Yadda aka kama wasu barayin A Daitata Sahu a Kano
Dubunsu ta cika bayan sun gyara babur din sun sauya mishi fenti da lamba
Dubun wasu barayin babur din A Daidaita Sahu ta cika bayan sun yi awon gaba da wani babur a unguwar Naibawa da ke garin Kano.
Matasan masu shekara 24 da kuma shekara 24 sun shiga hannu ne bayan ’yan banga sun cafke daya daga cikinsu a unguwar Kofar Dawanau, suka mika shi ga ’yan sanda, su kuma daga baya suka cafko abokin cin mushensa.
- An tsinci gawar dan kasuwar Kano a daji bayan an biya fansar N6m
- An sanya na’ura mai ba da fatawa da Hausa a Masallacin Harami
Matashin ya ce, “Shekara daya ta gabata an taba kama ni, aka yanke min hukuncin daurin shekara daya a gidan yari ko kuma biyan tarar N30,000, amma iyayen suka biya tarar aka sake ni.”
Ya bayyana cewa, “A Daidai Sahun da muka sace ba ya ma aiki, sai da muka gyara muka sauya masa fenti da lambar KAROTA don kada a gane.
“Ni ne na ajiye ta a wuri, har zuwa lokacin da aka kama abokina, wanda hakan ya sa nima aka mako ni.”
Da yake gabatar da su Hedikwatar Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano, kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce bayan ’yan sanda masu bincike sun titsiye na farkon ne aka kai ga cafko daya matashin a unguwar Na’ibawa Kwanar Ciyaman