Yadda aka kama ‘dan kunar bakin wake’ dauke da bom a banki a Jos

‘Dan kunar bakin waken’ ya nemi bakin ya ba shi Naira miliyan 100, ko ya tayar da bom din da ke jikinsa

Yadda aka kama ‘dan kunar bakin wake’ dauke da bom a banki a Jos

Jami’an tsaro sun kama wani ‘dan kunar bankin wake’ da ya yi barazar tayar da bom din da ke jikinsa a cikin banki a Jos, fadar Jihar Filato.

A safiyar Litinin ne matashin da ke daure da ababen fashewa a jikinsa ya shiga reshen Bankin UBA da ke unguwar Dadinkowa a garin Jos,  ya nemi a ba shi kudi Naira miliyan 100, ko ya tayar da bom din.

Wani jami’in bankin da ya nemi a boye sunansa ya ce ma’aikatan bankin suna tsaka da kula da kwastomomi ne matashin ya yi barazanar tayar da bom din.

A cewarsa, dan kunar bakin waken ya yi basaja ne kamar kudi zai cira, ya je kan kanta ya shaida wa jami’in bankin cewa akwai bom a jikinsa kuma idan ba a yi abin da yake so ba zai tayar da bom din.

“Sai ma’aikacin ya sanar da babbansu cewa a sanar da jami’an tsaro nan take su bude wa kwastomomi kofar baya domin fitar gaggawa.

“Ana cikin haka ne aka sanar da jama’a cewa su fice daga cikin bankin domin tsira da rayukansu.

“Da ya lura jama’a na ficewa ta kofar baya sai shi ma ya shige cikinsu, amma jami’an tsaro suka kama shi, aka kira ’yan sanda masu kwance bom.

“Da suka zo sai suka wuce da shi zuwa ofishinsu da ke Rantya domin gudanar da bincike,” in ji jami’an bankin.

A cewarsa, wanda ake zargin ya samu shiga cikin dakin bankin ne saboda bom din da ke jikinsa ba na gaske ba ne, shi ya sa ya iya wuce kofar shiga bankin dauke da shi.

Zuwa lokacin da muka kammala wannan labari kakakin yan sandan jihar Filato, DSP Alabo Alfred, bai amsa kira ko sakon da kuma tura masa ba na neman karin bayani kan lamarin.

Faruwar lamarin dai ya jefa mazauna yankin cikin fargici, inda suka yi ta guje-gujen neman tsira da rayukansu.