Yadda aka kama barauniyar jariri

Ta yi batan dabo da jaririya mai wata uku da haihuwa a wurin koyon sana’a

Yadda aka kama barauniyar jariri

Dubun wata matashiya da ta yi batan dabo da wata mai wata uku da haihuwa ya cika bayan an shafe kwanaki ana neman ta.

Ban ’yan sanda sun bazama neman matar da ta arce da jairiryar uwargidanta mai koya mata dinki ne suka yi ido hudu da ita, nan take suka yi mata dirar mikiya.

A ranar Lahadi ne mai koyon dinkin ta goya jaririyar da cewa za ta je cire kudi a ATM ta dawo, daga nan aka neme ta sama da kasa aka rasa.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ondo, Salami Amidu Bolaji ya ce bayan samun labarin sace jaririyar daga shagonta dikin ne jami’an Rundunar suka bazama domin ceto ta cikin gaggawa ba tare da wani lahani ba.

Ya ce bayan kwanaki ana farautar wadda aka zargin ba dare ba rana ne aka yi kacibus da ita kuma tiso keyarta.

Kwamishinan Rundunar iyaye su rika kula sosai da ’ya’yansu, musamman ’yan kanana, su kuma rika ba wa ’yan sanda bayanai a koyaushe don gudanar da aiki cikin gaggawa.

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro