Yadda aka kama barawon kudi ta katin ATM din wasu a Gombe

’Yan sanda sun kwari katunan ATM na mutane 21 a hannun matashin a garin Dukku da ke Jihar Gombe

Yadda aka kama barawon kudi ta katin ATM din wasu a Gombe

Katin ATM

’Yan sanda sun kama wani matashi kan zargin satar kudi ta na’urar ATM a Jihar Gombe.

Rundunar ’yan sandan jihar ta kama matashin, wanda ake wa inkiya da Mai Shanawa ne kan zargin aikata yaudara da satar kudi da katin ATM ta na’urar PoS.

Matashin ya fada komar ’yan sanda ne bayan wani mazaunin garin Abuja Bula, da ke Karamar Hukumar Kwami ya kai rahoto ofishin ’yan sanda na Dukku a ranar 22 ga Watan Mayu 2024.

Muhammad yana zargin matsahin da yaudarar sa da kuma satar kudi a asusun bankinsa a banki a lokacin da yaje cire kudi da katinsa na ATM.

Ya ce bayan ya saka katinsa  na’urar ATM ba ta ba shi kudin ba, ashe matashin yana biye da shi a baya, sai ya yaudare shi cewa ya shiga cikin banki ya yi musu bayani.

Bai ankara ba, ashe a lokacin matashin ya zare masa katin ya bar shi a wajen.

Mutumin ya ci gaba da cewa, yana tsaye yana jira can sai yaga sako an cire Naira dubu dari uku daga asusunsa ta wani POS da ke kusa da bankin a garin na Dukku.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, ASP Buhari Abdullahi, ya ce bayan  samun rahoton korafin suka shiga bincike suka yi sa’ar kama wanda ake zargin.

ASP Buhari Abdullahi ya ce a yayin binciken sun samu katunan cire kudi na ATM daban-daban har guda 21, ciki harda na wanda ya kai korafin, a hannun matashin.

Sannan ya ce suna kan ci gaba da bincike, da zarar sun kammala za su tura wanda ake zargin zuwa kotu.

Dalilin da ba zan bai wa Gwamnatin Tinubu shawara ba — Sarki Sanusi

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana