Yadda aka kama gungun barayin motoci a Sakkwato

An taba kama daya daga cikin barayin motocin kan satar motoci uku, kuma yanzu da zaran an kammala bincike za a kai su kotu,” in ji ‘yan sanda

Yadda aka kama gungun barayin motoci a Sakkwato

An kama gungun wasu barayin motoci bayan sun sace motoci hudu a garin Sakkwato.

Rundunar ’yan sandan jihar ta kama mutanen su biyu masu shekaru 32 da kuma 44 ne bayan sun sace wa wasu mutane biyu motoci a garin.

Sanarwar da kakakin ’yan sanda a jihar, ASP Ahamad Rufa’i ya fitar ta ce, a satin da ya gabata ne wasu mutum biyu mazauna unguwar Badon Barade suka kawo koken a sace wa kowanensu mota kirar Corolla LE da kuma Pontiac Vibe.

“Bayan mun samu labarin sai rundunarmu ta sanar jami’anmu da ke shingen hanyar Birnin Kebbi a garin Bodinga.

“A binciken da muke yi wadanda ake zargi sun amsa laifinsu kuma an gano wasu karin motoci biyu a hannunsu, an kuma kama wani mutum daya.

“A baya ’yan sanda sun taba kama daya daga cikin barayin motocin kan satar motoci uku, kuma yanzu da zaran an kammala bincike za a kai su kotu,” in ji shi.

Jami’in ya yi kira ga al’umma su zama a fadake su rika bayar da bayanin duk wani abu da ba su gamsu da shi ba ga hukumo ko ta lambar rundunar  ta kar-ta-kwana: 08032345167.