Yadda aka kama miyagun kwayoyi miliyan 8.2 a Saudiyya

Hukumomin Saudiyya sun kama miyagun kwayayoyi sama da miliyan takwas da aka yi fasa-kwaurinsu zuwa kasar a lokaci guda.

Yadda aka kama miyagun kwayoyi miliyan 8.2 a Saudiyya

Tulin miyagun kwayoyin da aka kama a Saudiyya. (Hoto: SPA).

Hukumomin Saudiyya sun kama miyagun kwayayoyi sama da miliyan takwas da aka yi fasa-kwaurinsu zuwa kasar a lokaci guda.

Kakakin hukumar yaki da miyagun kwayoyi na kasar, Manjo Marwan al-Hazmi ya sanar da haka a lokacin da yake gabatar da kwayar captagon guda miliyan takwas da dubu 280 da 78 da ake kokarin fasakwaurinsu zuwa kasar.

Daga cikin kwayoyin har da wadanda aka boboye a cikin mazubin gahawa, domin bad-da kama.

Al-Hazmi ya ce an kama mutum biyar da ake zargi da shigo da kwayoyin, da suka hada da ’yan kasar Siriya uku mazauna kasar da ’yan kasar Paikstan biyu.

Ya ce an gabatar da batun a gaban kotu domin yanke musu hukunci.

Hukumar ta yi kamen ne kwana 17 bayan wata kotu a birnin Jidda na kasar Saudiyya ta yanke wa wasu ’yan kasar 17 da wani dan Siriya hukuncin daurin shekara 80 kan laifin sarrafa miyagun kwayoyi.