mai gadin ya ce kada ya kuskura ya dauka. Nan mutane suka taru aka dauki hotonsa da nawa a yadda aka same mu”, inji ta.

– Ya ba mu kudi mu rufa masa asiri

Ta ce bayan mutane sun taru sai aka sanar wa mijinta shi ma yazo, sai baturen ya nemi a rufa masa asiri ya ce zai biya kudi N200,000. Amma mijinta ya ki amincewa ya ce sai ya sanar da ‘yan sanda.

Sai manajan gidan ya ce ko an fada wa ‘yan sanda su za su ci kudin su kuma juya maganar; ganin haka ne ya kai wa kungiyar kare hakkin dan Adam maganar.

– Sai an an hukunta baturen —HRID

Shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam ta HRID, Onoja Ken ya shaida wa Aminiya cewa za su tabbatar an bi wa matar hakkinta an kuma hukunta baturen dan kasar Faransa.

“Don haka muka shigar da takardar koke ga Kwamishina ‘Yan sandan Legas, Hakeem Odumosu da kuma Ofishin Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda mai kula da shiyya ta biyu, AIG Ahmed Iliyasu.

“Za mu tabbatar an yi adalci kuma a shirye muke mu je kotu”, inji shi.

Aminiya ta zanta da mai taimaka wa manajan kamfanin man fetur na  Bourbon inda Baturen da ake zargi ke aiki, Ezikiel.

Ya ce kamfanin ya fara binciken lamarin, kafin daga bisani ya ce lauyan kamfanin ne zai iya cewa wani abu akan tuhumar.

Hakazalika wakilin Aminiya ya tuntubi lauyan wanda ake zargin,  Olamide Balogu, amma ya ce masa a jira sakamakon takardar koken da aka shigar.

– Kamfanin Bourbon ya dakatar da mijin matar

Da fari kamfanin na Bourbon ya bai wa mijin matar, Clement Ukpoji, tabbacin ci gaba da aikinsa kamar yadda ya saba, inda suka bayyana a sakon kar-ta-kwana da suka aike masa, cewa ba su da matsala da shi.

Sai dai daga baya kanfanin ya ba da sanarwar dakatar da shi.

– ‘Yan sanda sun fara bincike 

Jami’an ‘yan sandan yankin Panti a Yaba  da ke binciken lamarin, sun shaida wa Aminiya cewa suna gudanar da bincike.

Sun sunayen wadanda za su aike wa sammacin a wannan mako sun hadar da baturen kasar Faransar da budurwarsa da ke baraza ga matar da ta yi koken.