Yadda aka kama mutum 333 da muggan makamai a zaben Kano

Mutum 333 sun shiga hannu kan zargin aikata laifuka a yayin zaben cike gurbi da aka kammala a Jihar Kano.

Yadda aka kama mutum 333 da muggan makamai a zaben Kano

Mutum 333 sun shiga hannu kan zargin aikata laifuka a yayin zaben cike gurbi da aka kammala a Jihar Kano.

A ranar Asabar aka gudnar da zaben na cike gurbi a mazabun Majalisar Tarayya da akamaimaita a ranar Asabar a mazabar Ghari/Tsanyawa da kuma zaben cike gurbi na Bagwai/Shanono.

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya sanar da karuwar adadin mutanen daga 288 a ranar Litinin a hedikwatar rundunar da ke Kano.

A cewarsa, zaben ya fuskanci barazana sakamakon “shigo da ’yan daba da dama daga cikin da wajen jihar” da suka yi yunkurin dagula tsarin zaben, amma an samu nasarar shawo kan lamarin ta hanyar haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

 

“An kama mutane 333 a yankunan Ghari, Bagwai da Shanono bisa zargin dagula tsarin zabe, kuma an kwato abubuwa da dama daga hannunsu,” in ji CP Bakori.

Ya ce abubuwan da aka kwato sun haɗa da bindigogi 6, gorori 94, takubba 16, adduna 18, barandami 32, wukake 18, baka da kibau 23, alburusai 45, motoci 14, akwatin zaɓe guda 2, takardun zaɓe da aka riga aka dangwala guda 163, da kuma kuɗi Naira 4,048,000.

Bakori ya ƙara da cewa duk waɗanda aka kama an gurfanar da su a kotuna kan zargin haɗin guiwar aikata laifi, tayar da hankali, mallakar makamai masu haɗari, tsoratarwa, yawo ba tare da dalili ba, satar kayan zaɓe da kuma neman ƙuri’a ta hanyar da ba ta dace ba.

Ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kare sahihancin tsarin zaɓe da tabbatar da cewa duk wanda ya yi yunkurin dagula shi zai fuskanci hukunci.

Ya yaba da ƙoƙarin hukumomin tsaro da ya bayyana da “ƙwarewa da sadaukarwa” a lokacin zaben, yana mai cewa hakan ne ya hana tashin hankali ya yadu.

Bakori ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bin doka da oda tare da ba da haɗin kai ga jami’an tsaro, yana mai jaddada cewa tsaro alhakin kowa ne.